LAIFINA NE 10

100 11 0
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       ❤️ *LAIFINA NE*❤️
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*Ina cigiyar Takarduna Kamar haka...*
'''A dalilin so
A dalilin matar uba
Hisabi
Rayuwar Wasu
Zeenat Yar jarida
Yar makafi
Silar gidan aiki'''
    duk Wanda yake dashi should send me via 08067088446

*PAGE 🔟*

Haidar ne Zaune se tinanin Fauxeey yakeyi, Kallon agogon jikin dakin yayi yaga after 1, Lalabo wayarshi yayi ya fara Dialing numbern Fauxeey ko zaiyi sa'a cikin dare ta kunna wayar, Amma yaji a kashe, Tinanin Maganar Ahmad ne ya dawomai akan anya ma tanada Asali kuwa, Dan betaba ganinta da kowaba da sunan yan uwansu, ko yaji tana labarin family dinta, Wani  Nunfashi yaja aranshi "yace To danme zatamai haka, kuma ya nuna ba sonshi takeyiba Dan da tana sonshi bazata taba gujenshiba.
    Cillar da wayar yayi kan gado, Ga Zafi biyu, Yanzu dole yasama abunda zaidinga keeping dinshi busy, Dan ba aiki yake zuwaba, Wata zuciyar tace ya sanar da mahaifiyarshi wata zuciyar tace kuma ka dakata! Tashi yayi yai Alwala yai Sallah ya roka Allah in har Fauxeey alherice Allah yasa ta dawo in kuma ba alheri bane Allah ya kawo mai mafita, Dan yanzu for how long zata dawo, inma ta dawon kenan, Ahaka bacci ya kwasheshi

Kirar Sallah yaji yai maza ya tashi yace oh akwana a tashi asarar mai rai, wai har subhi tayi koda yake ban kwanta da wuriba,

Shiga toilet yayi ya daura alwala yai Sallah, Ya shirya Kamar zaije office Nan ya tsaya tinanin Ina zaije....

WASHE GARI
     Su fauxeey tun wuri suka tashi, dama ita bawani bacci tai ba, Dan a matse take gari ya waye, misalin Karfe 8 Ta kalle agogo tace Yanzu Haidar bazaije office ba, Kwalla ne ya cika idonta aranata tace" Akwai alhaki akaina, meyasa banmai Hukunci
Daidai da laifinshiba, jitai Sam bata da kuzari a atare da ita, tana tsoron kar alhakin Haidar ya kamata, Dan duk da tasan yafi karfin haka, tasan ta cutar dashi

Ummie ne ta kalleta tace" Sist lafiya kuwa naga sudden change a tare dake yanzu haka, what's wrong ko duk tinanin ya haidar ne? Kallon ummie tai a azuciyarta tace wannan akwai mayya wlhi, sai kace me karantar zuciyar mutun, Kirkiro Wani murmushi tai tace Ke kincika sa ido, Ummie ta kyalkyale da daria, Fauxeey tace ko kunyar mama bakyaji ko? Ummansu najinsu tai kamar bata wajen, Dan Ummie batasan ta ido ba, Tafi fauxeey rashin Kunya kodan karamace Oho

   Harhada kayansu sukai 9:00 suka Bar hotel din suka nufa inda Fauxeey ta Kama masu, Sunga gida Masha Allah, 2 bed room ne sai falo da toilet 2 and kitchen sai dan madai daicin tsakar gida,

Ummiey Tace kai Amma unguwar akwai kyau Wallahi, yanzu Aunty Akwai nisa da inda aka Kai kine? Nikam zanso nasan Wajen aikinki anan naga da Chan wanne yafi kyau

Jitai gabanta ya fadi dum, meyasa ummie keson bata mata shiri, yarinya kamar mai duba, Fauxeey kallonta tai tace to yawale Ai baki isaba, Tai sauri ta shashantar da zancen tace Anjuma zamuje kasuwa musiyo katifa da sauran kayayyakin da zamu bukata, Ummansune tace Da kun bari an kwana biyu Ko tabarmane ma kwana akai,

Ummie tace kai Haba mama.

Fauxeey tace" baza'ai hakaba mama tunda da kudi ai komai me sauqine

Ummie tace aunty Har kinsa naji dadi, Ummansu kuwa tace Allah yai muku Albarka, A tare sukace Ameen,

Shuru sukai na Dan mintina, Fauxeey tinanin yanda zata Shiga gidan azzalumin Mutumin nan da yai ma Yarinya fyade takeyi, Ummie ta kaseta daga tinaninn tace" Aunty na kosa muje kasuwa akwai abunda Zan siyo,

