KARSHEN PT ONE

370 14 5
                                    

  *NADAMAR DA NAYI*

           _WRITTEN BY_
           *MRS OMAR*

              _STORY BY_
       *HAUWA M JABO*

          _DEDICATED TO_
           *BEEBAH LUV*

    
         _PAGE 30_
              🔚


Rayuwa Fatima suke da Bilal tamkar wa da ƙanwa kamar yanda ya umarceta ta ɗaukeshi haka kuwa ta ɗauke shi, zasuyi wasa da dariya amma babu wani maganar aurattayya a tsakaninsu.
Fatima tana waya da Musaddik sosai amma har yau bata nuna masa ta sake wani aure ba dan tana tunani wannan lokacin idan har ta faɗa masa kamar ta rasashi ne gabaki ɗaya shiyasa tayi shiru bata faɗa masa ba.

A kwana a tashi babu wuya wajan Allah gashi yau ta cika wata ɗaya a gidan Bilal, zaune take a parlour tana danna wayarta Bilal ya shigo ɗauke da murmushinshi yana faɗin.

“Matar wucen gadi kina nan zaune kenan”

Dama haka yake kiranta tunda akayi auran kuma ya lura tana son sunan shiyasa ya ci-gaba da kiranta haka.

"Hmm wallahi kuwa kawai dai ina trying number Musaddik ne yau taqi shiga”
“what!number Musaddik Fatima a gidan nawa kefa matar aure ce ko kin manta?”

Baki Fatima ta sake tana kallonsa sai da ya tsaya da magana tace

“Yaya Bilal yaushe ka fara kallona a matsayin matarka koka fara sona kar zuciyar ka ta fara kishina? ai kam idan ko har haka ne zanyi maka tsanar da ban taɓa yiwa wani ba wallahi”

Cikin sanyin murya ya zauna kan kujerar dake fuskantarta yace

“Ba haka bane Fatima gani nayi kawai akwai igiyoyin aure a kanki shiyasa na faɗi haka dan naga hakan bai dace ba”
“Amma ni a tunanina wannan ba problem bane  ya Bilal domin kuwa ko ba dade ko bajima dole zamu rabu na auresa saboda wallahi zuciya ta shi kadai na mallakawa ita bani da wani buri daya wuce na aureshi ya Bilal zan iya shanye komi saboda Musaddik wallahi”

'O Fatima yaushe zaki gane masu sonki tsakani ga Allah, wallahi bansan haka so yake ba saida na aureki tabbas Faruok son daya ke maki muna ganin yayi yawa, tabbas nasa ko rabin nawa bai kai ba dan zaman da nayi dake na gani irin martabar dake gare ki, i promise u Fatima sai nasa zuciyarki ta manta da wani babin soyayyar Musaddik a duniya ina sonki Fatima..'

“Ya Bilal magana nake maka kayi shiru kana tunani ko kaima tunanin masoyiyar taka kake”

A hankali ya dawo daga dogon tunanin daya lula, murmushi ya sakar mata yace

"Hmm kamar kin sani, tunanin masoyiyata nake ko ya zata amince dani a wannan lokacin dan gani nake nafi kowa sa'ar mata”
“Ayya kada ka damu muna rabuwa kawai saika aureta nima na auri wanda nake so”
“ko?”
“Yes”

Ta kashe mashi ido ɗaya da sauri ya lumshe ido danjin tamkar shock ya kamashi.

Fatima macece da ko wane namiji yaga surarta dole ya rikice domin kuwa Fatima Allah ya bada irin sigar da ko wane irin ɗa namiji ke so uwa uba muryarta mai kama da sarewa idan tana magana tamkar falguni na raira waka fatar jikinta kam tamkarta pragya haka ma hasken idanuwanta tamkar na bulbul kai Fatima dai macece da koke mace 'yar uwata sai ta baki sha'awa, shiyasa yanzu ɗan zaman da sukayi da Bilal yaji duk duniya babu macen dayake son  zama da ita, sama da ita.

Wayar shice tayi ƙara da sauri ya juya yana kallon wayar sunan Faruok ne da ya gani yana yawo a screen ɗin wayar yasashi saurin kai hannunsa ya ɗaga

“Hello namijin duniya meke tafiya?”
“Please idan kana gida ka ɗauko Fatima kazo da ita nan CT hospital Daddy ba lafiya”

Cikin sanyin murya Faruok yayi magana tamkar yana kuka.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 12, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now