Zumuncin Zamani

By Nazeefah381

7K 517 25

Labari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
38
39
40
41
42
43
44
45
47
48
49
50
51
52

46

133 13 1
By Nazeefah381

Zumuncin Zamani....

A bakin gate 'din gidan su Saudan Ya tsaya, saboda dama ya san gidan tun sanda ya siyeshi kuma Abban ya yiwa sha'awarsa sai dai ya san ko zai mutu Abban ba zai karb'a ba sai da wannan dabarar ta zo masa.

Gidan tas tun daga harabar gidan yake ji k'amshin girki, da gani babu tambaya suna cikin walwala sab'anin wancan lokacin, hakan ya sa ya ji da'di a ransa, fiye da lokutan baya da yake jin 'daci cikin ransa idan yazo ya tarar da su cikin k'uncin rayuwa.

A filin ya tsaya yana kwarara sallama, Wanda hakan yasa Umman Sauda ya fito da azama jin Muryar Hisham 'din tana ganin shine kuwa ta saki fara'a "Lalala! Maraba da Hisham, Abban Sauda fito kaga bak'o daga sama."

Abban Sauda shima da sauri ya fito daga falon sanye cikin wani yadi fari tas da shi, jikinsa ya yi tas fuskarsa har ta 'd'an washe ka'dan ba wannan duhun na bak'in talauci da ya yi musu dabaibayi.

"Maraba da Hisham, daga ina haka kamar an jefoka daga sama?"

Hisham ya zube gwiwoyinsa a k'asa yana gaishesu cikin tsantsar ladabi. "Daga Abuja Abba, Sauda ma tana can tana gaisheku ba zata iya doguwar tafiya bane shi yasa.."

"Dama Ina ita ina doguwar tafiya ai ina jin watan gobe ne watan haihuwar ta ko? Idan lissafin bai b'ace min ba." Umma ta fa'da tana kau da
Kai alamar y'ar kunya ka'dan na bayyana a saman fuskarta. Hisham ma cikin kunyar ya 'daga kai.

Kitchen ta shiga ta ha'dowa Hisham 'din kunun gya'da da na ayar da take siyarwa har da fura. Sai sinasir da miyar taushe Allah yasa ta gama shi da wuri da zafinsa shi ta musu da rana. Ta ajiye tray 'din a gaban Hisham. Ya dinga kallon kwanukan kamar dama ta San yunwa yake ji. Ba kunya ya ja kwanukan ya ci abincin sosai a ransa yana fa'din "Dole Sauda ta iya girki ashe gado ta yi." Sai da ya ci ya k'oshi nak kunun ayar mai sanyi ya sha ya bar kunun gya'dar a flask da zummar sai zai tafi ya tafi da shi da furar.

"Ya muka ji da hak'urin mu?"

Maganar Abba ta shiga kunnuwan Hisham a bazata. Da sauri Hisham 'din ya 'dago yana kallonsa gabansa ya fa'duwa ya ce "Hak'uri kuma Abba? Waye ya mutu?"

"Sa'adu 'dan uwanka." Hisham bai San sanda ta waro ido ba Yana fa'din "Sa'ad fa kace Abba? Yaushe ya mutu? Ya aka yi kuma ba mu sani ba?"

Ya fa'da k'wallar idonsa na gangarowa. Abban ya dake sosai baya son shima ya saki kukan kamar yarda Hisham da Maryama suke yi.

"Sa'adu baya buk'atar kukan ku Hisham, addu'a kawai yake so. Satinsa uku da rasuwa. Ciwon kwana biyu kacal ya yi Allah ya 'dau abin sa Allah ya ji k'ansa ya gafarta masa. Abinda ya sa ban sanar da kai ba Saudatu nake ji, bana son 'daga mata hankali saboda shine mafi soyuwa a wajenta a cikin y'an uwanta. Idan ta haihu sai a sanar da ita Amma yanzu kam ina jin tsoro. Allah ya raba lafiya yasa ita zata haifa min wani Sa'ad 'din."

Hisham Ya share k'wallarsa yana amsawa k'asa-k'asa.

"Ya aka yi ka samun labarin mun dawo nan?"

Abba ya yiwa Hisham tambayar da ta saka shi saurin 'd'ago kai.
Ya yi azama ya ce "Na je can gidan, sai suke sanar da ni kun ta shi su suka bani kwatancen nan 'din."

"Haka ne Khalilu ya fansheka ya siya mana gida don na San tuni kake da wannan burin... bakomai Hisham Allah ya baka ladan niyya." 

"Ma sha Allah" Hisham ya ce kamar bai San komai ba. Tsawon lokaci suna sake jima min rashin Sa'ad kafin su yi sallah da Abban ya kuma yi musu sallama, don ganin lokacin tafiyarsa zuwa Abuja ya yi don ta jirgi zai bi ya san kuma zuwa lokacin jirgin ya zama ready.

Har waje Abba ya rako shi yana sake jaddada a gaisar min da autata. Hisham ya dinga amsawa yana murmushi ha'de da saka ledar tarkacen Sauda da Umma ya ba shi na su kuka kayan ka'di dai da su Daddawa. Kamar ta San yanzu Sauda 'din tuwo ne kawai abin marmari a wajenta.


