NADAMAR.. 10

188 14 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

     *NADAMAR DA NAYI*

        
             _WRITTEN BY_
            *MRS OMAR*

              _STORY BY_
        *HAUWA M. JABO*

         _DEDICATED TO_
       *BEEBAH LUV*

_Page ɗin yau naku ne ƙawayen kirki aminan arziki wa'anda kuke tsaye kaina akan duk makiyana
SAMIRA UNCLE DEE
MAMAN DADDY
NANUS OGA ABU
MRS SANI OFFICER'S QUARTERS
MAMAN KHAIRAT
kuna bani gudun muwa sosai a kan wannan littafin nawa
THANK U VERY MUCH

           _PAGE 10_

          ******

Yau saura kwana hudu bikin Major Faruok da Fatima Lamido duk wani abu da ake na wajan 6angaren ango da Amarya Dad ya gama komi hatta kayan lefe ya tura kuɗi Dubai aka haɗa komi hatta kayan ɗaki. Yayinda cikin manya_manyan gidajenshi yaba Faruok ƙyautar ɗaya duk da Faruok mahaifinshi ya bar mashi tarin dukiya amma baya komi da ita sai juya mai da Dad yasa anayi.
Gidan da Dad ya bashi a wata unguwa mai suna mafias quarter's gidan ya haɗu iya haɗuwa dan unguwar sai wane da wane.
Dad duk wani abu da zaiyi dan yashawo kan Fatima yayi amma abin yaci tura dan har ƙyautar sabuwar mota ya bata ƙirar Range Rover da ƙyautar kuɗi har two million duk dan tayi hidimar daya kamata.
Hmm amma abin haushin  Fatima bata canza ra'ayi ba.
Rabon da Faruok yasa Fatima a idonshi tun ranar data suma wani irin wasan 'yar 6uwa suke dashi bataso ta ganshi shi kuma yau yayi alkawarin saiya sakata a ido.

Misalin 5:pm na yamma ya shigo gidan babu inda ya nufa direct sai ɗakin Fatima knocking yayi amma bata amsa ba ya tabbatar da tana cikin ɗakin yasa a hankali ya murɗa ƙofar ɗakin ta buɗe zaune take a bakin gado tana wasa da wayarta,
Tana ɗaga kai sukayi ido biyu dashi ta kuma sauya fuska.

Why,why,why?I hate this guy in my life,I hate to see him at all.why is he following me all around? I feel like killing myself because of him.

Duk a tunanin ta a cikin zuciyarta tayi maganar saida taga yana murmushi yana fad'in.

"Why fatima,I just love you,why are thinking of killing yourself because of me?why?just because I said I love you?so ni maye ne, thank God ni mayenki ne kuma duk sonki ne ya jamin zaki iya kirana da duk sunan da kike so wannan ba damuwata ba ne.
But don't forget mun kusan zama inuwa ɗay.."

Da sauri tun kafin ya ida magana ta ce.

"Never"
"Why"

Wata irin harara Fatima ta watsa mashi mai firgitarwa da manyan idanunta, a hankali Faruok ya lumshe ido ya sauke ajiyar zuciya ya dafe hannunshi ɗaya a zuciyarshi ya ce.

"Oh my God sweetheart a kullum idan kina min irin wannan kallon nakanji bansan duniyar da nake ba. Please dear look at me again, i like the way you look at me."

Murmushi takaici Fatima tayi take idonunta suka chanja colour  zuwa red ta fara magana cikin gadara.

"Love love!! every day u just talk about loving me, u don't even know anything about love.
Ya Faruok kenan kasani shi so tamkar hadarin damina ne a duk lokacin daya taso to tabbas sai ruwan sama ya sauka idanko har kaga bai sauka ba tau tabbas bakan gizo ne ya gitta.
Hmm Ya Faruok ya kake so ka zama mai irin halinshi ko kana so ka raba soyayyar da aka share lokaci ana ginata ta hanya mai ƙyau.
To wallahi Ya Faruok koda ban aure Musaddik ba maza sun kare a duniya bazan taɓa maka kallon mijina ba."

Wani abu Faruok yaji ya sokai a zuciya  mai kama da kibiya.
Da sauri ya dafe zuciyarshi ya ce.

"Fatima kina tunanin har zan iya hakura da sonki?"

  Baki ta taɓe ta ce

"That's ur problem  its not mine".
"Alright na fahimceki Fatima no problem duk kiyi abinda kikaga dama one day zan rama."

Tsoki Fatima taja kamar zata cire halshenta ta wurga mashi pillown kusa da ita tayi hanyar waje da sauri.
A hankali Faruok ya lumshe ido ya ce.

"Yea that's good."

A parlour ya sameta zaune ta ɗan tada kai da hannun kujera ta takure babu kowa a parlour sai sautin ƙarar TV. Murmushi yayi ya wuceta dan yasan idan ya tsaya zata koma faɗa mashi duk wata magana data fito bakinta..

★★★★★★★

Ƙwance take kan gadon da yake ɗauke da lafiyayar shinfiɗa mai ƙyaun gaske daga ita shi wasu matsatson kaya da duk wani surar jikinta kana kallonta a waje sai juyi take a kai a hankali ya turo ƙofa sanye yake da jallabiya daka ganshi kasan daga masallaci ya fito.
Cak ya tsaya dan ganin Hafsat ƙwance a kan gadonshi ga shigar da take jikinta take yaji wani sabon lamarin abu ya shiga zuciyarshi...

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now