NADAMAR.. 9

189 12 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

     *NADAMAR DA NAYI*

             _WRITTEN BY_
            *MRS OMAR*

                _STORY BY_
       *HAUWA M. JABO*

            _DEDICATED TO_
           *BEEBAH LUV*

        _K'ORAFI_

_Ina mai ba masoya wannan littafin hakuri akan rashin jina kwana biyu haka ya faru ne saka makon wasu aiyuka da nake amma yanzu zamucigaba daga inda aka tsaya. Love u all my fans_

          _PAGE 9_

"Musaddik maganar aurena da Ya Faruok tana shirin tabbata domin kuwa Dad yau ɗin nan ya nuna min iv ɗin aurenmu nan da sati mai zuw.."
"What? No!! Hubby taya Dad ke shirin mana haka wai Fatima ban dace dake bane?
Humm na tabbata dani mai lafiya ne ina gani kuma mai tarin dukiya ne da tabbas Dad zai baki ni. Amma babu komi akwai lokaci har yanzu."

D'an shiru sukayi na wani lokaci shidai babu abinda yake saurara sai sautin kukanta.
A hankali ta ce.

"Please Musaddik listen to my heart wallahi a duk lokacin dana rufe ido,i always see your face,sonka ya riga ya shiga cikin jikina banda burin da nake fata irin naga na aureka ."

A hankali Musaddik ya sauke ajiyar zuciya dan jin kalaman Fatima masu shiga zuciya.
Saida ya rufe idonshi ya buɗesu a hankali ya kuma sauke wata ajiyar zuciyan kafin ya ce saboda ya tabbata Mama kaka zataji abinda yake cewa.

"OK Hubby please stop crying yanzu ina cikin mutane later zan kiraki musan abinyi.."
"Wallahi Musaddik kaji tsoron Allah.
Anya musaddiq a mari hakkilo bo? Wodi ko a taski kanjum wadi avi mo ado nder himbe ko?"

Tana fara magana Musaddik yayi saurin katsi wayar saboda ya tabbata Mama kaka zata iya faɗin duk abinda ya fito daga bakinta.
Haka Mama kaka tacigaba faɗanta ta gaji Musaddik bai taka mata ba daga karshe ya laluba wayarshi har ya samu sa'ar kunna waƙa haka ya dinga bin wakar tamkar shi yayita.

  °°°°°°•••••••••••••°°°°°°°°°°°°

      *OFFICE*

Zaune yake a office ɗinshi mai ɗauke da sanyin AC kota ina.
Idanunshi a rufe suke yayinda kujerar da yake zaune a kai take juyawa.
Knocking ɗin da akayi ne yasashi saurin buɗe manyan idonshi masu kama da madara. A hankali ya furta

"Yes come in"

Yanda yayi maganar tamkar baya sanyi.
Matashin saurayi ne ya shigo wanda bazai wuce sa'ansa ba fari marar jiki ga hanci babu laifi yana da kyau shima kayan jikinsa kaƙin soja ne da sukayi masa gwanin ƙyau a hankali ya iso gaban Faruok yaja kujera ya zauna suna fuskantar juna Faruok ya yatsina fuska ya ce.

"Sai yanzu kaga damar zuwa?"
"Am sorry major wallahi kasan garin nan yanda yake da cinkoso."

Wata irin harara Faruok yayi mashi da sauri ya kauda kai, murmushi Faruok yayi kafin ya ce.

"Captain Bilal kenan kai dai kullum cikin uziri kake baka taɓa barin a kamaka da laifi. Any way dama i just call u ne kawai dan muyi wata mahimmiyar magana u know bani da wani aboki sama dakai Bilal ina cikin damuwa."

A hankali Faruok ya tsaida kujerar da yake kanta yana fuskantar Captain Bilal sai da sukayi shiru na wasu yan mintina kafin Bilal ya ce

"Friend what is the mater? Please tell me maybe idan wanda zamu iya warwarewa ne a nan musan abinyi tun kafin yayi nisa."

Saida major Faruok ya girgiza kai ya cije lips ɗinshi na ƙasa ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce.

"Bilal my problem a kullum a kan just one girl ne, inama zata fahimci abinda ke zuciyata Bilal har yanzu Fatima taki amincewa dani narasa ina zansa kaina wallahi zuciyata na dab da bugawa."

Zama captain Bilal ya gyara kafin ya kama hannun Major Faruok ya ce.

"Abokina duk wannan matsalar mai sauki ce, mezai hana ka cire Fatima a zuciyarka ka barta ta auri wanda take so."
"Bilal bazan iya ba a kullum idan nayi tunanin haka to wallahi Allah a ranar bazan samu damar yin barci ba. Bilal dole naso Fatima domin irin tarin alherin da iyayenta sukayi min i trust my heart wata rana Fatima zata soni."
"Are u sure?"
"am very sure"
"Humm major kenan har yanzu baka san meye so ba shi so wani abune dayake shiga zuciya a lokaci ɗaya fitar dashi kuwa zayi wahalar gaske shawara ɗaya da zan baka kabar yarinya ta aure wanda take so dan samin kwanciyar hankalinku baki day.."

"No!! Bilal bazan iya ba wallahi koda ban aure Fatima ba bazan taɓa barinta ta aure wannan ɗan iskan yaron ba."
"Why?"
"Au tambayata kake saboda me Anya Bilal kana sona?"

Murmushin takaici Captain Bilal yayi ya ce

"A kullum Major kana bani mamaki sanin kanka ne bani da wani masoyi sama dakai ko kana so na zama butulu ne mai manta alheri?"
  "Au kai baka so ka zama butulu amma ni kake so na zama koka manta wannan auran nawa da Fatima shine kadai abinda zanyi na sakawa wannan bayin Allah?"

Shiru captain Bilal yayi yana tunanin magana abokinshi kafin ya murmusa ya ce.

"Na yarda da maganarka major problem ɗin shine kada ayi auran nan daga baya ayi dana sani."
"Insha Allahu baza ayi ba.
For a moment ta fara wulakanci zanyi hakuri naga na danne zuciyata har ta amince dani."
"Alright Allah ya tabbatar mana da alheri."
"Amin."

Haka suka dinga fira suna jan junansu da wasa har Faruok ya fara mantawa da abinda ke damunshi..

  _3days a go_

Ana yinta fa...

Muje zuwa

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now