continuation page 6

77 6 0
                                    

Alh Mustapha labaran ya zauna kusa da Haj murjanatu Yana dubanta, sannan yace " meya faru da mujaheeda wani abin ya bata Mata rai ne ,,ko kuwa dai hakanan ciwon ya tashi, abinda ya dade bai tashi ba"
  Tadan yi jim gami da muskutawa sannan tace " Babu abinda ya faru , hakanan naji ihunta ko kafin na shiga harta sume" ta Karasa magana tana kokarin goge hawayen da suka Fara fitowa daga idanunta.

Alh Mustapha labaran ya girgiza Kai yace " Allah ya bata lafiya " asanyaye ta amsa " Amin ya Allah".
  Sai bayan issha' I sannan Allah ya nufa mujaheeda ta farfado ,idonta nakan mahaifiyarta wacce take ta murnar ganin ta dawo hayyacinta, ta dauke idonta akanta tana  runtse idanunta ,kalaman Taufiq sune suke yawo a kwakwalwarta .
Hakan yasa idanunta suka cika da hawaye .Alh Mustapha labaran ya Lura kwarai da hawayen dake fitama mujaheeda, ahankali ya nemi bakin gadon ya zauna Yana kallonta gami da Kiran sunanta, bata amsa ba sai hawaye da ya cigaba da wanke fuskarta.
  Yadan Matso kadan kusa da ita Yana cigaba da kallonta sannan yace " mujaheeda menene? Jikin ne? Ko wani abun Yana damunki ne ?".
Haj murjanatu ta taso " me zai dameta daya wuce ciwo" ya waiwayo ya dubeta yace ' kila bakiga damuwar da ke cikin kwayar idonta bane ,ko Kuma kingani kin zabi ki kauda Kai akan damuwarta ta " ta dubeshi sosai tace " Akan me Zan juyama damuwarta baya ,bayan duk duniya bani da wata damuwa da ya wuce damuwarta "
Asanyaye cikin galabaitacciyar murya mujaheeda tace " idan har damuwa damuwarki ce , da baki zama sanadiyyar damuwar tawa ba".
   A gaggauce Haj murjanatu tace " nice sanadin damuwarki mujaheeda?" Ta Karasa magana idanunta na kafe akanta.
Ta jinjina Kai alamar hakane. Hakan yasa Alh Mustapha labaran ya dubi mujaheeda cikin kulawa yace " ki kwantar da hankalinki ki gaya min abinda ya faru "
  Cikin kuka sosai mujaheeda ta sanar da Shi duk abinda yafaru da Kuma hukuncin da Taufiq ya dauka akan hakan.ta karasa magana cikin kuka tana cewa " Kin fi kowa sanin irin son da nakema Taufiq Amma kin kasa dannems zuciyarki tsanar sa balle har ki tayani sonsa, shin meye illar Taufiq me yasa kike raina arzikinsa kike ganin tamkar bai dace dani ba , bayan NI kadai nasan irin dacen  da nayi da samunsa,meye na dole sai kin muzanta Shi .
  To abinda baki sani ba shine Taufiq zai iya jure ki wukakanta Shi ki ci masa mutunci kiyi . masa komai amma bazai taba jurar ki wulakanta masa yan'uwa ko iyaye ba, yasha gaya min matukar abinda kike masa ya wuce Kansa ya fada Kan iyayensa Ko yan' uwansa to zai iya hakura dani har abada"
Ta Kara tsare mahaifiyarta da Ido sannan ta cigaba da cewa " Dalilin da yasa kenan dana dawo na tadda abinda kikayi akan lefen hsnkalina ya tashi saboda bansan irin abinda kika gaya masu ba, har sai da Taufiq ya kirani ya Kuma tabbatar min da wulakancin da kikayi ya Kuma gaya min ya hakura na gaya Miki kije ki aura min Wanda kike so Wanda zaki fi samun natsuwa dashi.bsyan kinsan duk duniya bani da wata natsuwa sai da Taufiq, bani Kuma da Wanda nake so nake Samun farinciki agunsa sai Shi .Na rantse idan ba Taufiq ba babu wani da namiji dazan iya aure sai dai na zauna babu aure har na  koma ga Allah ".

    Haj murjanatu ta kasa magana kanta na kasa har zuwa lokacin da Alh Mustapha labaran ya tashi ya dawo kusa da Haj murjanatu ya tsaya Yana kallonta , ta dago ta dube Shi tace fuska atamke "  Menene Ka tsare ni da Ido, don kawai an kawo kayan lefe na ce basuyi ba shine zai bullo da wannan maganganun na banza dama Yana neman na tafiya ne ,Kuma bai Isa ba ba' a haife Shi ba aurenki dashi ya Zama dole "
  Alh Mustapha labaran yace " Auransu ya Zama dole amatsayin ki na wacce zata ce dole ayi ko me? Taufiq shine yake da ikon dazai auri mujaheeda shine Kuma yake da ikon da zaice bazai aureta ba , saboda haka wannan izzar da kikeyi babu inda zata kaiki awannan Karon ya Zama dole ki sakko kije ki gyara abinda kika bata matukar kina son kwanciyar hankalin yarki,"
  Ta harzuko " To me zanyi ?" Ya gyara tsaiwarsa sannan yace " Ki nemi Taufiq ki bashi hakuri, sannan ki fita acikin salon zubar da kima da kika shiga ki rungumi abinda Allah ya kaddaro acikin rayuwar yarki kija girma da mutuncinki tun kafin ki rasa su awajen Taufiq, ki sani ke surukace wacce kike dai dai da matsayin Uwa awajen Taufiq,duk wadannan abubuwan da kikeyi ba  zasu haifar Miki da da me Ido ba.
   Ya kamata ki dawo cikin Tunaninki zuwa yanzu dai ko ba abinda kika karama Taufiq na muzantawa to ya sani wasuma sun sani cewar bai Miki ba , Baki sonsa zaki aura masa yarki don dole ne don tana sonsa Kuma lsifinsa daya ne don kina ganin ajinsa bai Kai ajin mujaheeda ba".
  Haj murjanatu tayi shuru nadan wani lokaci sannan tace " Nice Zan nemeshi na bashi hakuri" ya jinjina Kai yace " kwarai da gaske ammafa matukar kina son mujaheeda ta tashi daka Kan gadon asibitin nan ,ta Kuma Sami lafiya da Kuma mallakar abinda take so".
  Haj murjanatu ta girgiza Kai tace " Gaskiya bazan iya zuwa naba Taufiq hakuri ba, ai Bama zai yuwu ba ",
   Mujaheeda ta runtse idanunta zuciyarta na wani irin tukukin ciwo lokaci daya maganganun Haj murjanatu sukasa ta Kara birkicewa nan da nan idanunta suka Fara kafewa numfashi ya Fara Mata wahalar fita , gaba daya sukayo kanta daga bisani Àlh Mustapha labaran ya fice yaje ya Kira likita .
  Tambayar farko da likita ya Fara yi itace " Meya faru wani ya bata Mata raine" babu Wanda ya bada amsa acikinsu har likita ya Gama dubata yayi Mata allura wacce cikin kankanin lokaci bacci ya kwasheta.

NI MA MATARSA CE Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang