NADAMAR..15

194 13 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

      *NADAMAR DA NAYI*

  
             _WRITTEN BY_
          *MRS OMAR*

           _STORY BY_
      *HAUWA M. JABO*

          _DEDICATED TO_
            *BEEBAH LUV*

_Masoya wannan littafi ina mai baku hakuri akan  jina shiru kwana biyu, da yauwa wasunku sunsan nayi rashin lafiya to amma yanzu masha Allah naji sauki sosai zaku cigaba da jina insha Allahu._

               _PAGE 15_

*RANA BATA Q'ARYA*

Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya.
A yau juma'a 12 ga watan mayu 2010 aka ɗaura auran Fatima da Faruok akan sadaki mafi saukin gaske dubu hamsin, duk jama'ar garin Yola sun shaida wannan ɗaurin auran gata ne dan tunda Alhaji Bashir Muhammad Lamido ke aurar da yara ba'a taɓa tara jama'ar da aka tara ba, jama'a sun shaida auran 'yan gata ake dan sunci sunsha mai tafiya dashi gida ma ya tafi.
Tunda aka ɗaura auran Fatima hankalinta ya sake tashi ta tabbatar da yau ta zama matar Faruok ko tana so ko bata so, tayi kuka har ta godewa Allah.
Mom Hafsat ce zaune a makeken parlourn ta ita da zuri'ar ta sai maida yanda akai suke ko wace na faɗin albarkacin bakinta aunty Aisha ce ta gyara zama ta fara magana cikin ƙwanciyar hankali da natsuwa ta ce.

"Amma ni Mom a tunanina banga abin damuwa ba, akan Faruok ya auri Fatima ai da Fatima da Hafsat ni a tunanina duk ɗaya ne to meye abin damuwa da abinda Allah ya tsara.."

Wata irin harara Mom ta watsa mata ta ce.

"Da Allah rufe min baki mutuniyar banza wanda bata kishin yan uwanta, wallahi yarinyar nan bansan gidan ubanda ta gadi wannan halin ba?"
"To Mom dama ita taya zata damu tunda tana can gidanta zaune hankalinta ƙwance ta tada kai da naira ta tashi a naira ai mugara ta dinga yi mana bakin ciki."

Cewar aunty Zee kenan murmushi takaici Aunty Aisha tayi kana ta ce.

"Yanzu Zainab nike maku bakin ciki? duk na rasa wa'anda zanma bakin ciki sai ku? ni gaskiya nake faɗa maku saboda ina guje maku ranar NADAMA."
"Wallahi aunty Aisha gara ki dinga faɗa masu gaskiya dan abinda suke basa ƙyautaw..."

Kafin Minal ta rufe baki taji saukar mari a kuncinta Aunty Saratu ta taso tana faɗin.

"Yauwa Zee ƙarawa yar iska gobe ma idan manya na magana ta kuma sako masu wannan dan iskan bakin nata, banza yarinya wa'anda basa kishin mahaifiyarsu ni har akwai ranar da zanso kishiyar uwata shiyasa a kullum nake juya mijina yanda nake so dama kada wata rana yayi tunanin yi min kishiya."

Fuska Aunty Aisha ta ɓata kamar zatayi kuka ta dubi 'yar uwar tata mai maganar ta ce.

"Wallahi Saratu kiji tsoron Allah ki sani wannan duniyar ba a cikinta zamu dawama ba, to meye da kishiyar ai ni a tunanina kishiya yar uwa ce ni kam ko yau baban Teema ya ce zai ƙara aure wallahi hankalina kwance kuma na goya masa baya."
"Da Allah aunty Aisha mun gaji da jin wannan wa'azin nake idan baki bin bayan Mom to zaki iya tashi ki koma ɗakin masoyar taki haba ni ban taɓa ganin matar da bata kishin mahaifiyarta ba sai ke."
  "Naji Jamila zan tashi amma ku zauna da kyau kuyi tunanin maganata dan ina guje maku ranar NADAMA ga wanda aka zalunt.."

Bata ida rufe bakinta ba ta dinga jin saukar mari a fuskarta, daka  kalli fuskar Mom Hafsat zaka tabbatar da ranta ya ɓace sosai, irin yanda ta dinga zabgawa Aunty Aisha mari.
Murmushi aunty Aisha tayi ta goge hawayen da suka taho zasu sauka a fuskarta ta mike tsaye ta ce.

"Mom Allah ya huci zuciyarki wallahi bansan wannan maganar zata ɓata maki rai ba."

Tana rufe baki bata tsaya jin abinda mahaifiyar tata zata faɗa ba da sauran 'yan uwanta kawai ta fita da sauri, tsoki sukayi gabaki ɗayansu Hafsat ta ce.

"Ni wallahi wannan Aunty Aisha haushi take bani sai kace ba Mom ta haifeta ba.
Dakaje gidanta zata cikaka da wa'azin ƙarya."
"Da Allah ƙyaleta munafukar banza ni wallahi ita da wannan ɗayar munakufar tsoran magana nake gabansu."
"Kema kin faɗa Zee ai wallahi ku ƙwantar da hankalinku auran nan bazaije ko ina ba zai mutu muris."

