page 15

63 6 0
                                    

NIMA MATARSA CE
                         NA
  HÀBIBA ABUBAKAR IMAM
         (YAR GIDAN IMAM)
BABI NA GOMA SHA BIYAR
                    *************
     Mujaheeda ta dan kara dubansa tace " don Allah Kada Ka sama ranka wani abu harga Allah bani da nufin na kuntata maka illa iyaka ina son na maida hankali Kan abinda ya shafi kamfanin nan saboda akwai matsaloli da yawa kwance acikinsa,".
  Kai kawai ya maida kasa ba tare daya Ce komai ba, domin kuwa bai son Jan maganar itama fahimtar hakan da tayi ne yasa ta tattara ta tashi ta shige daki domin ta gyara kanta.
  Ayayinda Taufiq ya fada cikin nazarin yadda zai fahimtar da ita gaba daya baya jindadin dadin yanayin aikinta.
  Karfe biyar saura kwata na yamma wayar Haj saratu ta shigo wayar Taufiq, fitowarsa kenan daga wajen aiki da nufin ma ya tashi.
  Cike da girmamawa ya dauki wayar Yana kokarin gaisheta Amma jinta cikin wani yanayi na damuwa yasa yayi gaggawar tambayar ta abinda ke faruwa.
Tadan numfasa tace " Taufiq Ka hanzarta zuwa asibitin Kan tudu , an kwantar da Alh", a gaggauce yace " an kwantar dashi, yaushe ya Fara ciwon umma KO dazu da safe bayan na shigo office saida nayi waya dashi", tace " ai da Fara ciwon da kawo Shi asibiti ko awa biyu baayi ba," " gani nan zuwa umma" cewar Taufiq gami da kashe wayar, da sassarfa ya karasa bakin motarsa ya shiga lokaci daya yaja motar Kai tsaye asibitin ya wuce cike da damuwa da tashin hankali gami da adduar Allah yasa ba sosai bane.
   Isarsa asibitin ya tadda mahaifinsa sosai cikin jigata na ciwo,bayanin Kuma daya samu daga bakin likita shine ciwon sugar dinshi ne ya tashi domin sugar dinsa ta hau sosai.
  Yana zaune kusa da kafafun Alh Yusuf lamido Yana yi masa kallo me cike da tausayi ciwon sugar dinnan Shi kadaine yake cima Alh Yusuf lamido tuwo a kwarya Amma Taufiq ya rasa dalilin da yasa baya kiyaye dokoki da kaidojin ciwon musamman ma akan abinda yake ci.
  Ya waiwayi Haj saratu yace " umma agaskiya ya Zama dole Abba ya kiyaye Akan irin abinda yake ci domin likita ya tabbatar min da cewa irin abincin da yake ci sune suke jawowa sugarsa take hawa Kuma kiyaye abinda zaici yafi Shan magani muhimmanci agareshi Amma na rasa abinda yasa Abba yake wasa da lafiyarsa bayan yafi kowa sanin wannan ciwon Yana da matukar hatsari".

  Ta gyara zamanta Akan kujerar robar da take zaune akai, sannan tace " to ya zanyi dashi , babu abinda bana gaya masa Kan kiyaye dokoki Amma baya ji abinda yaso yaga dama Shi yake yi, ya ci abinda yaga dama yasha abinda yaga dama, to ta yaya zaiyi lafiya".
Taufiq yace " to aiko yanzu ya Zama dole ya kiyaye, tunda likita ya gayá min tahau sosai".
Haj saratu tace cike da damuwa" Allah dai ya bashi lafiya yasa Kuma kaffara ne".
Taufiq ya amsa da " Amin".

    Taufiq ya cigaba da Zama a asibitin tare da Haj saratu har dare yayi sosai karfe goma da kwata na dare , zuwa lokacin kuwa Alh Yusuf lamido ya Farka sai dai har yanzu akwai zafin ciwo atare dashi.
  Daga bisani Taufiq yayi sallama da su ya kama hanyar gida.
  Yana tafe Yana mamakin hali irinna mujaheeda da bazata iya daga waya ta kirashi ba taji halinda yake ciki musamman yadda yayi dare abinda bai saba yi ba.

    Fitilar motarsa ta haske wasu mutum biyu abakin titi, da sauri ya rage tafiya Yana kare musu kallo.
  Gabansa yayi mummunar faduwa domin tabbas idonsà ba gizo yake masa ba mujaheeda ya gani tsaye tare da wani namiji kusa da kusa suna magana,
  Yayi saurin kallon agogon hsnnunsa karfe goma sha daya saura na dare mujaheeda tana me awaje? Ita da waye? Me suke yi? .Jerin tambayoyin da yake yima Kansa kenan.
Jikinsa har rawa yake yi saboda kaduwa, saida yayi Dan gaba sannan ya tsaida motarsa inda Yana iya hangen komai daga inda yake.

   Mujaheeda ta saki jikinta sosai sunata magana da mutumin da Taufiq bai sani ba asalima bai taba ganinsa ba. Kwarai yaso yaji abinda suke fada.
  Shin waye Shi ga mujaheeda, shin ko dai mujaheeda amanarsa take ci, don idan ba haka ba me zai hadata da wani katon banza da wannan tsohon Daren.
  Akan idon Taufiq suka Gama maganganunsu, sannan kowa ya shige motarsa suka tafi.
  Taufiq ya aje numfashi ahankali ransa a matukar bace yawun bakinsa yayi daci saboda bakinciki.
Ahankali cikin matukar fushi yaja motar ya tafi.
Mujaheeda ta rigashi shiga gida don kafin ya shigo harta shiga wanka.
  A falo ya zauna duk abincin da masu aiki suka dafa na dare yana Kan tebur ko budewa babu wanda yayi.
  Yana nan zaune har mujaheeda ta fito cikin shirinta na kwanciya ta dubeshi cikin kulawa tace " yaya Taufiq kadawo" ya gyada Kai alamar eh batare da yayi magana ba, tace tana wucewa wajen tebur din cin abinci " Amma dai yau kayi dare".
  Ya juyo Yana kallon ta ta dakko farantin fruit tana sha daga tsaye, yace " ke Kuma yau kin dawo da wuri KO" ga mamakinsa sai yaji tace " ba lefi gaskiya yau da wuri na dawo ".

NI MA MATARSA CE Where stories live. Discover now