Fauxeey hararta tayi tace kyaji da shi

           ******
Haidar kuwa ya fito yai Sallama da mahaiyarshi,  gateman ya bude mai gate ya fita, tafiya ya farayi ahankali, Yana tinanin Ina zai dosa, Yanzu duk wajen wanda yaje this early morning zaice yayi losing job dinshi dukda ba abun kunya bane a wajenshi, Ahmad ya fadomai arai, dan haka yasan yanzu Yana Gida, Kai tsaya ya juya sitiyarin motarshi ya nufa gidan su Ahmad

Yana zuwa shima mai gadi yabude mai gate a daidai lokacin shima Ahmad Zai tafi Office dinshi, Yana ganin Haidar ya dan tsuke fuska, Yana kokarin Hawa mashin dinshi
  Haidar ne ya ce come on Nigga Kamar baka ganniba? Kazo mutafi kawai mana,

Sai a lokacin Ahmad ya kalleshi yace" oh kaine da safen nan, Haidar yace" eh nine kazo mutafi

Ahmad bude Sit din gaba yai zamanshi tare dacemai Assalamu Alaikum
    "Waalaikas Salam Haidar ya amsa dashi, yai reverse ya fita daga gidan bawanda yacewa kowa komai har suka isa PLAZA na Ahmad

Parking space yasamu yayi, sannan suka fito, Ahmad nagaba Haidar nabinshi a baya har suka iso office din Ahmad
Shuru sukai na mintina, Sannan Ahmad yace ya akaine? Haidar yace shawara nazo ba bani akan Fauxeey "Ahmed tsayawa kallon haidar yayi na wasu Mintina yaushe Son Fauxeey ta shiga ranshi haka, shi ya dauka kawai they're just frnds ne ashe abun babbane.....haidar ne yace plz say something,

"Ahmad yace Well Mubar maganar Losing din aikinka, tunda nasan kai Dan babban gidane, Kunada arziki dan kinfimu, You once told me dama saboda Fauxeey ne kke zuwa wajen aikin nasan definitely Ko ba'a korekaba tana dena zuwa kaima zaka Dena Right?

"Haidar yace exactly hakane, Yanzu matsalata daya yanda Mum zata duba fahimta ne, Bansone tasan akan wasu takardu aka koreni kuma kai kasan in anyi bincike da yawa za'ace. Fauxeey ne ta dauka, So I don't want fauxeey to involve a maganar

Ahmad yace abune me sauqi, Why not ka koma Kasar waje da karatu? Kace sunce Kaje Kai wani course tunda dama kanada shirin zuwa haduwarku ne da fauxeey yasa ka tsaya?

Haidar yace that's My nigga saiyasa nakesonka, Haka kuwa za'ai very soon zanbar kasar...Ahmad kuwa yace so then inkaje gida seka sanar da hajiya Yace Yauwa

Misalin 10:00AM, Wasu yanmata 2 suka shugo Inda su Ahmad suke, Tunda sukaga Haidar yazo jiya suka kasa sukuni, dan ya matukar masu kwarjina ga kyau gashi cikekken namiji, Basui tunanin zasu ganshiba

Zuwa sukai dan su tambaye Ahmad number Haidar kawai sukai kicibis dashi a Shagon, Gaba dayansu rikicewa sukai, Balle lokacin da ya daga Ido ya kallesu, Sameerah ce ta fara Ammm ammm Dan tsabagen rikicewa da tai, dan ya mata kyau sosai

Ahmad ne Ya dago tarkonsu yace" Su Sameerah seyau ake ganinku? Ai inasha fushi kukai tace" Wani fushi kazo musa labule Dan haka suka fita, Shikam Haidar danna wayarshi yakeyi

****
      Hajiyarsu Haidar tana zaune tana sauraron labaran radio na karfe 10:00AM kamar zata kashe sai kuma tace Bari muji Me kasar tamu ke ciki

Masu labarai nan suka Fara zayyyane komai na kasa, yanda kayan abinci yai tsada, ETC, sannan sukace suna jin qishin qishin din nan bada dadewa ba za'a koma school duka, Alhamdulillah tace wannan corana ai anzaunu a gida, Sannan taji ance to zamu rufe da Wannan labarin ne companyn ZAMS ne suka kora wani Mai suna *Aliyu Abdullahi dabai* Dan tsohon minister  akan Sama da fadi dayai da wasu takardu na contract din da za'a ba company din, yin hakan ba karamin cikas ya kawo musu ba, To duka duka anan muka kawo karshen shirin

Mik'ewa tai tace Haidar!!! Haidar, Kodai banji dakyau bane...

Kannanshine Suka fito a daki sukace Mum Mum kinji sharrin da akaiwa Ya haidar kuwa?

Sai a lokacin taji tabbas maganar da taji daidaine......

Zama tai a kujera hankalinta tashi dan har haki takeyi tace kui maza ku kiramun Haidar.........

TOOFAAA

MUJE ZUWA

Yan Wattpad Vote dinku yamun kadan gaskiya, Kudinga Voting in kunason Update

Urs Ummiey Xeey

Don't forget to FOLLOW
COMMENT AND VOTE

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now