_______

Gaba 'd'aya ta fita daga hayyacinta, ta hargitse sosai takaicin da take ciki da nadama Allah ne ka'dai ya san su. Ta kira wayar Hisham yafi a k'irga Amma wayarsa bata shiga. Ta tabbatar blocking 'dinta Ya yi hakan kuma shine abinda ya dace da mai laifi irin nata. Zuwa lokacin ta tabbatar Hisham ya gama tarwatsa labarin mugun ganin da ya yi musu a wajen iyayensa da nata, ko ma tuni takardar sakinta ta isa wajen iyayenta.

Zagaye 'dakin kawai take, cikin wani irin yanayi kana ganinta zaka zata mahaukaciya ce sabon kamu, don har a lokacin rigar barci ce a jikinta da gashinta a barbaje Babu gyara.

Ta kafawa kanta ido ta jikin dogon mudubin da yake tsaye a 'dakinta, kamanninta Sun canja idan ba idonta bane ya gane mata sai ta ga har wani bak'i ta yi. Hannu ta saka cikin gashin kanta tana jansa da k'arfin gaske tana cizar lab'b'anta, sai a lokacin kuka ya kece mata, ta ji nadama na son zautar da ita sai dai Tuni loakcin nadama ita da kanta ta San ya k'ure mata.

Kiran sallahr da ya shiga kunnenta ne ya farkar da ita rashin sallatar azahar da bata yi ba. Jikinta a sanyaye ta shiga wanka don ta manta ko wankan tsarki bata yi ba. Sai da ta fito sannan ta tada sallolin da suka tsera mata, tana idar wa ta shiga kuka tana istigfari ga Allah da neman gafarar abinda ta aikata.

____________

Annurin dole ya 'd'auko ya dasa a fuskarsa, ba don ya so ba sai don ya san idan Sauda ta gan shi da wata irin fuska sab'anin irin wacce ya ke shiga gidan zai sha tambaya a wajenta.

Ya dinga Knocking sai dai Sauda bata ji shi ba, saboda ta tafi can duniyar tunani, da zatonta yana can ya lafe a jikin Fareeda suna shan Soyayyarsu shi yasa ta kasa samunsa a waya.

Abinci ta ke ci, Amma turawa kawai take ta kasa nutsuwa ta ci yarda ya kamata.

Ya cigaba da dukan k'ofar da k'arfi tunanin ba mamaki barci mai nauyi ne ya 'dauketa ga shi dama ita ka'dai ce a gidan. Sai da ya saka dutse ya dinga bugun sosai kafin ta jiyo shi. Ta mik'e a tsorace da tunanin waye zai zo mata, don dai ta San ba su yi da Hisham zai dawo a kwana guda kacal ba. Tunaninta Ya bata mai gadi ne ya zo amsar abinci don haka ta kawar da tsoron a ranta ta bu'de k'ofar babban falon.

Baki sake take kallonsa cikin mamakin ganinsa. Ya ware hannunsa yana sakar mata murmushi "Come on Baby, ni ne dai ba gizo nake miki ba." Ta saki ajiyar zuciya ha'de da fa'dawa jikinsa duk da cikin jikinta yana tokare su ka'dan haka ya rungumeta sosai a kunne yake ra'da mata "Am really missed you dear."  Ta 'dan janye jikinta tana raurau da idonta kafin ta kama hannayensa tana cewa "Why? Me yasa baka gaya min zaka dawo ba? Me yasa ka yi kwana 'daya jal? Allah yasa dai ba wani abin bane ya faru. Ina matar Gold 'din taka da ta hanaka 'daukar waya ta tun jiya nake nemanka?"

Dariya ce ta so kama shi ganin yarda kishi ya bayyana b'aro-b'aro a fuskarta. Tsokanatta ya so yi don haka ya gintse fuskarsa "Kamar kuwa kin san ita ta kanainaye ni da soyayyarta ta hana ni 'daukan wayarki. Kai Fareeda ta iya soyayya gaba 'd'aya ta mantar da ni a duniyar da nake." Da sauri ta runtse idanunta ta saka hannayenta ta toshe kunnenta Jiki na rawa ta wuce shi da sauri zuwa cikin falo. Ya yi dariya yana bin bayanta yana son ganin yanayin idanuwanta a lokacin da kishi ya turnik'eta idanun k'ank'ancewa suke yi cikin masifa.

Durk'usawa ya yi a gabanta ha'de da dafa cinyoyinta yana latsa su a hankali ganin yarda suka k'ara cika dum-dum da su. Bai gaji da tsokanarta ba don haka Ya yi k'asa da murya "Yanzu ma taimako na nazo ki yi na kuma nemi alfarmar ki, ki ba ni Aron bed room 'd'aya tare na zo da ita don na kasa hak'urin yin nesa da ita..."

