page 26

62 6 0
                                    

NIMA MATARSA CE
                    NA
  HÀBIBA ABUBAKAR IMAM
   ( YAR GIDAN IMAM )
BABI NA ASHIRIN DA SHIDA
             ************
  Hafsatu ta aje gauruwar ajiyar zuciya sannan ta lalubi kujera ta koma ta zauna tana cigaba da kallonsa, cikin shakewar murya tace " Na dai gaya maka ba zaka iya aurenta ba saboda ba zamu yarda da ita a matsayin surukar mu ba, Kada ma Ka bari ko da wasa mallam yaji shi da yafi kowa burin Ka auro ya agidan dattako".
    Cikin matsananciyar damuwa Kabir yace " mana idan ko dattako ake nema ina ganin idan aka Sami gidan Mallam Umar to an wuce wajen, haka zalika idan natsuwa da cancanta ake nema shima idan aka Sami muhseena an je matakin karshe". Ta girgiza kai tace " hmmm babu abinda Ka sani a wañnan  bangaren sai abinda idonka ya gani kawai Wanda Kuma yaudara ce kawai, babu wani dattako awannan gidan kamar yadda babu wani kamun Kai da nutsuwa da zaa samu awajen wannan yarinyar ".
    Kan Kabir yayi nauyi zuciyarsa ta shiga tafasa Sam Sam bai son yadda ake aibata muhseena, ya Kara kallonta cikin Jan Ido yace " aah mama babu yaudara acikin Kamala da nutsuwar muhseena na yarda da dabi'un ta sune Kuma suka ingizani wajen kaunarta adalilin hakan har na Fara sha'awar yin aure" Hafsatu ta shiga girgiza Kai tana cewa " kabar wannan maganar domin kuwa abinda kake so ba zai taba yuwuwa ba, don haka kayi gaggawar cire wannan maganar aranka, kaje Ka Samo wata yar gidan mutunci gasu nan da yawa".
     Ya runtse Ido ya bude Jin abin yake tamkar Yana mafarki domin bai taba tsammanin zai Sami matsala da iyayensa wajen auren muhseena ba.
     Ya gyada Kai yace cikin murya Mai cike da ban tausayi " na rantse Miki ina son muhseena so na hakika bansan yadda zanyi da Kaina ba matukar na rasata domin rashinta tamkar Rasa wani bangare ne na jikina".
     Hafsatu ta saki salati da karfi tana tafa hannayenta " ni ko na shiga uku yaushe kayi zurfi a soyayyar yarinyar nan haka bayan ba zaka taba samunta ba domin dai matukar mune zamu fada aji to Baka Isa Ka auri wannan yarinyar ba".
   Cikin kaguwa Kabir yace " wai mama Mai tayi da baza'a iya aurenta ba , meye laifinta?". Tayi masa kallon tsaf tace " bata da wani laifi , laifin mahaifiyarta shine ya shafeta" Kabir yace " Aiko Allah baya kama bawa da laifin wani bawa face abinda bawan ya aikata da Kansa don haka babu dalilin da zaa hukunta muhseena da laifin mahaifiyarta" ya daga hannayensa biyu alamar roko yace" don haka don Allah mama na rokeki ki Goya min baya na auri muhseena". Ta girgiza Kai tace ," bazan iya Goya maka baya baya Ka aureta ba domin Ka godema Allah da ya kasance ni Ka Fara gayama wannan maganar ba mahaifinka ba domin da kasha mamaki".
   Kabir yayi ajiyar zuciya yace " don Allah mama Mai mahaifiyar muhseena tayi da har zaiyi sanadiyyar da zaa hanani auren muhseena".
     Hafsatu tace " nace kabar wannan maganar, kadai sa aranka babu aure tsakaninka da ita har abada".Kabir ya dafe Kansa da hannu biyu Yana fitar da wata boyayyiyar ajiyar zuciya baya Jin tunda yazo duniya ya taba riskar Kansa cikin tsananin tashin hankali da damuwa irin na yau , daker ya iya yunkurawa ya tashi Yana gauraye hanya ya fita daga dakin ba tare da ya Kara cewa komai ba . Hafsatu ta bi bayansa da kallo cike da tashin hankali bata taba tsammanin zata taba Jin wannan maganar daga bakin danta Wanda ta dora dukkan fata akansa, burinta da yawa ya cika ta hanyar dan'uwanta Alh Musa Wanda ya daukar Mata Kabir ya inganta rayuwarsa ta hanyar bashi ilimi da tarbiyya da Uwa uba aikin yi Wanda yaja ya Sami arziki shima tunda ya wuce da bukatun Shi da nasu duk abinda take so da ga ita har mahaifinsa mallam Hamza wanzami to fa zaiyi musu, to ta yaya bayan danta nagartacce ne zasu bari ya auri yar da bata da asali, ai idan ma sukayi haka lalle sun ci amanar dansu. Ta zuba tagumi tana addu'ar Allah Kada yasa wannan lamarin ya Zama damuwa a tare dasu.

       Shigar Kabir dakinsa ya fada Kan gado ya kwanta rigingine gami da runtse idanunsa , hakanan yaji wasu siraaran hawaye suna fita daga idonsa.zarihi bazai iya rabuwa da muhseena ba Amma, zaiyi yaki har sai ya aureta , domin idan yace bazai aureta ba bai San inda muhseena zatasa kanta ba Kuma zafi da radadin da yake ji ayanzu baya son ko kadan muhseena ta ji irinsa domin Shi kadai yasan abinda yake ji ayanzu. Domin har wani zazzabi yaji Yana neman ya kama Shi,baisan Yana son muhseena ba sai yau domin yadda yake Jin tamkar zaa cire masa rai.

NI MA MATARSA CE Where stories live. Discover now