NADAMAR DA NAYI 27

176 10 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

    *NADAMAR DA NAYI*

             _WRITTEN BY_
            *FATIMA ISAH*
            ( _MRS OMAR_)

             _STORY BY_
        *HAUWA M. JABO*

           _DEDICATED TO_
            *BEEBAH LUV*

               _Page 27_

           *K'ORAFI*

_To masha Allah masoya wannan littafi mai suna NADAMAR DA NAYI ina jin dad'in yanda kuke bani goyan baya  dari bisa dari nagode, sannan ina ganin k'orafin wasu daga cikinku akan idan Fatima ta auri Bilal littafi ya b'ace, to ku sani babu abinda zai bata wannan littafi domin kuwa taya Fatima zatayi NADAMA har ta gane kuskuran abinda take ba daidai bane ku sani wannan littafin yanzu na farasa domin kuwa ko rabi banyi ba, kudai kawai kucigaba da bina nagode_

        *******

Kai Faruok ya dafe dan ya rasa abinda zaiyi, domin kuwa da kunya ya fito kiri_kiri ya cewa Dad baya sonta muryar Dad ne ya daki dodon kunnensa da sauri ya ɗago kai.

"Faruok kayi shiru baka ce komi ba? babu dole fa cikin wannan lamarin idan har tayi maka kana sonta fine, ni kam ta ɓangarena babu matsala"

Cikin sanyin murya yace

"Eh to Dad dan Allah a ɗan bani lokaci nayi shawara"

Shiru Dad yayi na wasu mintinan da basu wuce uku ba kana yace

"To shi kenan Faruok duk abinda kace yayi ai kai zaka zauna da matar ba muba, dan haka babu matsala"

Juyawa yayi ya kalli Hafsat data sada kanta ƙasa kamar duka kenan yace

"To kinji abinda yace Hafsat sai kiyi hakuri a bashi lokaci Allah yayi maki albarka"
"Amin Dad"

Ta faɗa tana mai miƙewa shidai Faruok ido kawai ya bita dashi dan mamaki take basu, wata zuciyar nace mashi anya Hafsa ce lokaci ɗaya ta canza.
Mom ce ta katse mashi tunaninshi da cewa.

"Faruok muje ko kokana nan ne?"

Kai ya girgiza mata alamar a'a, cikin sanyin jiki ya tashi Dad duk yana kallonsa Mom tayi gaba shi kuma yayiwa Dad ban kwana kana ya bita daga baya a ɗaki ya sameta yana shiga ta haushi da faɗa.

"Haba Faruok wai me kake so ka zama ko kaima kana son ka biyewa yar uwarka ne ka dinga bijerewa maganarmu, meye wanda fatima take dashi wanda  hafsa bata dashi?"
"Mom tarbiya, Hafsa sanin kanki ne bata da tarbiya Fatima kowa yasan tana da tarbiya"
"Tarbiya kake faɗa Fatima na da tarbiya ta ina Fatima take da tarbiya? banga tarbiya a tare da ita ba Hafsat ko naga zallar tarbiyarta tunda har tana son abinda iyayenta ke so."
"Please Mom don't see dat wallahi Fatima nada tarbiya soyayya ce kawai ta rufe mata ido Mom kada soyayyar da kike min yasa ki manta irin tarbiyar da kika bawa ƴarki wallahi Mom Fatima mai tarbiya ce, saboda duk soyayya da Fatima ke nunawa Musaddik baisa ta saida mutumcinta ba."

Mom ta gano abinda yake nufi dan haka ta samu kan kujera ta zauna ta lumshe idonta saboda duk maganar da suke a tsaye suke yinta.

"Amma Faruok meyasa bazaka amince ka auri Hafsat ba? ko dan huce haushi please ka aureta"
"To naji Mom zan duba kada ki damu"

Ya faɗa yana mai ƙara matsawa kusa da ita yace.

"Haba uwata ta kaina kinsan fa ɓacin ranki dai_dai yake dana faɗa cikin ruwan zafi dan Allah kada kisa damuwa a ranki yanzu ma zanje na taho maki da autarki"

Faruok yakai ƙarshen magana yana dariya cikin tsokana.

"Faruok kenan ka barta kawai ta ƙarasa zamanta can hankalina ma zaifi kwanciya"
"A'a Mom kada kice haka Dan Allah kiyi hakuri na dawo da ita nan dan wallahi kwata_kwata hankalina baya kwance barin ta a gidan Iya kinsan dai Iya ba hanata fita zatayi ba nan kam dole ta natsu ta zauna waje ɗaya"
"A can kana tunanin yawo take?"
"A'a ba haka nake nufi ba, ina ma zataje kawai dai na faɗi haka ne"

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now