NADAMAR..22

180 10 2
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

      *NADAMAR DA NAYI*

              _WRITTEN BY_
               *FATIMA ISAH*
               ( _MRS OMAR_)
          

                  _STORY BY_
        *HAUWA M. JABO*

            _DEDICATED TO_
              *BEEBAH LUV*

   
                 _PAGE 22_
                 ********

"Ina zaki ai kya bari mu tafi tare ko? anya Fatima kinyiwa rayuwarmu adalci kuwa? Lokaci ɗaya duk kin ruguza komi yanzu ga abinda kika jawo mahaifinki yayi fushi dake akan Wannan makauniyar soyayyar dana tabbata yaron nan ba son gaskiya yake maki ba kece ke sonsa bashi ba."

Jajayen idanunta ta ɗago ta kalleshi dasu da suka koma  kamar gauta tayi murmushi takaici muryarta na rawa ta ce.

"Hmm ya Faruok kenan u will never understand my love for Musaddik jinina ne zan iya ganin komi dan ganin na chechi soyayyarsa. Musaddik namiji ɗaya tamkar da dubu, farin cikina shine naga na auri Musaddik ba wanda zuciyata tafi tsana ba."
  "Shikenan Fatima na yarda zuciyar ki bazata taɓa sona ba, duk abinda nayi mata ni kam nasan da sonki zan mutu, saboda duk lokacin danayi yunkurin  cire soyayyarki a zuciyata to a ranar bazan taɓa barci da lafiya ba, Fatima na barki ki auri wanda kike so."

Muryarsa tayi rauni sosai dan har saida kwalla suka taru a gurbin idonsa, da sauri ya fito daga motar shi daidai lokacin Bilal na shirin parking itama jiki babu ƙwari ta buɗe ƙofar ta fito, ita take gaba suna binta a baya a babban parlourn kakar tasu suka yada zango dan ganinta zaune ta kurawa TV ido tana kallon wani shiri daga tashar Arewa24 mai suna rayuwar matan arewa ana tattaunawane akan yawan sakin aure a arewa.
Ganninsu yasa ta maido hankalinta wajensu cike da mamaki.

"A'a umaru kune da safiyar nan inji dai lafiya?"
 
Murmushi sukayi suka samu waje suka zauna da sauki takai dubanta wajen Fatima ta ce.

"To fatsima har dake ake tafe anya tafiyar nan ta lafiya ce?"

  Ido Faruok ya lumshe ya ɗan numfasa kafin ya ɗago kai ya dubi kakar tasu ya ce.

"Iya da sauki dai?"
  "Kamar ya Umaru faɗa min meke faruwa."
"Iya akwai matsala babba na aikata abinda yasa nazo daga baya ina dana sani na saka yarinyar mutane a cikin matsala sanadin haka yasa Daddy yayi ikirarin bazata zauna mashi a gida ba."
"Kaga Umaru ni fa ban gane inda wannan maganar taka ta dosa ba ka fito fili ka gaya min."

Kai ya girgiza ya shaqi iska ya fitar sannan cikin murya can ƙasa ya ce.

"Na saketa Iya nayi mata sakin da ta haramta a wajen..."

Bai ida magana ba Iya ta buga yare tana fad'in

"Hande, hande en boni, yanzu Umaru irin sakayyar da zakayiwa iyayenta kenan? Anya Umaru."
"Iya kiyi hakuri banso nasa baki ba amma wallahi wannan matsala duk tana wajen Fatima.."

Hannu Faruok ya dagawa Bilal da sauri yana fadin.

"Please Bilal just keep quite u know i love Fatima don't say anything abt her please."
  "Taya zanyi shiru bayan ga gaskiya sai kaqi faɗinta ka ɗaurawa kanka laifi."

Murmushi Faruok yayi dan irin maganar da Bilal keyi da hausa yasan Iya zata iya yarda da abinda Bilal zai faɗa yasa ya ce

"Bilal wace gaskiya bayan wadda na faɗa ko kana so na ɗaurawa yar mutane laifin da bata aikata ba? No Bilal i beg u just keep ur mouth shut  please for my sake."
  "Alright I will do as u  say."
  "Thank u."

Dubanshi Faruok ya maida ga Iya ya ce.

"To Iya kinji abinda ya faru dan Allah Fatima ta zauna nan kafin Daddy ya sauko kuma nasan kece kawai zakiyi masa magana yaji."

