NADAMAR.. 21

180 14 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

     *NADAMAR DA NAYI*

            _WRITTEN BY_
            *FATIMA ISAH*
           ( _MRS OMAR_)

             _STORY BY_
        *HAUWA M. JABO*

           _DEDICATED TO_
            *BEEBAH LUV*

              _Page 21_
              *********

      _Dis page is for you my dear Jiddah Aliyu ina jin daɗi comments ɗinki sosai Thank u_

      ******

A hankali Mom ta sulale ƙasa tana kuka faɗi take.

"Haba Faruok meyasa zaka mana haka bayan duk irin karamcin da muka nuna maka mun soka fiye da yar cikinmu amma yanzu irin sakayyar da zakayi mana kenan? wallahi Faruok i will never forgive u ai wannan zalunci n..."
"Ke!!.

Daddy ya daka mata tsawar da ba ita ba ma har saida dukansu suka tsorata da tsawar.

"Dan Allah dakata Shamsiya shin ko kin manta waye Faruok idan kin manta bari na tuna maki.
Hmm Faruok ɗa ɗaya ne tamkar da dubu Faruok ɗane ɗan halak wanda na tabbata bazai taɓa iya aikata abinda ya rubuta a cikin wannan takardar ba, Faruok na son Fatima son daya nuna bai taɓa yiwa wata ya mace ba zai iya komi a kan ta yayi haka ne kawai dan kada na aikata abinda nace zan aikata a kan ta amma wallahi duk da haka bazan taɓa janye abinda nayi niya ba, aure ne dai kin kashe ko? fine to babu damuwa yanzu na yarda ke ba asalinmu bace dan haka daga yau kowa ya shaida bani da wata ya mai sunan Fatima."

Kuka Fatima ta fasa mai ƙarfi dan jin kalmar da mahaifinta ya faɗa, ƙasa ta faɗi tana faɗin.

"Wallahi Allah Daddy ka yarda da ni duk abinda Ya Faruok ya rubuta shine ainihin abinda ya faru Daddy tunda na aure ya Faruok na cire batin maganar Musaddik a raina na gane yaya Faruok shine *KADDARA TA*, Daddy wallahi duk abinda ka gani a takardar nan shine abinda ya far.."

Bata ida ba Daddy ya ɗauketa da mari ya hau kanta yana duka
Mom faɗi take

"Haba Alhaji kada ka kashe ta mana, wannan sheda ce duk wanda yaga rubutun nan yasan rubutun Faruok ne to meyayi saura bayan ya gama bamu kunya..."
"Dakata Shamsiya ai dama nasan duk iskancin da yarinyar nan take da saka hannunki."
"Wallahi Alhaji b.."
"Shamsiya just keep quite i don't want to hear anything from u Shamsiya ado numa mi yafai bingel doni be ko o wadini am do?"

Muryar shi ce ta fara rawa yayi tagal_tagal zai faɗi da sauri ya rike kansa da hannu ɗaya Mom tayo kansa ya dakatar da ita da niyyar daga mata hannu, kan kujera ya faɗa tamkar ya ɗaura hannu aka.

"Fatima kin cuce ni kinci amanar zumunci Allah Fatima kin nunawa duniya ni ba kowa bane, i promise u Fatima i will never forgive u, for dis mistake no matter how, dan haka ni Bashir Muhammad Lamido daga yau ku sheda bani da wata ya mai suna Fatima babu ita babu ni na cireta daga cikin zuri'ata ki fitar min daga gida i don't want to see ur face again..."

Kuka Mom ta fasa mai ƙarfi tana faɗin.

"Amma Alhaji a andi har jotta Fatima bingel on.. Alhaji kada ka yanke hukunci a fushin zuciya daga baya kayi dana sani."
  "Dana sani? Kike tunanin zanyi dan na rabu da ita never and ever."
  "Amma Alhaji ya kamata ka duba abin nan."
"Dakata Shamsiya babu dole kema ƙofa a buɗe take idan zaki bita fine."

Shiru Mom tayi tana kallonshi dan ta tabbata yau babu wanda ya isa ya hana shi abinda ya furta, a hankali ta juya ta kalli 'yar tata dake tsaye tana aikin kuka.
Suko su Aunty Zee kamarsu zuba ruwa ƙasa susha dan murna tsawa Daddy ya kuma daka mata babu shiri taja akwatinta tana kuka, da gudu Mom ta nufi ɗakinta itama tana kuka kamar yarinya.

****

A hankali take tafiya tana jan akwati har takai bata san wajan da take saka ƙafarta ba, wani irin horn ne ya daki dodon kunnenta da sauri ta tsaya cak tana kallon motar dake mata Horn, a hankali ya buɗe ƙofar motar ya fito sanye yake da kaki a jikinsa sun masa gwanin ƙyau tamkar wani balarabe.
Captain Bilal ne da sauri ya karaso wajenta yana faɗin

"Subhanallahi Fatima what happened to u? ina Mojar Faruok ɗin kike tafiya kina kuka meya faru please tell me."

