NADAMAR DA NAYI page 2

304 24 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

     *NADAMAR DA NAYI*

        
             WRITTEN BY
           *MRS OMAR*

              STORY BY
        *HAUWA M. JABO*

             DEDICATED TO
             *BEEBAH LUV*

                _PAGE 2_

*Wannan page naku ne*
Mrs Sani officer's quarters
Surayya Hamdana
Maman Amira dizu
Aisha Aliyu
Samira Uncle d
Nanus oga abu
Maryam Elyas(ant Meeral)

         *******

Wata mata ce fara 'yar kimanin shekara arba'in da wani abu, ta iso gabanta fuskarta a ɗaure babu alamar fara'a, a tare da ita.

  "Wallahi Fatima kin bani mamaki, ashe har akwai lokacin da mahaifinki zai zab'a miki abu ki ce a'a, har kina tunanin zamu so wani sama da Faruoq? ba mahaifinki ba koni ina mai farin cikin auranki da Faruoq saboda Faruoq yaron k'irki ne bazan tab'a man tawa da irin karamcin da Faruoq ya nuna min ba."
Kuka ta saki cikin sutin kuka ta ce.

"Haba Mom a matsayinki na mahaifiyata ya kamata ace kin goya min baya dan samun farin cikin rayuwata, Mom ina son Yaya Faruoq kamar yanda kike sonshi amma bada aure ba..."

Cikin fushi ta nufi wajan 'yar tata.

"Bada aure kike sonshi ba to da ubanki kike sonshi?"

"Mom baki fahimce ni ba nasan Yaya Faruoq yana da duk wani abu da ɗiya mace zata so shi, kuma wallahi da zuciyata babu son Musaddik a ciki wallahi da naso Faruoq Mom ki fahimce ne please Mom."

"Maganar banza."

  Da sauri ta duka k'asa ta kama k'afar mahaifiyar tata tana rokonta.

"Please Mom listen to me, wallahi duk maganar da nake maki daga cikin zuciyata ne. Son Musaddik ya riga da ya mamaye zuciyata wanda yasa a duk lokacin da akayi gigin rabani dashi to  wallahi zan iya rasa rayuwata."
Murmushi Mom tayi ta girgiza kai.

"Humm Fatima what do your father said, you know nobody can change  him,  dan haka kawai kiyi hakuri ki amshi zab'insa."

"Toh ni dai gaskiya Mom bazan iya zama da ko wane miji ba in ba Musaddik ba."

"Fatima kenan aure duk sunansa aure na tabbata idan kika aure Faruoq zaki soshi fiyi da son da kikewa wannan."

Tashi Fatima tayi daga durkushin da take ta koma kan gado ta zauna taja majina ta ce.

"Mom na tabbata ke da Dad bazaku tab'a fahimta ta ba, wanda ya tab'a soyayya ne kawai zai fahimce ni. Mom kada ki manta duk sauran 'yan uwana babu wanda aka tab'a yi mashi auran dole sai ni Mom yanzu za'ayi min?"
Bakin gado Mom tazo dai_dai kusa da ita ta zauna tasa hannu ta dafa ta.

"Please Fatima promise me, bazaki tab'a kin wannan zab'in na mahaifinki ba, wallahi Fatima saboda so da k'auna da Alhaji ke maki yasa ya zab'a maki miji mai *NAGARTA* kamar Faruoq.."
Ɗan lumfasawa tayi kafin tacigaba da magana.

"Sauran da kike faɗi baiyi masu auran dole ba idan kinyi tunani ai zakiga ba tarbiyarku ɗaya ba, abinda yasa Alhaji ya zab'a maki Faruoq kenan dan irin tarbiyar da ya ga na baki. Humm Fatima sai gashi yanzu soyayya nason rufe maki ido ki manta da alkairin mahaifinki. Dan Allah Fatima ki taimaka ki tausaya min kada mutan gidan nan suyi mana dariya wallahi Fatima da ina da wata y'ar dana bama Faruoq ita dan ki samu farin cikin rayuwarki."
Magana Mom take kamar zatayi kuka hak'ika Fatima ta tausayawa mahaifiyarta dan dai kawai babu yanda zatayi da soyayyar Musaddik a zuciyarta ne.
Gani tayi ɗiyar tata bata da niyar k'ara magana yasa tatashi sai da ta kai dai_dai bakin k"ofar fita kafin ta ce.

"Idan kinga dama ki fita ga Faruoq can a parlour yana jiranki salan idan kinje kiyi mashi yanda kika saba akoda yaushe.

Baki ta turo kamar zinguro. Mom bata tsaya jin amsarta ba ta fita da sauri.

  Cikin fushi taja mayafinta ta nufi parlour kamar zata tashi sama.

Zaune yake kan kujera one sites yayinda ya ɗaura k'afarshi ɗaya kan ɗaya, sanye yake da kak'inshi na soja color army green, sunyi mashi k'yau sosai kamar dan jikinshi akayi kayan, k'yakk'yawan matashi ne mai jini a jika dogo ne marar jiki sai dai yana da cikar gaba, shiba bak'i ba kuma ba fari ba, zamu iya kiransa da chocolat color watau (wankan tarwaɗa ) yanada hanci kamar biro fuskarshi dogowa ce yanada manyan idanuwa bakinshi ɗan k'arami ne ga wata suma mai laushin gaske a kanshi daga nesa yana da cika ido. *FARUOK AHMED LAMIDO* kenan namijin duniya.
Tunda ta shigo kanshi ke duke a kan wayarsa yana dannawa, yayi kamar baisan ta shigo ba dan kuwa ko sallama batayi ba. Sai da yaga bata da niyar magana yasa ya ɗaga kansa ya kora mata ido  kamar zai cinye ta.

Urs mrs omar

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now