Cewar aunty Saratu da alama Saratu duk tafuso rashin kunya da fitsara.
Bayan fitar Aisha direct ɗakin Mom Fatima ta nufa ɗakin cike yake da jama'a shiyasa tayi baya ta nufi ɗakin Fatima, ƙwance take tana aikinta data saba watau kuka 'yan mata ne biyu kusa da ita da alama ƙawayenta ne amma ɗayar tayi kama da Pendo Ummi sosai.
A hankali Aunty Aisha ta isa wajansu ta ɗaga fuskar Fatima tana kallo murmushi Aunty Aisha ta sauke kafin ta koma kan gado ta zauna yan mata sukayi sauri gaida ita cikin fara'a ta amsa masu.

Hannuwanta duka biyun tasa ta ɗago fuskar Fatima da idanunta sukayi kamar na mujiya sunyi jajir gashi duk sun kunbura kai aunty Aisha ta girgiza ta ce.

"Ya salam Fatima yanzu abin naki har yakai haka gaskiya Fatima bakiyiwa kanki adalci ba kuma bakiyiwa iyayenmu ba, meye a auran Faruok da har kike nuna mashi tsana kai tsaye haba Fatima anya?"
"Hmm Aunty Aisha kenan bazaki taɓa ganewa ba, tunda ke ba auran dole akayi maki ba auran so da kauna kikayi ni kam da za'ayiwa na dole ai dole nayi kuka."

Aunty Aisha zama ta gyara cike da tausayin 'yar uwar tata ta ce.

"Fatima na fahimce yanda kikeji amma hakuri zakiyi kiyi biyayya ga mijinki da kuma iyayenki sai kiga komi ya wuce kamar ba'a yiba nasan yanda so yake amma ki daure zuciyar ki dan samawa iyayenmu farin cikin ruhinsu, Fatima duk mai sonki shawarar da zai iya baki kenan na tabbata idan kika zauna da Faruok lafiya zakiyi sa'ar miji fiye da sauran mata, amma fa idan kin ƙwantar da hankalinki."

Tashi Fatima tayi daga jikin aunty Aisha ta koma ta jingina da kan bed ta lumshe idanunwanta dake ta faman zubar da ruwa ta ce.

"Aunty Aisha ina ta ƙokarin cire son Musaddik a zuciyata amma na kasa ban taɓa tunanin ina mashi irin wannan son ba sai yanzu bansan lokacin da nayi zurfi cikin sonshi ba sai yanzu, aunty Aisha wallahi zuciyata na faɗa min ina shiga gidan yaya Faruok da gawata za'a fit.."

Bata ida ba Aunty Aisha tayi saurin rufe mata baki da hannunta tana fad'in.

"Don't say that Fatima.
Kefa musulma ce kuma ansan musulmi da tawakali kada ki zama mai irin halin Khausar mana a cikin ( son zuciya)"
"Hmm ai Aisha Fatima bazata taɓa jin abinda ake fad'a mata ba, domin soyayya ta riga ta rufe mata ido bata kallon kowa a gabanta sai wanda tasa a zuciyarta."

Murmushi Aisha ta kuma saukewa a duk lokacin da tayi murmushi sai fuskarta ta ƙara haskawa, tana fara'a ta ce.

"Sannu da zuwa Pendo Ummi."
"Yauwa Aisha."
Pendo Ummi itama ta isa dai_dai inda aunty Aisha take ta zauna takai dubanta ga yan matan dake zaune a ɗakin ta ce.

"Kun kafe mutane da ido kuna kallo, amma kun gagara faɗawa ƙawarku gaskiya."

Murmushi mai kamala Pendo Ummi tayi ta ce.

"Mom kema ai kinsan ina faɗawa Fatima gaskiya wallahi duk bayan nabar  ƙasar nan ne komi ya lalace."
"OK to ai Ikram duk mai son Fatima yanzu ya faɗa mata gaskiya idan tayiwa kanta faɗa ita taso, dan haka kizo mahaifinki nason ganinki."

Hannunta Pendo Ummi ta kama tasaka mata hijab suka fita Fatima ta zama abin tausayi a wajan Aunty Aisha tana tausaya mata.
Haka ta kamata har suka isa ɓangaran Dad bayan sun gaisa da Dad ta ajeta tafita abinta.
Dad yayi gyaran murya sannan ya fara magana cikin dattako da manyan taka.

"Alhamdulillahi Fatima yau dai kin zama matar Faruok lakadan ba ajalan ba, na cika wannan alkawarin dana daukarwa kaina Allah ya cika min burina Fatima dan Allah dan sonki  da Annabinmu Fatima ki zauna da mijinki lafiya kiyi masa biyayya kiba mara ɗa kunya Fatima idan kikayi min haka zan zama mai alfahari dake.
Fatima gam Allah a joda jam be gorko ma,to a wadi ninnon a timmini am kodume ,miyidi mi laruma nder seyo kanjum wadi mi hautima be Faruok.
Wallahi Fatima duk ranar da kika kashe auranki da Faruok daga ranar babu ni babu ke dan Faruok ɗan ɗan uwana ne kuma amanata ne, dan haka ba zanso abinda zai cutar dashi ba.
Sannan ga wannan ka ɗan daga cikin ƙyautar da nayi maki kenan Allah ya baku zaman lafiya, ki tashi kije ki ɗauki duk wani abinda ya kamata ki ɗauka idan anjima nida kaina zan kaiki ɗakinki kamar yanda na saba idan yaso duk mai zuwa yaje daga baya tashi kije Allah yayi maki albarka."

Tunda yake magana Fatima ke fitar da ƙwalla zuciya ta na faɗa mata inama zata iya cire son Musaddik a zuciyata da tayiwa iyayenta biyayya...

Kash wallahi naso page ɗin yafi haka amma kuyi hakuri.

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now