page 7

53 6 0
                                    

NIMA MATARSA CE
                       NA
     HÀBIBA ABUBAKAR IMAM
          BABI NA BAKWAI
           ******************
   Washegari jikin mujaheeda yayi sauki sosai, sai dai kallo daya zaka Mata Ka tabbatar da tana cikin matsananciyar damuwa. Haj murjanatu kuwa sam bata jindadin irin kallon da mujaheeda take yi mata mai cike da tuhuma da dora laifi.
  Ta tashi daga inda take zaune ta dawo kusa da mujaheeda ta zauna tana kallon ta cike da kulawa, ta Kara Ciro wayarta ta Kira Taufiq karo na kusan goma sha daya kenan data kirashi tun daga wayewar gari amma babu kiranta daya Wanda ya daga.
 
  Ta Kara kallonta tace " Na Kira Taufiq sama da sau goma amma yaki daga wayata"
  Mujaheeda ta waiwayo ta dubeta sosai tace " me zaiyi Miki kike kiransa" ta dan hadiye yawu sannan tace " Zan bashi hakuri ne " a gaggauce ta Kara kallonta ta maimaita maganar " zaki bashi hakuri?" Ta gyada Kai tace " kwarai da gaske matukar yin hakan zaisa ki Sami natsuwa da kwanciyar hankali to Zan bashi hakuri, Amma Kiri Kiri yaki daga wayata saboda dole sai nuna bani da kima ko daraja agunsa"
     Dai dai lokacin Àlh Mustapha labaran ya shigo cike da jindadin yadda yaga mujaheeda ta sami sauki kai tsaye ya wuce bakin gadon Yana kallonta " mujaheeda yaya kike Jin jikin naki" ta gyara kwanciyar ta ahankali tace " Naji sauki daddy".
  Yace " Alhamdulillah Allah ya Kara lafiya, Kuma ina son ki daina sama kanki damuwa wacce kinsan damuwar ba zata gagara na warware Miki ita ba , saboda Auranki da Taufiq insha'Allah babu abinda zai hana Shi kasancewa "
  Cike da shagwaba tace " Naji daddy Amma fa har yanzu bai kirani ba"
  Ya girgiza Kai yace " Kada ki damu bai kiraki bane saboda bai San kina asibiti ba"

" Ta yaya zaisan tana asibiti bayan yaki daga Kirana babu irin Kiran da banyi masa ba Amma yaki dagawa ".
  Gànin idanun mujaheeda sunyi rau rau alamun son tayi kuka yasa Àlh Mustapha labaran ya dubi Haj murjanatu yace " Haj zo" ya Fadi maganar Yana fita daga cikin dakin ayayinda Haj murjanatu ta bishi abaya.
   Daya daga cikin kujerun dake girke a waje Haj murjanatu ta zauna ayayinda Àlh Mustapha labaran ya cigaba da tsayuwa Yana kallonta sannan yace"  Ràshin daga wayarsa ba wata damuwa bace tunda kina da damar da zaki iya zuwa har gidansu Taufiq ki basu hakuri" da sauri ta juyo tana kallonsa tace " gidansu Taufiq na basu hakuri?" Ya gyara tsaiwarsa yace" eh babu wani abu ni Zan iya daukarki muje ki basu hakuri komai ya wuce, bana Jin Kuma zai Zama matsala kema agareki  idan akayi laakari da kema kina bukatar kwanciyar hankalin mujaheeda kina son kiga ta bar kan gadon asibiti ba tare da damuwar komai ba"

NI MA MATARSA CE Where stories live. Discover now