NI MA MATARSA CE

By habibaimam1986

3.5K 284 7

labari me cike da darasi, kudi ba Shi ba ne komai Wanda Kuma kake ganin Bai isa ba sai kaga ya isa, labarin y... More

NI MA MATARSA CE FREE PAGE 1
NI MA MATARSA CE PAGE 2
NI MA MATARSA CE PAGE 3
NI MA MATARSA CE PAGE 4
CONTINUE PAGE 5
PAGE 6
continuation page 6
page 7
continuation page 7
page 8
page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
page 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
page 35
page 36
page 37
page 38
NI MA MATARSA CE PAGE 39
PAGE 40
NI MA MATARSA CE PAGE 41

NI MA MATARSA CE, PAGE 5

83 9 0
By habibaimam1986

Hakkin mallakar YAR GIDAN IMAM ne.
          FREE PAGE 5

             ********************
       Haj madina ta dubi Haj murjanatu cikin fuskar da babu yabo babu fallasa, tace " Gaskiya Haj abinda kukayi bai kamata ba wannan ba dai dai bane,ta yaya zaku kushe mutane agabansu, ina ma laifin Ku bari su tafi sai Ku Fadi duk abinda kuka ga damar fada, wannan gaskiya cin fuska ne, bayanni banga aibun wadannan kayan ba tsakani da Allah iya kokari sunyi".
   Haj murjanatu tayi mata wani irin kallo sannan tace "Ai da yake duk kanwar ja ce shiyasa zakice bakiga aibun kayan ba, duk kanana ne babu wata babbar atamfa ko leshi ko shadda aciki, Kuma idan ban gaya musu agabansu cewa kayan ba suyi ba wa kike son na gaya ma,sun Dade basu ce anci musu mutunci ba"

   Haj Nana ta kebe baki tace, " To ta yaya zaa yabi abinda Bai Kai ayaba ba, wannan Kaya dai an cika akwati ne Amma babu kayan arziki aciki, Kuma akalla ya kamata kasan inda kake neman aure, wannan kayan idan wani waje aka Kai godiya za'ayi tayi ana fadin bajintarsu saboda an kaisu inda ya dace dasu, Amma idan Ka Kai wani wajen na rantse da Allah tir za'ayi da Allah wadai saboda ka kaisu inda Bai dace dasu ba,don haka ni banga aibun fadin gsskiyar cewa basuyi ba".
  Haj Binta ta gyara zamanta tana kallon kayan a wulakance tace " Kayafa ba suyi ba, don Allah dubi wancan leshin na rantse Shi na Saima Mai aikina shekaranjiya dubu goma sha biyar don kuma wulakanci ace irinsa za'asa a lefan mujaheeda...."
   Wane leshin ne kika Saima me aikinki,? Cewar mujaheeda wacce dawowarta kenan gidan tana rike da jakunkunan sayayyar da tayi na tarkacen kayan  ciye ciye.Haj madina ta juya ta gyara zaman hijabinta ajikinta tace Allah ya bamu alheri.haj murjanatu ta zuba mata harara tace " Amin sauka lafiya" kafin ma ta Karasa magana har takai bakin kofa.
  Haj murjanatu ta tashi ta ruko hannun mujaheeda wacce take aikin kallon akwatina da Kayan dake ciki, tace " Kada wani abu yadameki, kayan lefe na banza Taufiq yayi Miki Amma Kada ki damu kema kinsan Kona arziki ya kawo ba zaki sa ba don kayanki da zakisa da bikinki sun riga sun kammala", mujaheeda ta zauna asanyaye ayayinda Haj Binta tace " Allah ya riga ya rufa Miki asiri ba don haka ba da bakinciki ya kasheki don babu abu mafi zafi daya wuce ace anyima budurwa banzan lefe,
Don babu dadi Amma ta yaya yasan gidan da kika fito amma zai kawo Miki irin wannan lefen".
  Mujaheeda dai tayi shuru tana Jin maganganun da suke yi itama Haj Nana tana Kara fadan nata hasashen
Tsam mujaheeda ta tashi ranta abace ta haye sama ba tare data duba kayan ba ko ta tamkama duk maganganun da suke yi ba.
  
