page 24

54 5 0
                                    

NIMA MATARSA CE
                  NA
  HÀBIBA ABUBAKAR IMAM
    ( YAR GIDAN IMAM )
BABI NA ASHIRIN DA HUDU
               **********
     Ya shiga duba hotunan daya bayan daya, har ya Gama kallo sannan ya dago Kansa Yana kallon Taufiq sosai, yace " Amma banjidadi faruwar abinda ya faru ba, babu Wanda ya zugaka ya Kuma tilasta maka ganin laifin hotunan illa shaidan".
     Ya Kara matsowa kusa dashi Yana kokarin Mika masa wayar yasa hannu ya Karba a sanyaye.sannan Alh Mustapha labaran yace "Ta Yaya ko amanarka mujaheeda zata ci , ta rasa da Wanda zata ci amanarka sai Alh jibrin, mutumin da ya haifeta, Kuma amintaccen  mahaifiyarta ne, Shi Kansa bazai iya cin amanar Haj ba,Kuma nayi mamakin da ka kasa gane duk Wanda ya turo maka wadannan hotunan yayi ne don kawai ya shiga tsakaninka da matarka".
     Ya nisa ya cigaba da cewa " ban so faruwar hakan ba banso kayima mujaheeda magana ba ba tare da sanin ainihin gaskiya ba, Kuma Ka sani babu abinda mace ta tsana a duniya sama da mijinta ya zargeta akan abinda bata aikata ba Kuma zargi a aure babu inda yake Kai auran sai tafarkin rabuwa, ko Kuma a daina ganin mutuncin juna ".
      Taufiq ya yi kasa da Kansa zuciyarsa ta Fara nadamar faruwar komai, Amma ya kasa cewa uffan.
    Alh Mustapha labaran yace " don haka ina son kaje Ka zauna Ka natsu kayi ma duk hotunan nan kyakkyawan kallo da fahimta ananne zaka gane Basu dauke da abinda kake zargi" Taufiq ya gyada Kai yace " to Alh nagode ".
    Alh Mustapha labaran ya Kara kallonsa yace " zuwa yanzu dai ina son ka tafi kabar asibitin saboda yadda Haj ta fusata ko ni bazan iya shawo kanta ba idan yaso idan ta sakko komai ya lafa Zan sanar da Kai da Kaina kazo mu zauna Duka ayi magana".
    Shi Kansa Taufiq din zai fi bukatar ya Sami lokacin Kansa da zai zauna yayi nazari yadda ya kamata zamansa a asibitin kuwa zai iya sawa ya Sami sabani da Haj murjanatu domin yadda yake da saurin fushin nan Bai Jin duk ràshin gaskiyar sa zai yarda ta ci masa Kashi aka, don haka ya amince da abinda Alh Mustapha ya fada. Yayi masa sallama sannan ya juya ya tafi Shi Kuma ya Kada Kansa ya koma cikin dakin.

     Har yanzu mujaheeda na rungume a jikin Haj murjanatu, da alama Kuma mujaheedan ta Gama gaya Mata duk abinda ya faru tsakaninta da Taufiq, idan yayi laakari da yadda ta Kara fusata matuka.
      Alh Mustapha labaran ya dubeta yace " don Allah ki kwantar da hankalinki ki Sami natsuwa Haj a asibiti fa Muke ki Bari mana ta Sami sauki koma me zaayi sai ayi".
    Haj murjanatu ta dubeshi da jajayen idanu tace " wannan Karon Taufiq zai gane ya tabo ni, har ya isa ya jefi yata da Kalmar zina ni ban haifi maxinaciya ba Kuma zai yi nadamar fadin hakan" Alh Mustapha labaran ya girgiza Kai yace " yaushe yace Mata mazinaciya? Aah kadafa ki maida maganar wata iri" ta Watso masa Ido tace " meye bambancin kana zargin matarka da zina , ai abinda yake nufi kenan Kuma ma don wukakanci da Alh jibrin Kai  Kai gsskiya Taufiq ya ci mana mutunci ya zaluncemu".
   Àlh Mustapha labaran ya daga Mata hannu yace " naji Amma don Allah ki bar maganar nan don babu amfanin yinta anan ki bari mu koma gida tukuna".
    Ya dubi mujaheeda yace " ke Kuma ki daina wannan kukan ki yi shuru don baida amfani, Kuma ba wai warkewa kikayi ba hakan zai iya sawa ciwon ya Kara tashi kin dai fi kowa sanin dalilin tashin ciwonki saboda haka ya Zama dole ki kiyaye"
    Haj murjanatu tasa hannu tana goge Mata hawaye tana cewa " ki daina zubar da hawayenki Akan Wanda bai cancanta ba , Taufiq dai dole ya sake ki don ni ban shirya rasaki ba"
      Gaban mujaheeda yayi mummunan faduwa duk da tana cikin fushi da Taufiq bata Jin zata iya rabuwa dashi domin har yanzu tana son sa fiye da tunanin me tunani." Subhanallah haba Haj ta yaya kike irin wannan maganar ki kashema mujaheeda aure a wane dalilin" ta ce " adalilin kashe min ya da yake son yi da Kuma zargin banza da wofi da yake yi akanta"
    " To wannan ba ita bace mafita babu maganar saki, Zama dai zaayi ayima hanci tufka Amma har yaushe akayi  auran da zaace zaa rabu".
    Cikin fusata tace " to rabuwar aure da mutum irin Taufiq har wani abin damuwa ne, shiyasa tun farko ban so auran nan ba don nasan babu abinda zata samu a auran talaka sai bakinciki da kuntatawa amma saboda kwanciyar hankalinta na yarda ta aure Shi don gudun damuwarta Amma Shi ya kasa gane alfarmar da akayi masa na auran mujaheeda to zai sani, idan ma baya hayyacinsa ne zai dawo hayyacin nasa ".
    Cikin kosawa da maganar Àlh Mustapha labaran yace " duk naji a dai bar maganar zuwa ta samu lafiya". Ta saki tsaki gami da Kara rungume mujaheeda ji take tamkar ta cire duk wata damuwarta ta dawo da ita kanta, tana son yarta matukar so akanta zata iya yin komai.

NI MA MATARSA CE Where stories live. Discover now