NADAMAR..23

239 16 4
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

      *NADAMAR DA NAYI*

             _WRITTEN BY_
             *FATIMA ISAH*
             ( _MRS OMAR_)
         

                _STORY BY_
        *HAUWA M. JABO*
     
             _DEDICATED TO_
              *BEEBAH LUV*

                _Page 23_
               **********

  Iya ce ta turo ƙofa ta shigo cikin sauri Fatima ta kashe wayar ta aje dan bata son iya ta gane gaskiya.
Iya kasaitatcen murmushi tayi tazo dai_dai inda take ta zauna tana fuskantarta tace,

"Hmm Fatsima kenan yanzu irin rayuwar da kika saka kanki kenan? gaskiya albasa batayi halin ruwa ba, duk irin tarbiyar da mahaifiyarki ta baki ace lokaci ɗaya kin manta da ita anya Fatsima."

"Iya kenan dan Allah me nayi? ai ya kamata ku yarda dani tunda har wanda nake zaune dashi ya faɗa maku gaskiya"
 
Harara Iya ta watsa mata sannan ta ce .

"Anya Fatsima a habdini danyobe ma bo?dikka a vo'itini hakkiloma, gaskiya rayuwarki ni kam akwai gƴara."

Fuska Fatima ta ɓata ta wani juya ƙwayar idonta tace,

"Hmm iya kenan komi wadi ma,bawo aya ya Faruok yeccimma gonga, ko a yidi mi fewa on? komi fa na Allah ne dama can Allah ya rubuta ni ba matar sa bac..."

Bata ida ba iya tasa hannu ta kaiwa bakinta duka Allah yaso bada ƙarfi bane.

"Da Allah rufa min baki marar mutunci kedai dama can bakya son auren kuma kin kashe hankalinki ya kwanta, ai da yake duniya ce ta isa kowa riga da wando har dama zanin ɗaurawa."
"Oh my God! please Iya believe me wallahi ba  karya nake ba."

Murmushi takaici Iya tayi bata tsaya bata amsa ba, ta fita abinta..

*Bilal da Faruok*

Faruok da Bilal babu inda suka zarce sai gidansu duk da yasan bashi da wata sauran k'ima a idon iyayyen nasa domin a tunaninshi ya gama basu kunya.
Suna shiga parlour sukaci karo da Hafsat zaune tana aikin danna waya tana ɗago kai ta gansu cike da farin cikin da kissa ta tashi tana fad'in

"Oh my God! ya Faruok I'm very happy today wallahi, ban taɓa jin ina k'ara sonka ba irin na yau ka gama min komi wallahi tunda ka saki stupid girl dinan dama can ba class ɗinka bace look at me kasan nice dai_dai da kai."

Tunda ta fara magana Faruok da Bilal suka tsaya kamar wawaye suna kallonta da irin yanda take karairaya sai kace irin 'yar rawar makosa.
Murmushi takaici Faruok yayi ya girgiza kai yace

"Hafsa kenan u will  never change, wallahi duk namijin daya aureki ya ɗaukarwa kansa bala'i danke ba matar arziki bace."

Ƙara nufoshi tayi da gaske tana shirin shiga jikinshi ya daka mata tsawa yana fad'in

  "stop Hafsa don't ever try to touch me with ur dirty hands! hmm wallahi sai kinyi dana sani."

Bilal gani yayi ran faruok ya ɓaci matuka yasa yayi saurin janshi yana faɗin.
"Please major just calm down, ba batunta ya kawo mu ba muje inda mukazo please."

Tsaki yayi ya girgiza kai captain Bilal yaja hannunshi da sauri suka shiga ciki ɗakin Dad suka nufa kaitsaye sukayi knocking cikin kasaita da murya irinta dattawa Dad yace su shigo Bilal ya tura kai Faruok na biye dashi.
Kai Dad ya ɗago ya kalle su sannan ya mai da kansa da abinda yake.
Dai_dai kusa da shi suka samu waje suka zauna kasan carpet.

"Barka da kwana Dad?"
"Yauwa barkanku dai, yanzu kuke tafe lafiya bakuje aiki ba?"
"Lafiya qlau Dad.. Dama Faruok ne yazo ya baka hakuri akan abinda ya faru."

Kai Dad yad'ago ya daina abinda yake ya kalli Faruok yace

"Akwai abinda kayi min wanda ni bansani ba? Bilal ni a tunanina Faruok bai taɓa aikata min wani laifi ba da har zan rike shi a raina."

