NADAMAR DA NAYI page 6

234 18 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*
  

       *NADAMAR DA NAYI*

        
             WRITTEN BY
           *MRS OMAR*

              STORY BY
        *HAUWA M JABO*

           DEDICATED TO
             *BEEBAH LUV*

               _Page 6_

_*Tofa!! itafa rayuwar nan sauki ne da ita wanda yace yanayi dakai to dole kayi dashi saboda duk wanda ya ce maka yana sonka tabbas ya gama maka komi hak'ika yan kebbi amana tane dan sunada karamci dole ku zamo masu rukon amana domin Jidda Aliyu ta fito daga wajanku hak'ika wannan page na sadaukar muku dashi*_

       •••••
    >>>>...>>>>.>.>>>....>>>>

Mota ce ta danno kai ba tsayawa motar ta haɗu ƙirar ( Land cruiser) wanda ta amsa sunanta mota black ce ga tinted tasha baƙi, baka iya ganin mutumin dake ciki. Direct wajan da ake parking motoci mai tuƙata ya nufa cikin sauri wanda ke mazaunin driver ya fito ya nufi bayan motar da alama zai buɗewa mamallakin motar ne, ba wani ɓata lokaci ya buɗe marfin motar saida ta fara duro da kafarta ƙasa kafin ta ida fitowa da gangar jikinta sanye take da black gown anyi mata aiki da white stone fuskarta sanye take da eye glass shekarunta zasu kai 35 zuwa da 38 tayi kyau babu laifi. Tana ganin Fatima da Faruok ta wani haɗa fuska kamar an aiko mata da sakon mutuwa, cikin isa ta isa wajansu tana wata yatsina kamar irin taga kashi. Saida ta kalli Faruok sama da ƙasa kafin ta ce.

"Munafukan banza wallahi andai ji kunya."

Wani irin kallo Faruok yayi mata sannan ya danyi murmushi wanda daka ganshi kasan na takaici ne, hannu ya mikawa Fatima ba musu ta mika mashi nata cikin isa ta mike tsaye tana kallon matar dake magana.
Matar wata irin dariya ta saki ta ce.

"Gaskiya Faruok kunfa burgeni dan wannan salon naku a film kawai ake yinsa..."

Saida ta ɗan tako dai_dai inda suke ta ɗaure fuska kamar bata taɓa dariya ba ta ce.

"Amma kada ka manta Fatima ina gaba da ita a gidan nan,wanda suka fita shekaru ba'a aurar dasu ba balle ita idan kanason matar aure zaka iya auran koda Hafsat ce amma banda Fatima."

Faruok saida ya cije lip ɗinshi na ƙasa ya dubi Fatima yaga idonta na kansa sannan ya fara magana kamar irin yana kunyar magana.

"Humm Fatima mace tamkar da dubu tarbiya ilimi asili NAGARTA dadai sauransu,shiyasa duk namijin da yarasa Fatima dole yayi babbar asara."

Fuskarta ya ɗago yana kallon cikin idonta dukda Fatima idan yayi magana tanajin zafi amma taji daɗin maganarshi cikin irin salonshi yaci gaba da magana.

"Aunty zee kenan bazaki taba fahimtar meye soba har sai kin samu wanda ya nuna makishi sannan zaki fahimta. Hmm wait for a moment, let me remind u that fatima will soon be my wife  . Nakanyi murna because Fatima is my life, koba haka ba babyna?"

Murmushi ƙarfin hali Fatima tayi dan kawai kada aunty zee ta gane abinda ke zuciyarta. Ido Faruok ya lumshe a hankali ya furta.

"Oh my God baby This smile is killing me."

Wani irin haushi ne ya sake shiga zuciyar Aunty zee cikin fushi ta finciko Fatima ta ɗaga hannu zata wanka mata mari Faruok ya rike hannunta yana huci."

" How there you touch my wife's face?if this action repeat itself again you will regret being my sister."

"Wow Faruok that's great. Because of this dirty girl har zaka iya buɗa baki ka faɗa min magana.. Ni Zee Bashir Lamido. Gaskiya ne."

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now