Ganin hakan yasa su Haj Binta sukayi sallama da Haj murjanatu suka tafi. Ayayinda Haj murjanatu ta Kira hadiman gidan ta basu umarnin su kwashe kayan su Kai dakin  baki su aje acan.
Sannan ta tashi tabi bayan yarta .
Kwance ta sameta asaman gado ta zubama saman dakin Ido, ta Sami kusa da ita ta zauna gami da Kiran sunanta ,ta juyo ta dubeta sosai fuska ba walwala sannan ta Watso Mata tambayar " mummy me yasa kike son ki dinga muzanta Taufiq".
  Tambayar tazo Mata a shammace ,ta dubeta sosai tace " KO kadan bani da tunanin muzanta Taufiq, illa ke da nake kokarin Karema mutunci", ta tashi ta zauna sosai tana kallonta tace " kare mutuncina mummy Yana nufin ki sama min mutunci awajen Taufiq ne.amma abinda kike aikatawa baiyi Kama da kare min mutunci ba,ina yarda da abubuwan da kike yine saboda ina tunanin kamar Donni kike yi don Samun fsrincikina,to Amma yanzu wannan abinda kikayi na hanyar muzanta Taufiq gaban kawayenki Yana min nuni da cewa martabarki da girmanki kawai kike son karewa"
Haj murjanatu tayi saurin girgiza Kai tace " Aah mujaheeda saboda ke nakeyi" ta girgiza Kai tace " idan Donni kike yi saiki mutunta kayan lefena gaban kawayenki ki yabesu Wanda KO da ga  baya kinzo kin Fadi aibunsa agabana bazan damu ba ,kamar yadda baxanga laifinki ba, Amma baa gabansu ki biyesu kuna aibata kayan ba harda cewa me aikinta ta sayama irin leshin cikin lefena, shin mummy da Taufiq zaiji ko zaiga abinda abinda kukayi akan lefensa kina tsammanin yaya zaiji?".
 
Haj murjanatu ta jinjina Kai tace " ban dauka hakan zai bata ranki ba Amma bazan Kara yin maganar lefen ba,ba Kuma Zan fito dasu kowa ya gani ba"
  Ta dubeta sosai tace " bazaki bari kowa ya gani ba saboda kina Jin kunyar nuna kayan amatsayin lefen yarki Ko mene?"
  Haj murjanatu ta dan hadiye yawu sannan tace " eh kusan haka ne" .A hankali mujaheeda ta koma ta kwanta gami da juyama Haj murjanatu baya ranta na cigaba da kuna hakan yasa duk bayanan da Haj murjanatu ta cigaba dayi Mata bayanin dalilinta nayin abinda tayi Ko zata fahimta Amma tunda ta kwanta ta juya baya bata Kara ko da kwakkwaran motsi ba balle tasa ran zata tanka Mata harta gaji da magana ta tashi ta fice.

              ************
  Iya harzuka Haj Bilkisu ta harzuka don harta Gama labartama mahaifiyarsa da Taufiq labarin abinda ya faru zuciyarta bata lafa daga haushi da Jin zafin maganganun dasu Haj murjanatu suka yi musu ba
   Haj laraba tace " shifa aure ya gaji haka gutsiri tsomarsa yayi yawa babu wani aure da zaayi Shi Salin slin ace babu wata matsala da aka samu,saboda haka hakuri shine Kan gaba wannan ba wani abu bane " Haulat
Ta girgiza Kai tace " gaskiya goggo wannan wani abu ne don gaba daya yaya baiyi sa'ar suruka ba Ai ana barin halal don kunya meyasa ba zatayi hakurin mu tafi ba kafin suyi wulakancin da suka yi niyya ammafa agabanmu suke kushe kayan da muka Kai duk irin kokarin da yaya yayi basu gani ba "

Continue Reading

You'll Also Like

75.7K 3.4K 79
❤️
42.5K 897 91
Continuation of Modesto story who happens to intercourse with friends,mature,classmates,strangers and even family...
36.8K 998 82
In which Kim Saena is in a groupchat with a bunch of idiots Or In which Bangchan finds himself inside a groupchat with a bunch of delusional fans ~~★...
172K 357 21
just some of my horny thoughts;) men dni