NADAMAR DA NAYI page 4

262 25 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

     *NADAMAR DA NAYI*

        
             WRITTEN BY
           *MRS OMAR*

              STORY BY
        *HAUWA M. JABO*

          DEDICATED TO
             *BEEBAH LUV*

  _This page is for you sis  Aisha Ibrahim saboda irin so da kauna da kikewa Fatima na baki k'yautar wannan page d'in naki ne *KE D'AYA*_


            _Page 4_

Cikin isa Hafsat ko kunya babu ta k'araso wajen Faruok kamar zata shige cikin jikinshi har yana jin saukar lumfashinta. K'ara shak'e murya tayi kamar ta babyn roba ta ce.

"Please  Yaya Faruok ya kamata ka gane irin soyayyar da nake maka wallahi idan har ka amince zaka aure ni, to wallahi zan daina duk wani abinda nake please Yaya.."
"Stop Hafsat what are you doing ?"

Cikin fushi yayi mata wannan tambayar dan ganin zata faɗa saman k'irjinshi wanda a kullum idan tana kallon wajen ke sata k'ara son shi saboda a rayuwarta tana son namiji mai faɗin k'irji. Kuka ta fasa, ta faɗi k'asa tasa hannu ta dafa zuciyarta kafin taci gaba da magana.

"Yaya Faruok  kaine mutum na farko da ya kamata ka tausaya min karfa ka manta da irin tarin alkhairin da mahaifinmu yayi maka. Haba Yaya Faruok sonka ɗaya ne tak a cikin zuciyata wallahi idan har baka aure ni ba to zan.."
"Dakata Hafsat I don't know what  u are talking about, kina 6ata yawun bakinki dan zuciyata bazata ta6a amincewa dake ba, dan zuciyata tsarkakakka ce tana son ta auri mace mai *NAGARTA* wallahi Allah Hafsat ko ban auri Fatima ba to bazan aureki ba."

"Wayyo Allah na shiga uku Yaya Faruok ya zanyi da sonka a cikin zuciyata?"

Kafaɗarshi ya ɗaga ya ta6e baki ya ce.

"This is your problem."

Yana kai karshen maganarshi ya tafi ya barta nan tana kuka
cikin isa yake takunshi har ya isa upstairs ɗin da zai sadashi da bedroom ɗinshi, yana tafe yana 6alle ma6allan rigarsa. Direct hannu yasa ya buɗe dakin, lokaci ɗaya kamshin turaren ɗakinshi ya gaurare ko ina. Babu laifi kana shiga ɗakin kasan maishi dan gata ne, ɗauke yake da Italian bed yasha bedsheet  mai ɗauke da flowers a gefe ɗaya kuma wardrobe daga hannun dama dressing mirror ne yasha kayan shafa iri_iri,  plasma kawai dake ɗakin abin kallo ce. Bayan ya shiga direct wajan gado ya nufa ya zauna gefan gadon ya fara cire booth ɗin k'afarshi cikin lokaci kaɗan ya cire. A hankali ya k'wanta yayi rigingine yana kallon sama sai da ya juya k'wayar idonshi sannan ya lumshe idonsa.

'Oh ya Allah ka mallaka min Fatima ta zama uwar ya'yana Allah kasan abinda ke zuciyata Allah ka cika min wannan burin'

Knocking ɗin da yaji anayi ne yasashi dawowa daga dogon tunanin da yake, cikin isa ya nufi k'ofar hannunshi yasa mai ɗauke da gashi k'wance yasa ya buɗe k'ofar ɗakin. Ganin Mom Fatima a tsaye yasashi saurin sakin fuskarshi yana faɗin

"A'a Mom kece da kanki? yanzu nake shirin na watsa ruwa kafin  na shigo."
Fuskarta ɗauke da murmushi k'wance ta ce.

"Ba dole ba nashigo naga lafiyar ɗana."
"Kai Mom irin wannan kauna haka da kike nuna min tayi yauwa."

Kai ta girgiza kafin ta zauna a gefan wata kujera dake gaban gadonsa. Dai_dai wajan k'afarta ya zauna kan carpet kansa na kallon k'asa tafara magana.

"Faruok babu abinda zance dakai saidai nace Allah ya saka maka da alkhairi hakik'a kai ɗane wanda ko wane iyaye zasuyi alfahari dashi tun kana yaro kake sani farin ciki har zuwa yanzu. Faruok bansan da abinda zan saka maka ba, abinda kake so mallakina ne sai dai gashi yanaso yafi k'arfina wallahi Faruok idan har Fatima bata aureka ba bazan tabba yaf..."

Cikin sauri Faruok baisan lokacin da yayi sauri kai hannunsa dai_dai bakin Mom Fatima ba kamar zaiyi kuka ya ce.

"Please Mom kada kiyi mata baki. Na tabbata in bacin soyayyar makahon nan da tarufe mata ido wallahi da ta amince da zabin ku, amma duk da haka addu'a zamu dingayi mata har Allah yasa zuciyarta ta dawo wajena."

Tunda ya fara magana Mom Fatima ta kura mashi idanuwanta tana sauraron abinda yake fada.

"Amma Faruok kana ga haka zamu zuba mata ido muna kallonta sai kace ba yarmu ba, no this is impossible, bazan bari y'ar dana haifa  tafi k'arfinaba.

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now