LAIFINA NE 23

69 12 2
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*HASFAT TOORAE🤩* _congratulations for the completion of ur Super Novel....Allah ya kara basira dear💥💥💥_

*PAGE 2️⃣3️⃣*

Washe gari, Fauxeey tun asuba ta tashi, bayan tai sallah tasa ruwa a kettle ta dakko wayarta ta kunna, tana kunnawa text din Muhsin suka shugo wayarta guda 2, text din kalaman soyayya ne kawai a ciki, Karantawa tai, aranta tace you're not serious, kwantawa tai kafin ruwanta ya yai zafi bacci ya kwasheta

Misalin 8 Ummiey ta shugo dakin, ganin Fauxeey na bacci ta tasheta, tace yau Sister bazakije aikin bane karfe takwas
A firgice Fauxeey ta tashi ta shiga Wanka shap shap ta fito

    Wani dan Riga doguwa ta saka sannan ta Daukar Hijab din mamanta Zumbulele ta saka tace Yau dashi zan tafi mamanta tace Allah ya tsare, Tace Ameen

Fita tai da sauri Allah yasa ta sama adaidaita ya karasa da ita Layin

tana Shiga Gidan taci karo da usman Bobo yana motsa jikinshi a hararar gidan, Idanshine ya Sauka akanta, yaga tamai kyau, Tsaya yace ta staya chak

Karasawa wajen yayi ina mata wani irin kallo Wayartane ya fara kara tai maza tai Kamar tana gyara riganta ta kashe Allah yasa ba kara sosai yake fiddawa ba, Kallonta yai yace are you Ok kuwa? Kamar baki da gaskiya
     Addua tai a zuciyarta kan ta fara mai magana, tace kamar yaya fa?

Yanda tai maganar sound somehow to him ita zatamai magana a tsaye haka wai kamar yaya fa, Cewa yai naji karar Iphone a tare dake, Zare ido tai tace I me? Tab wazai bani AI seku manya irinku, Murmushi mugunta yayi yace Ok Ki shiga, Sidif sidif ta shiga jikinta ba inda baya rawa,  anya bazatabar aikin na ba kuwa yanzu da yaga wayata karyata ta kare, he will see all my pics kuma zaigane Nice Wacce yake nema shekarun baya, Innalillahi Wa inna ilaihir tajiun tace? take tambayar kanta, dan Already jiya mamanta tace batason aikin ta hakura kawai, wani Breathing tayi tace ya Allah see me through da kai kada na dogara...

Bobo Kuwa binta da ido yayi seda yaga ta shiga Dakin sannan ya karaso wajen gate man ya kalleshi, yace kasamun ido sosai a yarin yar nan, Ni ban yarda da itaba

Gateman yace Angama Oga, Kodai kana cikine? Bobo dan tsuke fuska yayi yace i don't knw for now

Gate man Yace Oga Oga...yauwa jiya wata tazo nemanka nace mata bakanan

"bobo yace wa kenan, Gateman yace" sumayya, ohhh Bobo yace

Bayan fauxeey ta shiga Dakin, tsayawa tai ta  hangensu daga window taji dai suna magana and she's sure akanta akeyi, tasan Bobo tun a school idan yasama ido ka shiga uku

Tsaki taja ita kadai tace I'll do my possible best bazan bari wannan yaron ya raina niba, already nariga nasan waye shi tun a school yanzu maganinshi kawai zanyi

Falon Hajiya ta shiga dan gaisar da ita ta tarar batanan, Too ina taje this  Early morning ta fada a zuciyarta,
    chanza kaya tai sannan ta fara aikin daya kawota

Bobo ne ya shugo ya sameta tana shara, yace idan kingama kizo ina nemanki, tai kamar bata jiba

      "Tsawa yai mata yace Bakiji me nace bane?

Tace me kace?

Yace kizo kisameni a dakina idan kingama, Sai alokacin taji tabbas ashe haka yace tanasha bataji da kyau bane..Tow tacemai

Yabar kitchen din ya tafi part dinshi...

Yana fita kamar ta fashe da kuka meyasa zai dinga cewa tana binshi daki, Gashi Hajiya yau batanan, Wata zuciyar kuwa tace mata ko tananan mezata iyayi? Tunda iyayen nan ne marasa tsawatawa yaransu

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now