page 37

57 6 0
                                    

NIMA MATARSA CE
             NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM
  ( YAR GIDAN IMAM )
BABI NA TALATIN DA BAKWAI
           *************
    Durmi kauye ne me ruko da al'ada da kaucema duk wani abu da zai zamanto sanadiyyar zubewar mutuncinsu. Hakan yasa suke taka tsan tsan da rayuwar yayansu gami da killacesu , duk da kasancewar talauci da ràshin wadataccen ilimi agarin to bai hana iyaye tsayawa akan tarbiyyar yayansu ba. Musamman da garin kowa ya San kowa domin a wancan lokacin mutanen garin babu yawa.
   Mahaifin Hajara mallam sule Yana daya daga cikin irin wadannan mutanen da suke kafe da idanunsu akan yayansu tare da kokarin tabbatar da tarbiyya akansu.

Duk da Hajara itace kadai Allah ya bar masa acikin Jerin yayan da matarsa daya tilo zainabu ta Haifa masa guda biyar, duk sun rasu ita kadaice tayi saura hakan yasa ya dauki kauna da so na duniya ya Dora Mata, talaka ne sosai domin bai aje ba baiba wani ajiya ba  duk da gidansa babu yawa to daker ake Samun abinda zaaci .

Noma yake yi Wanda kafin wata shekarar ta zagayo ya Gama kakkabar da komai babu dai tayi kaka gida acikin rayuwarsa hatta gidan da suke ciki ba nashi bane haya yake yi, tunda shima baida wasu yan' uwa Kuma babu abinda ya mallaka daga gadon mahaifinsa tunda shima Bai da Shi.

   Rayuwar Hajara ta cigaba ba yabo ba fallasa babu karatun boko sai dai makarantar allo Wanda itace kadai ta taimaketa arayuwa.zainabu kuwa babu wata Sana'a sai dai dan aikatau shima din Saita samu, hakan yasa ake zaune babu Mai taimakon wani. Rana tsaka Allah ya dorama mallam sule lalurar ciwon kafa daji ya kama masa kafa tun Yana jurewa ya na dauriya ya dingisa ya fita yadanyi buga bugarsa har abu ya Fara fassakara domin yadda kafar ta kumbura tayi suntum ga azabar ciwo mara musaltuwa dole ya tsuguna agida ana maganin gargajiya shima din sai Allah yasa an samu Wanda zai iya hakurin bada bashi . Sannu ahankali itama daya kafar ta kama ruwa mai wàri na fita daga jikinsu. Awannan lokaci babu wani tashin hankalin da Hajara da mahaifiyarta suka taba shiga sama da wannan arayuwarsu, ciwo ya samu da talauci haka zainabu take fita aikatau ita da Hajara domin Samun abinda zaa ci da Wanda zaayi magani.

Abin takaici Kuma babu mai taimaka musu domin kowa ta Kansa yake Masu Dan zuwa gaida Shi ne suke dan bada kudin da bazai isa ayi komai ba. Rayuwa fa tayi ma gidan mallam sule zafi dole tasa yar gonar tasa ta rufin asiri ya daga ya sayar domin yin magani. Alokacin ne aka basu shawarar zuwa babban asibiti a jigawa domin a duba Shi.
  Aminin malllam sule mallam kallah shine yayi masa rakiya zuwa general hospital na jigawa. Gwajin farko aka gano cancer ce ta kamashi Kuma harta Fara yaduwa ajikinsa . Take suka bashi gado aka cigaba da gwaje gwaje . Mallam kallah shine ya Komama zainabu da labarin an kwantar dashi don haka itace ya kamata ta je ta zauna dashi.

Hakan yasa sauran Yan kudin gonar ta tattara washegari Mallam kallah yayi musu jagora da zainabu da Hajara zuwa jigawa. Aranar Shi ya dawo gida su Kuma suka cigaba da zaman jinyar Mallam sule.kullum cikin bukatar kudin magani ake ga abinda zasu ci kullum haka suke Zama da yunwa ko Kuma idan masu jinya sun rage abinci su Basu su ci. Zaman asibiti dai Bana kare ba domin duk kudin hannunsu sun gama kakkabewa, hakan yasa  zainabu take tura Hajara wajen asibiti tana Dan nema musu taimako.

Wata Mata da take jinyar danta Haj lami idonta nakan su zainabu sosai take tausaya musu domin ta fahimci suna cikin tsananin talauci , sau tari duk abincin da aka kawo Mata tana duba ta Basu tana Kuma Kula kwarai da hankali da nutsuwar irinta Hajara .cikin kankanin lokaci Haj lami ta Saba da zainabu ita kanta zainabun bata kyashin gaya Mata halin kuncin da suke ciki Basu da mataimaki sai Allah. Wata ranar laraba ne Haj lami ta dubi zainabu tace " gaskiya Mijin ki Yana jinya Mai wahala ,ba zaku iya da asibitin nan ba" zainabu ta numfasa tace " gamu gatan kowa Allah, ai Haj idan ba Dama tattarawa zamuyi mu koma gida kawai" Haj lami tace " to ammafa ciwon nan yayi yawa ajikinsa bazai yuwu ace wai Ku koma gida ahaka ba" tace " to ya zamuyi babu ai bata gwaninta" Haj lami ta gyara zamanta tace " da babu damuwa da nayi miki wani taimako" zainabu tace " ta yaya zaa damu da taimako ai abinda Muke nema Kenan don Allah hajiya ina jinki". Haj lami tace " tunda yarinyarki tana da nutsuwa akwai wata Haj me kudi ce sosai mijinta ya rasu ya barta da ya daya gashi baa Dade ba ta Kara aure shine take ta neman me aiki , shine Naga ko Zan Kai Mata itane ta Fara Mata aiki kafin asallameku kinga anan zata samu abinda zaku ci da Kuma kudin aikinta don Zan CE kullum ne zaa dinga bata albashinta basai wata ba kinga kafin asallame Ku akalla kun Sami abubuwan da zaku rage wahala da wannan fita neman taimakon da take yi awaje ai ina ganin gara wannan din".

NI MA MATARSA CE Where stories live. Discover now