"Umaru kenan ƙarya kake abinda ka faɗa min ga abokinka nan naso ya faɗi gaskiya ka hanasa anya Umaru."
  "Iya kenan iya gaskiyar kenan na faɗa maki kuyi hakuri iya da irin kunyar dana baku ban cika alkawarin ba."

Shiru Iya tayi tana kallonshi saida ya gama magana ta ce.

"Naji Umaru amma ka sani zata zauna a nan na wani lokaci amma duk  ranar da gaskiya tayi halinta na gane ita ce keda laifi to tabbas nima sai ta bar min gida."
"Insha Allahu bama za'ayi haka ba."

Ita dai Fatima duk tana jinsu bata tanka ba, sun ɗan jima suna fira kafin suka tashi har zasu fita Faruok ya dawo ya cewa Iya yana son zaiyi magana da Fatima tashi Iya tayi ta basu waje, inda take zaune bata gusa ba yazo ya zauna ya kura mata manyan idonsa ya ɗan ɗauki lokaci yana kallon ta amma ita kam taki ɗago kai.

"Fatima yanzu cikin ƙwanakin da bazasu wuce wata biyu ba anyi komi an gama, Fatima ada duk son da nake maki na wasa ne ban gasgata haka ba sai jiya a darenmu na farko Fatima kina da wata baiwa da bako wane namiji bane ya kamata ya zama mijinki nagartacen namiji ne kawai ya kamata ya zama mijinki Fatima kina da baiwa."

Sai da ya numfasa kafin yaci gaba da cewa.

"Fatima ki rufawa kanki asiri kada kiyi kuskure auren makahon nan."
"Dakata ya Faruok dama tunda naji ka fara magana nasan sai ka kushe abun kaunata, to kasani wallahi ban taɓa NADAMAR rabuwa dakai ba, ina farin cikin sosai dan yanzu zan mallaki abun kauna ta."

Tana rufe baki ta wani tashi zata wuce Faruok cikin zafin zuciya ya fincikota da karfinsa ta faɗi masa.

"Kina tunanin wannan makahon shine farin cikin ruhinki? alright naji kuma na yarda ke kina son sa amma shi ba son gaskiya yake maki ba."
"Naji a tunaninka kenan ka barni na shiga ciki kana taɓa ni ko ka manta ni ba matarka bace yanzu."
"Hahaha sai ki bari ki gama ida kafin ki fara ƙiran kanki a bazawara amma har yanzu ke matar aure ce."

Fuska ta yamutsa tayi shiru dan tasa duk maganar da tayi Faruok na dai_dai da ita.

"To ki ɗaga ni kinji jiki mai daɗi ba irin na makahonki ba kin kasa tashi."

Ido ya kashe mata ɗaya cike da kunya Fatima ta tashi da sauri ta nufi dakin da suke sauka idan sunzo.
Faruok har ta shige yana kallonta.
Faruok na fita Bilal ya haushi da bala'i.

"Yanzu major abinda kayi ka kyauta wannan wace irin soyayya ce kuke daga kai har ita a rashin sani?"
"Hmmm Bilal kenan wannan ita ce soyayya ta Gaskiya any way mubar wannan maganar ma ida a office."

Juyawa yayi ya shiga mota yabar Bilal a tsaye dan yasan halin Bilal da nacin magana.

*********

Su Fatima kenan tana shiga ɗaki ta maida ƙofa ta rufe ta ɗauko waya ta danna number Musaddik tamkar yana jirin kiranta ya ɗaga da sauri.

"Amincin Allah ya tabbata a gare ka yakai kyakkyawan mijina na har abada."
"Tare dake sarauniyar matayen duniya."

Murmushi tayi cike da jin daɗi ta ce.

"Noor Hayat kenan anya kana missing ɗina."
"Kamar ya mekika gani."
"Hahaha babu komi wasa nake maka, albishirinka."
"Goro amma idan ba albishir ɗin takardar sakinki zakiyi min ba to kiyi shiru da bakin ki."
"Oh my God me kakeci na baka na zuba, yau Faruok ya sake ni saki har uku."
"Oh my God are u sure."
"Yes dear mun kusan kasancewa tare har abada."

Knocking ɗin da ake ne yasa maganarta ta tsaya cak tana kallon ƙofa..

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now