LAIFINA NE 12

76 7 0
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       ❤️ *LAIFINA NE*❤️
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*PAGE 1️⃣2️⃣*

Fauxeey na kwance wasu zafafan hawaye suka zubo mata, Tinanin haidar ta shigayi yanzu ko wani hali yake oho hankalinta ne yai matukar tashi dan mafarkai da takeyi kwana biyu akanshi, tambayar kanta takeyi anya tamai adalci? Wata zuciya kuma tace kin manta namijine AI duk abunda kikai daidaine nidai nace a'a
   Yauma zaune take Kanta na ciwo, Ummie ne ta dubeta "tace wai meke damunkine naga tunda muka Dawo nan sam hankalinki ba kwance ba Dan Allah ya Fauxeey menene? Murmushi tai mata tace" bakomai ni kinga tashima zanyi naga goma tayi nazo na tafi wajen aiki "Ummie tace uhmm hakane yar uwa, Yanda tai maganar yasa fauxeey tai saurin d'ago kanta ta kalleta Tasan taji maganar ne kawai bawai ta yarda na

   Dan haka fauxeey ta tashi ta shiga wanka, Simple makeup tayi sannan ta bude akwatinta ta dakko wani material me kyau Dan kasar indonosia ta sanya a jikinta, dinkin gifted gown ne ya amsa jikinta sosai, saboda Fauxeey tanadan tsayi gatada shape daisai gwargado, kayan ya amsa jikinta sosai kamar ready made kuma dinkashi akai, Ta dakko takalmi flat se ta yafa gyalen material din, Se kamshi takeyi ta dakko jakarta

Sallama taiwa mahaifiyarta sannan ta fito batare da tasan inda zata dosa ba,
   Tino da baba mairo tayi sannan tace bare naje gidan na gaishesu, tafiya takeyi ahankali tinani fal a zuciyarta yanzu ta ina zata farane dan akwai abubuwa da yawa agabanta

    Wani hadadden motane yake ta mata horn, Tai burus kamar bada ita akeyi ba, dan in akwai abunda ta tsana a rayuwarta be wuce a tareta a hanya, mutun min nan kuwa sai horn yakeyi take sauraranshi

Kasa hakuri yayi dan Yanaji da girman kai duk garin jos baiga wacce ta isa ya tsareta taqi sayawaba, Dan haka parking yayi Shida wani Abokinshi suka fito

   Abokinshine yace baiwar Allah bakiji muna miki horn bane aiko bakisan wayeba kya tsaya kiji me muke tafe dashi
     Wani harara Fauxeey ta watsa musu
Tace ku wasu irin Dakikai ne? Abokin muhsin ne Ya sake baki yace Kai! Ke Bakisan Wanene ba? Tace ko uban waye bandamu insaniba, inba iskanci ba zakuita wa mace horn!!

Abokin muhsin dinne yace duk yanda akai wannan bakuwace, Batasan waye kai ba, Muhsin shidai yana tsaye yana kallon ikon Allah, Wai yan Matan dake rububi akanshi, Yau wata banza keso ta gayamai ba sugar
   Hannu yasa ya gyara babban riganshi, kamshin turaranshi ya buge hancinta, kallon ido cikin iso sukai taga guy din ya hadu, wani murmushi ya sakar mata ita kuma Kara balla mai harara tayi hade da tsuke fuskarta dukda tanajin guy din ya hadu bashi zaisa taqimai rashin mutunci ba, shikam muhsin kafeta da ido yake tayi dan haka duk taji ta tsargu

    Muhsin na kallonta yanayinta ya chanza, yace" Ina zakije da safiyar nan?
    Fauxeey magana ta suma, Ina ruwanka dani? Ina ruwanka ma da inda zani? Ko maza wallahi wata sa'in kuncika Shiga abun da ba ruwanku ni banason shisshigi ehe