Wannan karan a zafafe ta k'ura masa ido ta kasa cewa komai bakinta sai rawa yake don ta kasa fitar da maganar da take son ta gaya masa, bata son yi masa rashin kunya ta san tulin zunubin hakan, Umma ta gaya mata daga ranar da ta fara sa'insa da miji daga ranar k'imarta da mutuncinta za su ragu a zuciyar mijin bata fata ta zamo 'daya daga cikin wa'dannan matan, don haka ta mik'e da sauri ta shige 'daki Har tana jin k'ugunta yana amsawa.

Hisham ya bita da sauri sai dai kafin ya isa har ta kulle 'dakin da lock ta ciki, bugun duniya kuma ta k'i bu'dewa illa ce masa da ta yi "Bana buk'atarka ka wuce wajen matar gold. Ai dama ni nasan ba abinda zaka yi da ni kana tare da Balarabiya..".

Hisham murmushi kawai ya saki ya ja k'afafunsa ya wuce 'daya falon don ba k'aramin barci yake ji ba.

Bai san kuka Sauda kawai take sosai a cikin 'daki ba, zatonta duk abinda Ya fa'da 'din da gaske yake ba wasa ba. Ta da'de a kwance kafin ta mik'e jin ana kiran sallahr la'asar ta sake watsa ruwa ta zura wata rigarta zubin senegalese bu'daddiya daga k'asa da ta bawa cikinta damar sakewa sosai yarda ya kamata.

Bayan idar da sallahrta direct kitchen ta wuce. Ta fara shirin 'dora sassauk'an abinci da ba zai mata wahala ba. Jallop za tayi da peppe soup na kifi.

Tana wanke plates ya shigo kitchen 'din, sarai ta ji shi Amma ta yi burus da shi, Har sai da ya k'araso ya rungumeta ta baya yana sakin ajiyar numfashi wani irin feeling yake ji kawai ya yi missing 'dinta tsananin jiya kawai da yau. "Ajiye aikin nan, mu je mu yi ibada."  Da sauri ta dinga k'ok'arin k'wace jikinta, sai dai ta kasa don rik'o ya mata bana wasa ba, cikin wata irin murya ya ce "Wai me ye haka? Bari mana ko so ki ke na je waje na nemi matan banza?" Murya a cunkushe ta ce "Ka je wajen matar Gold." Tsam ya Zare jikinsa "Wallahi kuwa gwara ma da kika ankarar da ni, ana zancen Gold wa ya ke ta azurfa?" Da sauri ta waro ido cikin Jin 'dacin furucinsa ta ce "Ni kake fa'di ma haka?" Lumshe mata ido ya yi alamar "eh" bata san sanda ta saki plate 'din hannunta ba ya tarwatse ta saka k'afa ta tsallake ta bar kitchen 'din tana ganin duhu a idanunta ga jiri yana 'dibanta ka'dan. Ganin tana tanga'di hakan yasa Hisham ya tsorata da sauri ya bi bayanta don sarai ya san ba'a son tashin hankalin mai ciki..

Cak ya 'dauketa duk da tana tutturjewa Amma bai direta a ko ina ba sai a saman gadonta ya sauketa yana haki yana mamakin nauyin da ta k'ara. Ya kunna mata a.c ya zauna daf da ita ha'de da mayar da kanta saman cinyarsa yana shafawa kukan take son yi da sauri ya hau fa'din "Ki yi shiru Dearie, wasa fa nake miki duk abin nan wallahi It's just joking, kin ma ji ba rantse Miki da girman Allah."

Ta ha'diye wani Abu da ya tokare nata numfashi Jin ya yi rantsuwa ta tabbatar da gaske yake ta lumshe ido tana Kai masa duka da hannunta. Ya ha'da da ita da hannu ya rungumo jikinsa sosai "Yi barci ya isa haka.. ke kan ki kin san ko a mafarki na gaya Miki haka ai kya ce k'arya ne ba ni bane, sai dai wani ne ya yi basaja da kamannina, har abada ba ni da wata macen da zata Kai ki a wajena. I love you irin yarda ba zaki fahinta ba."

______________

Fareeda cikin wani irin ciwon ciki ta farka tana duba gadon ta ga ya yi faca-faca da jini gabanta na fa'duwa ta dinga bin jinin da kallo ta tabbatar ko ba'a fa'da mata ba b'ari ta yi, b'arin cikin da tun tuni suka so zubewarsa sai yanzu........ cikin na mur'da mata tana sakin kuka saboda gata dai cikin ciwo ga ba mataimaki a gida...

Continue Reading

You'll Also Like

83K 4.4K 59
labarine da ya kunshi rikitacciyar soyayya da ramuwa,Wanda masoyan suna son juna Amman sun kasa gasganta haka Wanda har suka kusa su rasa juna hmmmm...
445K 16.2K 192
Won Yoo-ha, a trainee unfairly deprived of the opportunity to appear on a survival program scheduled to hit the jackpot, became a failure of an idol...
Gentle touch By K

General Fiction

49.9K 1.1K 32
It had been mere months after her eighteen birthday, when she was pulled from the safe haven of her life and forced into the fantasy the women had cr...
3.2K 275 25
bana nada bayani kawai ki bibiyeni