NI MA MATARSA CE PAGE 39

64 6 1
                                    

NIMA MATARSA CE
            NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM
  ( YAR GIDAN IMAM )
BABI NA TALATIN DA TARA
           ***********
  Hajara ta hadiye wani zazzafan yawu tace cikin kukan da ta kasa tsaida Shi.

" Inna ina cikin tsaka mai wuya,kullum zuciyata cikin masifar Kuna da damuwa take domin.na rufe bakina naki gayama kowa damuwata balle naji saukin masifar damuwar da nake ciki"

Zainabu adaburce tace " Hajara gaya min Kada kisa zuciyata ta buga , gaya min". Sannu ahankali Hajara ta Gama sanar da mahaifiyarta komai, Wanda zuwa wannan lokacin tuni zainabu ta fita hayyacinta nannauyan numfashi kawai take saki zuciyarta kuwa kamar ana rura Mata wuta ta Kai minti daya ta kasa magana sai Ido data zubama Hajara, saida Hajara tasa hannu tayi ta girgizata sannan zainabu ta dawo hayyacinta hade da fitar da hawaye daga kwarmin idanunta,

Cikin rawar murya tace " innalillahi wainna'ilaihirrajiun, yanzu Hajara abinda ya faru da ke Kenan Amma kika ki gaya mana bayan mune yakamata mu Fara sanin wannan bakar kaddarar " kuka take sosai tana cewa " Amma Haj ta ci amanar mu , tana nufin tace duk irin wannan ta'addancin da mijinta yayi Miki Shi take goyama baya, ta turo ki tace zata zo taki zuwa duk girman wannan maganar " Hajara ta goge hawayenta tace " tun kafin tahowata gaba daya ta canja min na fuskanci son zuciya da son Kai irin na mutanen birni Yana nan acikin zuciyarta " zainabu tace " me suka dauki mutanen kauye?, Marasa galihu ko marasa daraja wadanda Basu San yancin kansu ba?. Hajara har yanzu cikin kuka take tace " Inna ya zanyi da wannan bakincikin" zainabu ta kama Kai ta rike Kam Jin wani abu take yi Yana yi Mata yawo duhu kawai take gani agabanta ta rasa abinda ke yi Mata dadi.

Zainabu ta dago ta dubeta tace " Hajara ina son wannan maganar mu barta Bana son wani yaji wannan maganar, domin kinfi kowa sanin mutanen garin nan ba zasu taba yi mana Uzuri ko adalci ba matukar wannan mummunar maganar ta fita,mu aje ta anan mu cigaba da zaman jiran zuwan Hajiyar, duk da banji a raina zata iya taimaka mana da komai ba", ta Kara kallon Hajara tace " cuta dai an Riga an cucemu duk abinda zasu yi mana bazai wanke damuwa da bakincikin da suka jefamu ciki ba, shiko Alh bazan taba yafe masa ba har abada".

Hakika tunda zainabu take bata taba shiga bakinciki da tashin hankali irin na wannan dare ba, domin shine dalilin da itama bata Kara Samun bacci ba da daddare, duk dare hakanan suke kwanciya da ita da Hajaran duk babu mai iya runtsawa.nan da nan damuwa ta Fara nuna su duk da Mallam sule kwance yake Yana ji da Kansa to fa ya fahimci akwai damuwa haka yayi ta tambayar meke samunsu amma zainabu tana basarwa tana nuna masa damuwar ciwon sa ne kadai ke damunsa.

Amma duk da haka kullum cikin tambayar yaushe Hajara zata koma jigawa yake daga karshe dai zainabu ta gaya masa zasu Dade Basu dawo daga tafiyar da sukayi ba , shiyasa Hajara ba zata koma ba har sai sun dawo.

   Ahankali kwanaki suka shude satittika suka shude ayau watannin Hajara biyu da dawowa Durmi , Wanda har yanzu wannan lokacin Bai dauke damuwa da fargabarsu Hajara da mahaifiyarta ba, musamman da har zuwa wannan lokacin babu amo babu labarin Haj.

Ciwon mallam sule Kuma kullum gaba yake yi Dan saukin ma da ake Samu yanzu babu sai dai na musulunci.

  A wañnan lokacin ne Hajara ta Fara ciwon da aka Rasa Gane Kansa, laulayi sosai take yi duk abinda ta ci sai ya dawo.

Hankalin zainabu yayi mummunan tashi ta fada wani mugun damuwar domin idan har abinda zuciyarta take raya Mata gaskiya ne tabbas sun shiga cikin babbar masifa wacce bazata misaltu ba.

  Awani dare ne zainabu ta tada Hajara ta Kura Mata Ido cike da fargaba tayi Mata tambayar " Hajara yaushe rabonki da ganin al'adarki?". Duk da Hajara bata San ma'anar tambayar ba sai da gabanta ya Fadi sosai , ta gyada Kai tace " rabona da ganinsa tun ina jigawa Inna". Wata irin kibiya ta tsire zainabu a kahon zuciyarta kanta ya Sara wasu zafafan hawaye suka dinga fita Mata, ta Dora kanta a jikin cinyoyinta tana Jin kamar ta hadiye zuciya ta mutu.

NI MA MATARSA CE Where stories live. Discover now