NADAMAR.. 17

166 13 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

   *NADAMAR DA NAYI*

         _WRITTEN BY_
        *MRS OMAR*

            _STORY BY_
    *HAUWA M. JABO*

         _DEDICATED TO_
          *BEEBAH LUV*

              *****

_Bana gajiya da baku kyautar page ɗin littafina saboda soyayyar da kuke nunawa wannan buk nawa._
Mrs Uncle Dee
    And
Mrs Lt Col Sani
_Saboda son da kukewa Musaddik nake baku kyautar page_.

  

                _PAGE 17_
                     ****

Wata irin runguma Faruok yayi mata wanda duk dauriyarka sai kaji wani iri, cikin murya kasa_kasa ya furta.
"Hubby na me kike dafa mana? kinji ko yanda girkinki ke kamshi tun daga ɗaki nake jin wannan kamshin mai dad'in shaka,gaskiya nayi sa'ar mata ta ko ina"

Kiss yakai bakinshi zai mata da sauri ta kauda kai taja tsaki ta ce.

"Please ya Faruok tun muna mu biyu ka sake ni bana so."
"What na sakeki,why? Bazan taɓa sakin abinda nake so ba dake zan rayu dake zan mutu danma kada na barki duniya wani namiji ya auran min mata."

Yana magana yana ƙara narke mata a jiki, har wani dan rawa yake a jikinta yana lumshe ido.
Fatima gani tayi da gaske yake yasa ta fara ƙokarin amsar kanta da duk wani ƙarfi nata amma ina.
Murmushi yayi ya wani juyo da ita gabanshi cikin wani irin salo mai wuyar fasarrawa, ya haɗata da kantar kitchen ya jayo irish ɗin dake kusa dasu ya saka a bakinshi ya nufi dashi wajan bakinta tayi sauri ta kauda kanta gefe tana girgiza kai.
  "No Yaya please let me feed my self."
Ina ai ƙara matseta yayi da hannu ɗaya, ɗayan kuma ya juyo da fuskarta ya buɗe mata baki da ƙarfi ya saka mata irish ɗin dake bakinshi cikin salo iri_iri.
Humm haka ya dinga yi yana ɗaukowa ya saka a bakinshi kafin ya bata har saida yaga idanunwanta sunyi ja kafin ya ɗauketa cak bai  sauketa ko ina ba sai parlournsu kuka tacigaba dayi tana bashi hakuri, amma kamar tana ƙara zugashi, wani irin salo ya dinga jifarta dashi mai shiga jikin mai karatu dan kuwa Fatima komi bataji hahaha.
Hannu tasa tana dukan kirjinshi duk dan ya sake ta amma ya kiya da alama ma dadin dukan nata yakeji knoking ɗin da akayi ne ya dawo dashi daga duniyar daya lula ya fara ƙokarin dai_daita kansa saida ya tabbatar da ya nitsu kafin ya dauko wani remote ya danna a take ƙofar ta buɗe amma hannunshi na rike dana Fatima dan yasan daya saketa guduwa zatayi.
Aunty Zee ce da Hafsat suka shigo sai wani dage hanci suke suna bin ko ina da kallo, Faruok na ganinsu ya ƙara shiga jikin Fatima ya narke.
Da murmushi  Aunty Zee ta iso wajansu tana faɗin.

"Amarya da ango Amarya bakya laifi koda kin kashe ɗan masu gida, kinga irin ƙyan da kikayi kuwa rana ɗaya."

Ta wani juya ta ƙara karewa gidan kallo Faruok duk yana kallonsu ya wani haɗe girar sama data ƙasa wani irin shu'umin murmushi Aunty Zee tayi tazo dai_dai inda suke zaune ta dan wani dafa kan kujerar cikin wani irin salo ta ce.

"Wow Bros kayi fa sa'ar gida, kai Faruok this beautiful house looks like  its in London, I only saw beautiful houses like this in London,you are really Lucky with Dad gaskiya kai fa dan gata ne."

"Yes Aunty Zee dis is a   beautiful house.sai dai matar dake cikinshi ne dai kawai batayi marching da gidan ba."cewar hapsat.
 
