page 10

74 4 0
                                    

NIMA MATARSA CE
                     NA
   HÀBIBA ABUBAKAR IMAM
         (YAR GIDAN IMAM)
      BABI NA GOMA
                  **********
    " Ta yaya zakace mujaheeda bata da dalilin yin aiki , bayan dukiyarta ce take son ta koyi yadda zata ciyar da ita gaba,
Bayan duk irin kokarin da mahaifiyarta tayi na ganin ta tafiyar da hsrkokin ita kadai yanzu Kuma lokaci yayi da zasu hada hannu tare su taimaki junansu sai kace ba haka ba, idan har Ka yarda da matarka meye abin damuwa don kawai zatayi aiki bayan aikin nan ba na wani tashin hankali bane babu abinda zai rageka dashi".
   Ran Taufiq ya shiga kuna domin fahimtar da yayi bazai samu goyon bayan mahaifinsa ba akan maganar, shin meyasa Àlh Yusuf lamido ya dauki soyayya ya dorama mujaheeda Anya kuwa hakan bazai zamo illa agareshi ba.

  Haj saratu ta Kara hade rai tace " gaskiya Alh Kada Ka ce zaka goyi baysn su mujaheeda Akan maganar nan, shima Taufiq Yana da damar da zaa tsaya aji uzurinsa a Kuma girmama hukuncinsa ko kuwa shikenan Shi yayi aure ne kawai Amma baida yancin juya akalar gidansa yadda yake so"
Alh Yusuf lamido ya girgiza Kai yace " aah babu Wanda zai kwacema Taufiq wannan damar domin Allah ne ya bashi haka zalika bazan takura masa ba akan duk abinda ya yanke Amma ina son ya Sani Bana son damuwar mujaheeda ina so na bàta duk abinda ranta yake so badon komai ba sai don abinda mahaifinta yayi min arayuwa"
  Haj saratu tace "abinda mahaifinta yayi maka ai Bai maka don Ka rama mishi ba , balle har tasa Ka nemi tauye hakkin danka saboda kawai farincikin mujaheeda ".
   Yau dai Taufiq Yana son yaji abinda mahaifin mujaheeda yayi masa da har ya dauki Kula da yarsa da farincikinta amatsayin hanyar da zai saka ma mahaifin nata duk da kasa ta rufe masa Ido.

  Yadan dubi mahaifinsa kadan yace "wai Abba me mahaifin mujaheeda yayi maka ne da Ka dauki saka masa amatsayin dole duk da baya duniya".

   Ya numfasa gami da kallon Taufiq sosai , sannan yace " abinda Àlh sulaiman yayi min wani abu ne Wanda har na koma ga mahaliccina bazan taba mantawa ba .
Baya ga maidani babban yaronsa a office da bani dukkan wata daraja da kima , yayi min Kuma wani babban abu Wanda shine nake kallo nake Jin Zan iya yima yarsa komai matukar zatayi farinciki don nasan duk duniya baida wani abinda yake so sama da ita.".
  Ya Kara numfasawa sannan ya cigaba da cewa " mahaifiyata ta kwanta jinya kasani ciwon koda alokacin Bani da Shi Banda kudin dazan iya daukar dawainiyarta , nasan ba zaka manta irin mugun yanayin da Muke ciki ba lokacin,
A wañnan lokacin zaayi Mata aiki na kudi masu matukar yawa Wanda alokacin KO kwatan kudin ban mallaka ba , mahaifiyata na cikin mummunan halin da ko dai mutuwa ko rayuwa, na cire rai da ita don nasan banda inda Zan Samo kudin nan, ko a office Shi da Kansa Alh sulaiman ya fahimci ina cikin wani  mawuyacin hali da ya tambayeni Kuma banyi kasa a guiwa ba na gaya masa damuwar da nake ciki, ya bani hakuri tare da yima mahaifiyata fatan Samun sauki.
  Amma wani abu da ya bani mamaki aranar bayan na dawo gida , na shirya na koma asibiti sai likita ya tabbatar min da cewa gobe zaa yima mahaifiyata aiki saboda an riga an biya kudin aikin."
  Ya juyo ya dubi Taufiq yace " kasan waye ya biya kudin aikin Haj " ya girgiza Kai yace " aah "
Alh Yusuf lamido ya gyara zamansa yace " Alh sulaiman shine ya biya kudin aikin Haj, Kuma tun daga wannan lokacin shine ya cigaba da daukar dawainiyarta har Ta koma ga Allah ".
  Ya Kara zuba idonsa Akan Taufiq yace "yanzu Wanda yayi maka haka shine kana da damar da zaka saka masa Amma Ka kasa, kasan girma da kimar Uwa ? Na rantse maka duk Wanda ya kyautatama iyayenka bazaka taba mantawa dashi ba don haka mujaheeda matukar ina raye bazan taba bari ta tozarta ba don haka ya rage naka Ka taimaka min na sauke nauyin da na dorama Kaina , barinta tayi aiki babu wata illa matukar zata kare mutuncinta ta kare naka".
Haj saratu dai fuskarta bata nuna jindadin wannan hawan kawaran da ake yima danta ba , domin bata hango adalci acikin lamarin ba, ta maida idonta Kan Taufiq tana matukar Jin damuwarsa acikin zuciyarsa

   Taufiq ya numfasa hakika Bai son mujaheeda tayi aiki , babu hakan acikin tsarin auransa da ita, Amma yaya zaiyi tunda Yana son kwanciyar hankalin mahaifinsa , yadan gyara zamansa yace " Shikenan Abba, taje tayi aiki ba wani abu ".
Haj saratu tayi karaf tace " Kada Ka takura kanka idan Baka son tayi aikin nan fa dole zata hakura ". Ya dubeta yace " bakomai na barta taje tayi aikin"
  Haj saratu ta kauda kanta cike da Jin haushi domin dai tasan dole akayi masa don ba haka yaso ba .hakan yasa ta Mike tsam tabar falon.
Alh Yusuf lamido ya nuna jindadin sa kwarai matuka gami da sa masa Albarka, sannan ya cigaba da kwantar masa da hankali tare da misalai Kala Kala Akan ràshin kasancewar matsala ga aikin mujaheeda, sai dai Sam ba wata gamsuwa da Taufiq yayi domin dai hankalinsa bai kwanta da hakan ba , ya Jima a gidan kafin ya wuce gida zuciyarsa cike da Jin zafin yadda mujaheeda ta kwaso matsalarsu ta kawota gaban mahaifinsa.

NI MA MATARSA CE Where stories live. Discover now