page 36

59 6 0
                                    

NIMA MATARSA CE
         NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM
  ( YAR GIDAN IMAM )
BABI NA TALATIN DA SHIDA
           ************
   Malllam Umar ya Matso Yana kallon yadda muhseena duk ta fita hayyacinta, yace " kin bata magani" ta amsa " eh na bàta amma dai har yanzu bai lafa Mata ba ko ido daker take budewa.
    Ya durkusa agaban ta Yana cewa " sannu, don Allah ki sassauta ma kanki damuwa, Kada kizo ki fada wani halin daban". Hajara tace cike da damuwa ' abinda nake ta faman gaya Mata Kenan, duk bawa baya kaucema kaddarar sa Kuma rayuwa cike take da kalubale dole mutum ya koyi juriya da jarumta".
   Muhseena ta waiwayo ahankali idonta cike taf da hawaye tace " yanzu Inna ni har akwai wata juriya da jarumta Wanda ban nuna ba arayuwata, duk tsawon wannan lokacin na yarda da kaddarata amma kaddara daya ce na kasa dauka domin nayi Imani bata cikin Jerin kaddarorina hakanne ma yasa na kasa yarda da ita". Mallam Umar yace " wace iri kaddara ce " tace " kaddara kin gaya min ainihin gaskiyar lamarin" . Gaba dayansu suka dubi juna gami da numfasawa sannan mallam Umar yace ' muhseena ki kwantar da hankalinki na gaya Miki nayi miki alkawarin innarki zata gaya Miki komai".
    Bata  yi magana ba ya cigaba da cewa " sai dai ko kadan Bana son ki zargi mahaifiyarki ko ki dasama kanki tsanarta ko ki kasa yarda da abinda ta gaya Miki, domin tana da gaskiya babu karya acikin maganganunta".
    Muhseena ta numfasa gami da Kara rufe idanunta tace "Bani da hujjar kalubalentar mahaifiyata akan ko me ta aikata, kawai ni burina shine na sanin ko wacece ni". Hajara ta goge dan guntun hawayenta tace "Zan gaya Miki , Allah dai ya baki lafiya". Bata Kara cewa uffan ba adalilin sarawar da kanta yake yi kamar zai Fado kasa, tunda take bata taba yin irin wannan ciwon ba.
    Kabir kuwa Yana can ya kara fadawa cikin mawuyacin yanayi, guiwa biyu ya je ya zube ma mahaifinsa Yana rokon ya amince masa ya auri muhseena. Mallam Hamza yayi masa kallon tsaf yace " Kabir me yasa Ka dage dole saika auri muhseena" yayi sanyi da murya yace " saboda tana da mutunci kima da daraja , tunda nake ban taba ganin mace irin ta ba me matukar kamun Kai da rike talauci ba tare da kauce hanya ko gurbata tarbiyyar ba, sannan saboda ina matukar Sonta Baba tunda nake ban taba son wata ya ba sai ita, "
  Mallam Hamza ya gyara zamansa akan buzunsa  yace "yanzu kana tsammanin akan farincikinka mu za muyi wasa da mutuncin mu da kimarmu ( ya girgiza Kai) aah bazai yuwu ba don haka Ka daina wahalar da kanka ko daurama kanka damuwa ta banza domin yin hakan bazai iya canja komai ba".

    Kabir ya dago da jajayen idanunsa ya dubi mahaifinsa yace " shikenan Baba Zan rabu da ita ,Amma har abada bazan taba son wata irin yadda nake son muhseena ba Kuma har na mutu bazan fita daga cikin kuncin bakincikin ràshin ta ba ".

  Malllam Hamza yace " duk abinda kaji mutum yace bazai iya ba to baisa Kansa bane don haka zaka iya cireta aranka matukar Ka so hakan, maganar Kuma ba zaka taba son wata kamarta ba wannan maganar banza ce lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan".

  Daganan mallam Hamza ya tashi ya fice ya barshi a tsugune cikin matukar damuwa mara musaltuwa. Hafsatu ta karaso kusa da Shi tana kallonsa zuciyarta na matukar kwadaita Mata ta ji tausayinsa amma bata son ta nuna masa ta Kira sunansa " Kabir" ya dago Kai ya dubeta .

   Zuciyarta ta sare tausayinsa ya Kara kama ta tace " don Allah kayi hakuri Ka sama kanka juriya da dangana Ka sadaukar da soyayyar Ka saboda farincikin mu, da Kuma Samun zuria ta gari daga gareka,ina son Ka sani aurenka da muhseena babu abinda zai janyo mana sai kaskanci don haka matukar kana son kwanciyar hankalin mu to ya Zama dole Ka rabu da ita".

  Kabir ya girgiza Kai gami da numfasawa ji yake alokacin duk duniya da wuya asamu Wanda ya Kai Shi shiga damuwa da tashin hankali. Ya ce" shikenan babu komai Allah yasa hakan shine yafi Zama alheri agareni da ita kanta muhseena, Amma.....?" Hafsatu tayi saurin dakatar dashi tace " Kada Ka Kara komai akan wannan mubar maganar,".

  Ido kawai ya bita da Shi ya kasa magana harta wuce.ya Mike ahankali ya shige dakinsa ya fada Kan gado gaba daya zaman garin ya ishe shi kamar Yana Kan wuta haka yake ji kwata kwata baya Jin zai iya Kara ko da kwana daya agarin.

NI MA MATARSA CE Where stories live. Discover now