Muhsin tsayawa yai yana kallonta lalle wannan yarinyar da karfin hali take, sai alokacin ya Kara tabbatar da cewa lalle bakuwace ba Yar garin bace, dan da Yar garin ce zatasan waye MUHSIN

Abokin Muhsin kuwa ranshine ya baci, yace dallah see you, Daga ganinku talaucine ya koruku daga inda kke! Maganar ya Sosa Mata rai Kallon jikinta tayi, bata ga wani Abu a tare da ita ba, Sannan tace" mtsww yana daya daga cikin abunda yasa na tsana maza kenan saboda akwai Wanda sam basusan mesukeyi ba, Nonsense tace musu sannan ta wuce

Abokin muhsin har yakai hannu zai janyota dan ya fusata, Muhsin ya dakatar dashi yace Kai mata uzuri tanada dalilinta na fadan haka, Muhsin tsayawa yai yanabin bayanta da kallo at her age haka ace ta tsana maza lalle akwai dalili, Aranshi yace" zan so inji dalilin da yasa haka, kallon Abokinshi yayi yace" muci gaba da binta kawai, bazan bar yarinyar nan ba, Ina sonta

Abokinshine yai mamaki daga ganin yarinya, Shiga moto sukai duk inda ta shiga sai sun bita har ta tare napep ta je gidan baba mairo...bayan ta shiga sukaga gidan sannan suka juya duk a tinaninsu nan ne gidan su fauxeey

     ****
Fauxeey ta isa gidan baba mairo ta musu wuni se chan yamma, ta koma gida, Seemah taji dadin ganinta sosai, Da fauxeey zata tafi Ciro kudi ta basu sukai mata godiya.....

Bangaren Haidar kuwa
    Bayan kwana biyu mahaifiyarshi tai tambayar duniyar nan ya akai takardu suka bace yace shi Sam beda masaniya akan yanda akai suka bace

    Dan haka tace" OK baka saniba KO? Yace yes mummy tace OK yau zanje Company din, Gabanshine yaji ya fara bugun Tara tara, nan take yaji sam beda sukuni

    A chan company dinsu kuma Aisha ce Zaune da. Abokin aikinsu suna hira, Tace" kasan mene? Yace aa saikin fada, Ta fara magama tana cewa naji dadi sosai da aka kora Fauxeey da Haidar, kana Lura da abunda nake lura kuwa?

   Abokin nata mai suna hashimu yace kamar suna son juna KO? Yamutsa fuska tai tace haidar ke sonta kuma kaga fauxeey bata sonshi, yanzu hakama tabar garin, kaga dama inason haidar, Da muna good time to tun zuwan Shegiyar nan ya dena kulani sosai, kaga yanzu duk inda yake Zan nemeshi muyi soyayya, dama haushin nakeji idan na gansu da fauxeey tana magana hausarta bai fita sosai

Hashimu yace sosai saiki bada harama, tace kaida kasan komai Dan kawaima Ina ragamai ne Mu igala duk abunda mukeso sai munsan yanda mukai muka mallakeshi, Hashima yace" nasan haka

Suna magana ne Motar Hajiyar Haidar tai parking, fitowa tai tana tafiyar kasaita kallo daya zakai Mata kasan ta amsa sunan Hajiya lubabatu

Karaso tai Wajen dasu Aisha igala take, sunan da ake kiranta dashi kenan, Gaisawa sukai da mahaifiyar Haidar, Sannan tace Nine Mahaifiyar *Aliyou Abdaullahi dabai*

Dukansu mik'ewa sukai suna kare Mata kallo, lalle ta amsa sunanta kuwa, Cire Glass din idonta tai tace daga gani Ku ma'aikatane anan inason ganin manager

Aisha Igala Kashema Hashimu ido tai akan karyace komai

Ita tafara magana tace" Ranki shi dad'e Manager bayanan sedai kizauna kidan jirashi

Tace" No problem

Samun waje tai ta zauna tana dannan wayarta....................

Muje Zuwa

Yours Ummiey Xeey

Don't forget to follow
Vote and Comment






.

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now