NADAMAR.. 16

199 15 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

     *NADAMAR DA NAYI*

             _WRITTEN BY_
            *MRS OMAR*

            _STORY BY_
     *HAUWA M. JABO*

        _DEDICATED TO_
         *BEEBAH LUV*
  

  _Page ɗin yau naki ne ƙawar arziki tun ta yarinta Tabara Muhammad Kabir haƙika komi nada lokaci ubangiji Allah ya baku zaman lafiya dake da mijinki Allah yasa wannan aure an yishi a sa'a Ameen._

                  *******

                 _PAGE 16_

Duk wani abu da ya kamata ayiwa amarya Pendo Ummi tayiwa Fatima, irin abubuwansu na Fulani dadai sauransu ita kanta Fatima takanji sauyi a jikinta takanyi tunanin inama wannan gyara da akayi mata duk na Musaddik ne.
Bayan an gama komi da misalin ƙarfe 8:00pm Dad ya ɗauki ƴarsa da kansa zai kaita har gidanta kuma ya hana ko wace mace binsu uwa uba harda Pendo Ummi ya hana ya ce sai dai su tafi daga baya.
Fatima tanaji tana ganin yau zatayi ban kwana da 'yan uwanta za'a kaita gidan wanda tafi tsana a duniya, tana tafe tana kuka har ta isa mota Dad shida kansa yasa hannu ya buɗe mata sannan ya kamata ya zaunar da ita a kujerar baya, driver ne yazo da sauri Dad ya daga mashi hannu ya ce.

"A'a barshi Suleiman na hutar da kai yau ni zanja da kaina nakai ƴata har ɗakinta sannan na saka mata albarka."

Suleiman yana murmushi ya buɗewa Dad mota yana fad'in.

"Gaskiya ne Alhaji ai dama haka ya kamata duk uban ƙirƙi ya dinga yiwa ya'yansa duk ranar da aka ɗaurawa ƴar aure to ya ɗauketa da kansa ya kaita har ɗakinta yayi mata addu'a domin kuwa matan da za'a tara su kaita wata ko murna maybe batayi da aure balle ta samu damar yiwa ma'auratan addu'a gaskiya wannan halin naka Alhaji ya kamata duk uba na gari yayi koyi da kai, Allah ya tsare Allah yasa wannan aure an yishi a sa'a, in shaa Allahu wannan aure anyi shi kenan har abada."

Tunda Suleiman ya fara magana Dad ya tsaya yana kallonshi cike da jin daɗi kalamansa yayi murmushi ya ce

"Suleiman nagode da wannan adduar taka sannan ina mai yi maka albishir daga yau ka tashi daga driver gidan nan zaka koma kana cikin kashin kanka na baka ƙyautar million biyu da gida kaje kaja jari."
"Alhaji ne? Ko dai mafarki nake?"
"Suleiman ba mafarki kake ba da gaske ne wannan yana ɗaya daga cikin ƙyaututukan dana tana darwa wannan auran ga duk wanda ya taya ni murna cika wannan burin nawa."

Suleiman ƙasa ya faɗi yana mai cigaba dayiwa Abba godiya ita ko Fatima a zuciyarta ciwa tayi.

'Humm Dad kenan ai kam kana dab da asarar dukiyarka danko ni wallahi banga mijin aure ba'

Check Dad ya ɗauko ya rubutawa Suleiman har naira million biyu kamar yanda ya faɗa mashi tare da makullin gida.
Hannun Suleiman na rawa yasa hannu ya amsa yana godiya hawaye na fita a idonsa ya ce.
  "Alhaji nagode Allah ubangiji yasa ka gama da duniya lafiya a kan yanda kake taimakon talakawa insha Allahu wannan auran ainyishi kenan mutuwa ka raba su"
"Allah yasa Suleiman dan Allah sai aje a kama sana'a."
"Insha Allahu Alhaji na gode."
"Haba is ok godiya ta isa haka."

Har Dad ya tayar da mota ya fita Suleiman ya kasa tashi daga inda yake tsugunne.
Dad na cikin mota yana driving a hankali cikin ƙwanciyar hankali yana kallo ƴar tashi ta madubin mota, yana kallon yanda hawaye ke fita a fuskarta.
A haka har suka isa makeken gidanta dayasha ado na kece raini, bayan sun isa mai gadi yayi sauri ya buɗe mashi get ya shiga yayi parking ya fito ya buɗe mata yasa hannu ya kama mata hannu suna tafiya har suka isa bakin wata ƙofa wanda ake danna mata wasu numbers ta buɗe, itama ƙofar tasha ado da irin fentin zamani, a hankali Dad ya furta.

"To Fatima gashi Allah ya kawo ki gidanki kiyi addu'a kafin mushiga kuma ki shiga da kafar dama."
Kai ta ɗaga mashi alamar to tayi kamar yanda ya umarceta, wani katafaran parlour ne suka isa wanda yake ɗauke da kujeru iri daban_daban.
Kai gidan ya haɗu fa iya haɗuwa, saida Dad ya shiga ko ina ya nuna mata duk yanda gidan yake kafin suka dawo parlour suka zauna ya cigaba da yi mata nasiha mai shiga jiki kamar haka.

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now