Shiru tayi tana kallonshi ta kasa magana sai hawaye kawai dake sauka a idonta.

"Fatima magana nake maki kikayi shiru meya faru meya haɗa ki da Faruok ɗin meyasa kike tafe kina kuka ina yake daya barki cikin Wannan halin."

Duk a lokacin ɗaya captain Bilal ya jero mata tambayoyi.
Har wayau bata tankashi ba akwatin hannunta ya amsa ya saka mota sannan ya ɗauko wayarsa ya danna number Faruok saida ta kusan katsewa kafin ya ɗaga cikin fushi captain Bilal ya ce.

"Haba Mojar kai wane irin mutum ne zaka bar yar mutane tana tafiya a titi tana kuka yanzu da wani abu yasameta mezaka cewa iyayenta."
"What kamar ya bayan sai da na kaita har gida kafin na wuto office."
"Kaga yanzu babu wata magana gamu a titin Ibb way kazo muyi magana."

Yana faɗar haka bai tsaya jin amsar Faruok ba ya kashe waya ya juya kallonsa ga Fatima.

"Fatima please kiyi hakuri ki shiga mota ki faɗan duk abinda ke faruwa insha Allahu komi zaizo da sauki, kinji ko?"

Kanta ta kifa a jikin motar tacigaba da kuka, captain Bilal shiru yayi kawai yana binta ba kallo.
Motar Faruok ce tazo dai_dai inda suke tayi parking da sauri ya fito fuskar nan tashi ta koma tamkar ta namijin zaki.
Yana zuwa bai wani tsaya komi ba yaja hannunta ya turata cikin mota Bilal yabi bayansa, bayan yashiga motar Bilal ma ya shiga ya ɗan kwantar da kansa ajikin seat din motar ya wani lumshe idonsa yana tsotsar lips ɗinsa, kamar an tsikaresa Faruok ya buɗe idonsa a take ya ce.

"Meya faru bayan kin shiga ciki baki basu takardar dana baki ba?"

Shiru tayi shima bata tankashi ba, kai ya girgiza ya wani fincikota ta faɗa jikinshi har saida ya lumshe ido.

"Ki faɗa min abinda ke faruwa dan musan mafita."

Dakyar ta iya buɗa baki ta ce.

"Daddy ya koran ya ce babu ni bashi yace sai d..."

Kuka ne yaci ƙarfinta ta kasa ƙarasa magana.

"Faruok wai meke faruwa badai ka sake ta ba?"

Kai Faruok ya ɗagawa Bilal da sauri ya ce.

"What how can dis happen duka_duka yaushe akayi auran da har zaka sake ta?"
"Humm Bilal bazaka gane ba wallahi sanin kanka ne ina son Fatima nima babu yanda zanyi ne."
  "Akwai Faruok yanzu dole ka maida Fatima ɗakin ta shine kawai mafita."
"Hmm Bilal Fatima ta haramta a gare ni Fatima yanzu sai dai tazama matar wani."
“kana nufin saki uku kayi mata?”
 
Kai Faruok ya kuma ɗaga mashi

"What haba Faruok ni a sani na kai ba jahili bane amma taya haka ta faru bayan kasan saki uku a lokaci ɗaya hali ne irin na jahilai.”
"Hmm Bilal na sani nayi haka ne dan Fatima ta samu farin cikin ruhinta zan iya komi saboda soyayyar Fatima."
"Faruok baka da hankali saboda mace zaka sabawa Ubangijin ka haba wannan wace irin soyayya ce?"

Ido Faruok ya lumshe kafin a hankali ya buɗe su kan fuskar Bilal ya ce.

"Look Bilal just forget about what happened, abinda na aikata shine dai_dai damuwata ɗaya yanzu Daddy amma bari na kaita gidan kaka Iya kafin Daddy ya sauko."

Yana rufe baki ya tayar da motarshi da sauri Bilal ya fita ya nufi motarsa kafin ya bisu a baya.

*JIMETA* suka nufa direct suka ɗauki hanyar gidan da zai ɗauke su gidar kakar tasu, tunda suke tafiya Fatima ke kuka bai ce mata a mutu ba har suka isa bakin get ɗin gidan a katafaran harabar gidan yayi parking yana tsayawa Fatima tamkar tana jira su tsaya tasa hannu zata buɗe ƙofar mota da sauki Faruok ya fincikota da ƙarfi yana faɗin.

"Ina zaki? ai kin bari mu tafi tare ko, anya Fatima kinyiwa rayuwarm adalci kuwa?

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now