Murmushi takaici Faruok yayi ya wani yamutsa fuska kamar irin yaga kashi mai wari ya ce.
"Hmm are u sure gidan nan bai dace da matar da ake so ba? to Hafsat wace macece ta dace da gidan nan?"
"Hmmm yaya Faruok kenan ai ko ba'a faɗa maka ba kasan mace mai class ya kamata a kawo gidan nan , someone like me."

Wata irin muguwar dariya Faruok ya ƙwashe da ita harda tafa hannu kafin lokaci ɗaya kuma ya haɗe fuska kamar bai taɓa dariya a duniya ba. Duk abin nan Fatima na takure waje guda dan ya hanata tashi kanta a ƙasa
Sai daya ƙira sunanta kafin ya cigaba da magana cikin zafi rai.

"Hafsat. Humm yanzu dan Allah ko kunya bakiji ba? Ke in har ana maganar mace mai class har zaki iya saka baki har wani class ne dake, ai duk macen data nuna tana son namiji bashi ya nuna yana sonta ba to batada wata sauran darajar sauran mata dan kuwa wallahi Hafsat kulu mai aikin gidanku tafiki daraja a idona. Fatima kuma da kike faɗin bata dace da gidan nan ba kece kike ganin bata dace ba, hmm Fatima macece da Ko wane namiji yake fatar tazama uwar ya'yansa amma Hafsat duk namijin da kikaga ya zabeki  to wawane baisan darajar kansa ba, i love Fatima very much zan iya yin komi saboda ita so dan haka be carefull in ba haka ba hmm i promise u will.."
"No bros its ok ba munzo bane dan wani magana munzo ne kawai taya ku murna kasan halin hafsa so ka daina kulata."

Cewar aunty Zee ita ko Hafsat tunda ya fara magana take kallonsa sai kawai hawaye daya fara sauka a idonta na takaicin kalaman da yake faɗa mata masu zafi.
Juyawa yayi ya wani irin yiwa Aunty Zee dirty look da sauri ta ɗauke kanta daga nashi cikin isa ta ce.
"Why did u look at me like dat? Haba bros kasani fa ni yanzu komi ya wuce a wajena na yarda *MATAR MUTUM* kabarinsa so dan haka forget about everything that happened."
"Zee.. Kenan i know u. Zee can never change."

Yana magana ne yana wasa da hannun Fatima wani irin daɗi yakeji irin yanda yake wasa da hannun nata dan har wani lumshe ido yake.
Aunty Zee zata sake magana Hafsat ta daga mata hannu cikin muryar kuka ta fara magana.

"Please ya isa Aunty dama akwai ranar da zaki taya Makiyiyata murna bayan kinsan abinda nake so ta aura yanzu Aunty gabana kike faɗin haka?"
"No sis please listen to me, ya kamata ki sani shi aure nufin ubangiji ne dama can Allah ya rubuta Fatima matar Faruok ce dan haka kiyi hakuri Allah ya baki wani wanda yafish.."
"Ya isa dan Allah aunty kinci amanata nagode."

Tana rufe baki ta juya da gudu tana kuka aunty sai kiranta take amma kota juyo.
Murmushi tayi ta juya ta kalli Faruok da Fatima ta ce.
"Bro dan Allah kuyi hakuri da halin Hafsat kasan yanda so yake mutum zai iya yin komi akan abinda yake so ba kamar idan soyayyar farko ce."

Da sauri Fatima ta ɗaga kai ta kalli Aunty Zee ido ɗaya ta kashe mata.
A take Fatima taji wani irin zafi a zuciyarta na rabuwa da abin kaunarta, kafin ace me har hawayen da take ɓoyiwa sun bai yana a fuskarta sun sauka kan hannun Faruok, cikin rawar jiki ya juya yana tambayarta, sai can ya tuna da maganar da Aunty Zee tayi da sauri ya furta.

"Zee please ki fita bana son ganinku dan nasan ganinku ba alkhairi bane."
"Haba bros ya zakace hak.."
"Zee nace ki fita."

Yanda yayi maganar ne cikin tsawa ga yana yinshi ya sauya yasa aunty Zee tasha jinin jikita kafin ya dawo ta kan Fatima har tabar wajan da gudu ta nufi ɗakinta mutuwar zaune yayi ya tsaya yana kallon yanda take gudun duk wani sura ta jikinta juyawa take..

Kash mudaije zuwa
I love u fans

NADAMAR DA NAYIजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें