Zumuncin Zamani

Από Nazeefah381

7K 517 25

Labari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda... Περισσότερα

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
50
51
52

49

119 8 0
Από Nazeefah381

Zumuncin Zamani...

Na

Nazeefah_____Nashe.

............

Ga mahmud lamarin ya fara jirkita tunaninsa kullum cikin nadama da tausayi yake, duk da har a lokacin zuciyarsa bata daina Jin tsananin son Fareedah ba, ji yake kamar ma yanzu ne son nata yake sake bunk'asa a zuciyarsa, hakan yasa zuciyarsa ta dinga tunanin Allah yasa Hisham 'din ya sako masa Fareedan shi kuwa da ko ta wane hali sai ya mallaki Fareedan a matsayin matarsa. Shi a karan kansa ya san abinda ya aikata 'din bai kyauta ba, Amma ya kasa tuge Fareeda daga cikin ransa. Ya lumshe ido hawaye na bin idanunsa bai San wace irin k'addara ba ce mai girma take bibiyarsu shi da Fareedan da Allah ya saka musu matsanancin son junansu.

Ya dinga tunanin ko Hisham ta gayawa iyayensu ko kuma ya saki Fareedan kamar yarda yake fata. Ya ji zuciyarsa tana k'arfafa masa gwiwar ya je ya tambayi Mommy a wajenta ka'dai zai San gaskiyar zancen.

__________

Jin wani abu ya fa'do mai 'dan girma daga gabanta ya tabbatar mata ta samu miscarriage, ta runtse idonta tana addu'ar samun sauk'in azabar da take ji. Da k'yar ta bu'de idonta tana kallon 'd'an tayin da ya fa'do daga cikinta har an soma masa halitta, ta bi jinin da kallo gaba 'd'aya Ya b'ata mata k'asan toilet 'din Allah yasa ta yi dabarar shiga toilet 'din da haka 'dakinta zai yi kaca-kaca da jini. Ta na'de 'dan tayin a zani tana fa'din Allah nagode maka da bai zo a raye ba, da da wani idon zan dubi jama'a?

_________

A tsaye ya tarar da Mommyn tana gyara 'dan kwalin kanta a jikin mudubi. Da ido Mommyn ta bi shi ganin jikinsa a salub'e ba k'wari sam a tare da shi. "Kai Moody lafiya na ganka haka sukuku da kai?" Ta fa'da tana k'are masa kallo daga sama Har k'asa ganin sam baya cikin kwanciyar hankali, sai yau ma ta lura da irin ramar da ya yi.

Ya 'dan girgiza Kai "Bakomai Mommy ina Jin headache ne ka'dan."

Tab'e bakinta ta yi don idan duk jikinta kunnene ba zata yarda ba, murya a sark'e ta ce "Idan ta yi wari ma ji ai."

"Yaya Hisham kuwa ya zo gidan nan?" Ya jeho mata tambayar yana k'ok'arin saka nutsuwa a ransa.

Tana cigaba da abinda take a jikin mudubin ta ce "Yazo, har ya koma inda ya fito.. wani abin ne?"

Ya girgiza Kai "A'a na zata ba ya gari ne? Matarsa fa?" Ta sake juyowa tana kallonsa da mamaki a fuskarta "Ina ruwanka da matarsa kuma?"

Ya 'dan ji fa'duwar gaba "Kafin ya ce a'a na zata tare suka tafi ne, akwai kaya na da nake son 'daukowa a gidan." "Ba tare suka tafi ba, ta ce ba zata bi shi ba.." wata kyakykyawar ajiyar zuciya ya saki da yasa har Mommy ta juyo tana kallonsa. Ya yi saurin ficewa don kar ta Jeho masa wata tambayar da zai kasa amsa mata.

Kansa tsaye shai'dan yana sake ingiza shi ya ja motarsa sai gidan Hisham. 

Tun daga falon k'asa yake k'wala mata kira "Hello Sweety na."

Jin muryarsa ya sa gabanta fa'duwa ta jefar da comb 'din da ta gama take gashin kanta da shi... cikin taraddadin an ya ba gizo muryar Mahmud 'din take mata ba? Idan banda haka me zai dawo da Mahmud gidan nan ko giyar wake ya sha?

Har saman ya hau cikin karsashi da k'warin gwiwa, wannan karan ya shirya tsaf ko da Hisham zai gan shi ba zai gudu ba zai tsaya ya bayyana masa irin son da ya kewa matarsa, waye ya ce ya sake ta wasarere? Ya barta kal mu'allak'ati?

Ya tura 'dakinta da ya san nan ne mallakinta, da sauri ta waro ido tana ja da baya cikin firgici.

Yana murmushi ya dinga bin ta, har suka dangana da bango cikin shauk'i kawai ta ji ya ha'da ta da jikinsa."

Da sauri ta tura shi "Bari Mahmud ba lafiya bace da ni, baya ga haka ina tsoro Ina tsoron Hisham ya sake ganin mu, tunda ya tafi bai ce min komai ba na San akwai abinda ya k'udirta."

Duk maganar da take Mahmud jinta kawai yake Amma baya gane mai take cewa, so kawai yake ya jita a jikinsa suna aikata abinda suka Saba aikatawa, wannan karan kam Fareeda ta k'i ba shi ha'din Kai duk da abinda ta ji yana mintsininta Amma ina? Ta tuba ba zata sake ba. Sai dai da yake Mahmud ya iya yaudara dole ya bi da ita ta salon da dole ta biye masa amma iya romances kawai saboda rashin tsarkinta. Allah yasa mu fi k'arfin zuk'atanmu. 

"Ni na fi son yazo ya gan mu, Fareeda na fi son Hisham y'a sake ki ni na mallakeki ko ta halin k'ak'a." Ya fa'da bayan ya kai k'ololuwa a cikin wani yanayi. "Ki bani ha'din kai kawai ki maka shi kotu ya sake ki ta k'arfi da yaji, ni nake son ki Fareeda ni na San yarda nake jin zuciyata a kanki, ni na San daraja da mutuncinki ba wancan mutumin da ya yasar da ke ba."

Ido kawai Fareeda ta zubawa Mahmud tana mamakin furucinsa kamar Wanda ya samu tab'in k'wak'walwa.

**** *****

Sai dare Hisham ya koma gidansa lokacin dai ya san Dangerr tasa tuni ta sauka daga fushin data 'dauka da shi na ba gaira ba dalili. Ai ko dai tsaf take zaune da walwalarta ta yi wanka tana sanye da doguwar riga y'ar senegal sakakkiya ire-ire kayan da ta tsiri sakawa kenan, don bawa cikinta damar sakewa yarda ya kamata. Tana ganinsa ta ha'de ranta don ta San ba mamaki daga wajen Fareeda yake, yana shirin tab'a ta ta 'd'an ja baya da sauri  tana fa'din "Kaje ka yi wanka don na San daga wajenta ka ke."

Zuwa lokacin ya kasa k'unshe dariyarsa sai da ya saketa sosai har da rik'e ciki, ta bi shi da kallo don bata tab'a ganinsa yana dariya kamar hakan ba. Ta yi k'wafa kafin murna a raunane ta ce "Ai na sani, dama don ka wulak'anta ni ka aureni, tunda mai mata kamar Indiya mai zai yi da ni." Ya daina dariyar yana kallonta ganin yarda take shirin saka mi shi kuka, "Enough, wallahi ke ki ke ba ni dariya kawai kin sakawa kan ki kishi, ita Fareeda tana kano ma ta bar Miki mijinki. Kuma kada na sake jin kin ce wai me zan yi da ke ina da india, ni a wajena ke ta dabance Allah ya sani, duniya ma ta shaida na fi son ki a kan Indiyar da ki ke fa'da.. ke 'din fa ta dabance.." Ya fa'da yana 'daga mata gira, tare da kai hannu yana share mata hawaye "Share hawayenki kin ji My dear, har abada kin fi min mata dubu a wajena." Tuni ta manta da b'acin rai ta shige jikinsa cikin murna da farin ciki don ta San ba zai gaya mata k'arya ba. Ya ja matarsa suka cigaba da nunawa junansu matsananciyar k'auna tuni ya manta da Fareeda da Mahmud da bak'in cikin da suka k'unsa masa.

A yanzu Ya fi mayar da hankalinsa akan business 'dinsa da son ganin Sauda ta sauka lafiya, tunda cikinta ya isa haihuwa don haka ma Umman Sauda ta tura Yayarta Abujan ta kula da Sauda 'din a lokacin haihuwa.

Sati kuwa bai zagayo ba sai ga Inna Salamatu Yaya Sa'eed ya rakota har Abujan da kayan zaman dab'aron da za ta yi mata, su yaji zuma sabulun salo garin kunu da sauransu, tare da tofin saukar Kur'ani da Abba Mustafa ya zauna ya biye mata a cikin ruwan zam-zam da kansa. Haka aka Ware wa Inna Salamatu 'daki guda ta yi zaman ta saurarar haihuwar dafatan saukar ta lafiya.

___________

Siyasa ta matso gadan-gadan, gaba 'd'aya gari kowa ya hargitse musamman y'an Siyasa da suke shirin fara zab'en cikin gida, don su kai sakamako hukumar inec ita kuma ta tantance wa'danda za su tsaya takarar.

Alhaji Hamza tuni ya fa'da dumu-dumu cikin siyasar, so yake kawai a zab'an cikin gidan ya ga Ya kayar da Sule Jami'i. Don haka ya siyar da duk kadarorinsa ya zuba ku'din cikin siyasa da tunanin idan ya ci duk zai mayar da kadarorin.

Shi Sule Jami'i ma dariya abin yake ba shi, duk da matarsa ta shak'a da lamarin sosai, yana tausayawa Abban Hisham 'din yarda ya 'daukota da zafi, idan banda haka ta yaya zai iya zuba takara da shi shi da ya samu shekaru a kujerarsa ya ce zai tsaya da shi a jam'iyya 'daya.

Mommyn Fareeda a hassale take kallon maigidanta tana ikirarin zuwa ta 'dauko y'arta tunda Alhaji Hamzan Ya zama kaza ci ka goge bakin ka. "Ka San Allah Abban Fareeda wannan iskanci ne sosai, idan ba haka ba ta yaya zai tsaya takara da kai a jam'iyya 'daya don fitsara? To y'ata zan je na 'dauko wallahi tunda shi ya zama butulu."

Murmushi Senetor ya yi babu abinda ya dameshi don ya 'd'au lamarin Alhaji Hamzan wasan yara. "Ba abinda ya ha'da zancen takararmu da auren Fareedah, ba zan take hurumin Ubangiji ba takara ce dai mu zuba ni da shi, abu 'daya na sani ba mamaki watan talaucinsa ne ya zo tunda ance ya ka'd'ar da gaba 'd'aya kadarorinsa abokai suna zuga shi yana rabawa deligate ku'di suna cinye ku'dinsa a banza da wofi."

Sai sannan hanakalin Mommyn Fareeda ya kwanta ta tabbata gaskiya mijin nata yake fa'da tabbas Iska tana wahalar da mai kayan kara. Alhaji ya mik'e yana fa'din "Bari na je na ji yadda ake ciki ina da meeting yau." Ta girgiza kai "Allah ya bada sa'a Abban Fareeda ya tsare min gabanka da bayanka." Ya murmusa yana ficewa da sauri..

___________

A hankali yake sarrafa motarsa k'irar mercedez benz 320 bak'a wuluk da ita sai walwali take a kan titin yana tuk'in cikin nutsuwa da farin cikin yau zai ga iyayensa bayan shekaru biyu........Khalil Mustafa Mai shadda.....

Συνέχεια Ανάγνωσης

Θα σας αρέσει επίσης

136K 9.6K 16
in which a boy leaves small notes on a girl's desk because he's too shy to actually talk to her in person
Alina Από ihidethisapp

Γενικό Φαντασίας

1.5M 37.3K 75
The Lombardi family is the most notorious group in the crime world. They rule both the American and Italian mafias and have many others bowing at the...
77.4K 3.5K 32
labarin BURINA labarin Zainab (Zee) da Khalil ( IK) da Abdallah (Alhaji) labarin soyayya ban tausayi da nishaɗi.
One More Mistake | ✓ Από ⭑

Εφηβική Φαντασία

205K 7K 66
When Thea Nightingale enters her senior year she didn't expect to see the boy who had died over a month ago in the same room as her, also the hatred...