Gyara zama Bilal yayi cikin sanyin murya yace

"Dad hak'uri yazo ya baka akan abinda yafaru tsakaninshi da matarsa Fatima yasan bai kyauta maku ba.."
"Dakata Bilal naji ka kira wani suna da bansan dashi ba."
"Dad dan Allah kayi hakuri ka sauraremu ni kaina nasan ban kyauta ba abinda na aikata maku amma don Allah Dad kada ka hukunta Fatima akan laifin da bata sani ba."
"Faruok kenan bakada hankali soyayya ta rufe maka ido har kana shirin manta waye kai, to bari kaji Faruok ka sani banida wata 'ya mai suna Fatima bansan da ita ba."
"Amma Dad.."
"Dakata Faruok  nobody can change my words dan haka kada ka ƙara zo min da maganar yarinyar nan idan baso kake ranka ya ɓaci ba."

Jiki a sanyaye suka fito suka nufi ɗakin Mom.
Ta amshesu hannu biyu bata nuna masu komi ba kuma har a ranta ta gane irin soyayyar da Faruok kema Fatima ne yasa ya ɗaurawa kansa laifi.
Ita ce ta dinga bashi hak'uri da nasiha mai shiga jiki sannan ta kuma yimasa godiya sosai...

********

*Bayan wata d'aya*

Fatima da Musaddik sun buɗe wani babin soyayya, a koda yaushe phone d'inta na kunnenta idanuwansu sun rufe basaji basa gani.
Yau Fatima ta tashi da wani matsanancin ɓacin rai wanda ta rasa wanda zata faɗawa damuwarta domin kuwa yau kusan watanta ɗaya da sati ɗaya bataga menstruation ɗinta ba hankalinta ya tashi matuqa gashi babu yanda za'ayi ta faɗawa Musaddik wannan maganar shawara kawai ta yanke taje asibiti idan ma ciki ne zata fitar dashi a sirri babu wanda ya sani
Shiryawa tayi hankali kwance ta samu Iya zaune ta ce mata zataje gidan Pendo Ummi ba lafiya Iya tasan ƙarya take amma bata nuna mata ba  tace

"Sai kin dawo amma ki sani duk inda kike Allah na kallonki dan haka akoda yaushe ki zama mai tsoron Allah."

Tana faɗin haka tayi shiru da bakinta  Fatima kai ta ɗaga alamar toh, jiki a sanyaye ta tashi ta tafi.

••••     •••••
     °°°°°
••••••••  •••••

Faruok ne da captain Bilal zaune a office ɗin Bilal sunyi shiru suna kallon juna da alama magana ce zasuyi mai mahimmanci captain Bilal ne yayi gyaran murya yace

"Major kace kana son muyi wata magana mai mahimmanci amma kayi shiru ka kasa magana, please major what is ur problem please tell me."

Ido Faruok ya lumshe bayan wasu mitina ya buɗe su saida ya juya kwayar idonsa sannan ya fara magana cikin sanyin murya.

"Bilal ina cikin damu tun ranar dana saki Fatima nike cikin matsanancin tashin hankali ganina kawai ake ina tafiya Bilal But i don't know what i'm doing, tabbas Bilal kafi kowa sanin waye Musaddik sai gashi duk matsalar da ake samu da Fatima akansa ne, Bilal na rasa abinda zanyi shiyasa na yanke shawarar nazo wajen ka na roƙi alfarma.."

Shiru yayi yana kallon Bilal duk da shima shi yake kallo.

"Anhm ina jinka Allah yasa zan iya."
"Zaka iya Bilal."

Ajiyar zuciya mai ƙarfi Faruok ya sauke sannan ya furta da sauri.

"Bilal inaso ka auri matata Fatima."

Da sauri Bilal ya miqe tsaye yana faɗin.

"What? Na auri matarka Fatima kana hauka Major Faruok kana nufin auran kisan wuta kenan?"

Ido Faruok ya lumshe ya girgiza kai yace.
"Calm down!  please Bilal listen to me ."
Inda yake zaune ya koma ya zauna yana fuskantar Faruok daya k'ura masa manyan idanunshi.

  "Please Bilal ka fahimce ni wallahi ba auran kisan wuta nake nufi ba, inaso Fatima ta auri miji mai NAGARTA ne, kuma na tabbata kaine kawai wanda zai iya riƙe min ita da k'ima da daraja da mutunci."
"No major i can't do that"
"U can Bilal."
"No Mojar taya zan auri matar aminina da yayi min komai a rayuwata idan nayi haka naci amanarka."
"Bilal wannan alfarmar kawai zakayi min ka gama min komi a rayuwata."

Shiru Billal yayi yana kallon Faruok ya kasa cewa komi..

_To makaranta ana wata ga wata wannan page sunansa *BAKAR SAKA*_(littafin k'awata Fatima El Ladan) ko Bilal zai amince ya auri matar abokinsa, to wai ina labarin ita kanta Fatima mai zuwa asibiti kenan tana da juna biyu? Wannan amsa na barwa Maman Esha da Zahra darma..

Muje zuwa

Nice dai taku har kullum

Mrs omaru

NADAMAR DA NAYIWo Geschichten leben. Entdecke jetzt