Zumuncin Zamani

By Nazeefah381

7K 517 25

Labari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
38
39
40
41
42
43
44
46
47
48
49
50
51
52

45

109 13 2
By Nazeefah381

Zumuncin Zamani.

Na

Nazeefah Sabo Nashe

08033748387.

____________________

Jikinta rawa ya kama yi sosai ta kasa 'daga ido ta kalli Hisham da Ya kafeta da ido baya ko k'iftawa idanun nan sun ka'da sun yi jajir da su.

Hannunta ta 'dora a kai don ita kanta ta san ta gama yawo bata da abinda zata kare kanta ga Hujja zahiran b'aro-b'aro.

Bai mata magana ba don ba shi da k'arfin yi mata maganar ya juya jikinsa a salub'e ya fice daga 'dakin janye da akwatinsa da Ya shigo da shi.

D'akin da ta b'oye Mahmud nan ya nufa don ya san nan 'din ne kawai bata fiye shiga ba balle ta ajiye shirgi. Sauran kam tuni ta yi bake-bake da su suka zama nata kuma ba wani tsaftace su take yi ba.

Hannu ya saka Ya mur'da handle 'din da niyyar shiga amma ya ji shi gam a b'ame alamar an yi locking 'dinsa da mukulli. Mahmud da yake ciki tuni ya hau zare ido y'an hajinsa suka mur'da gumi ya cigaba da dita daga sassan jikinsa, Ya sani shikkenan tasa ta k'are don fes Hisham zai iya kashe shi, Har fitsari ya fara yi a wando don razana.

Fuskarsa a ha'de Ya juya ya kalli Fareeda da ta fara sakin fitsari a wando ya mik'a mata hannu "Give me the key." Bata da wani abin Yi da ya wuce mik'a masa Key 'din.

Yana bu'de 'dakin ya ga k'aninsa da suke Uwa 'daya uba 'Daya al'amarin da ya sake firgita shi, duk da ya da'de yana zargi da hasashen hakan amma bai kawo lamarin nasu ya girmama haka ba. Dalili kenan da ya bi kowane lungu na gidan ya saka secret camera musamman 'd'akinsa ba tare da ita Fareedan ta sani ba. Tun a asibiti ya fara kafa ayar tambaya a kansu sannan d aya dawo gida a ranar da ya dawo ya tsinci zoben da shi ya kawowa Mahmud tsarabarsa a tsakiyar gadonsa.

Jingina ya yi da bango yana jin zuciyarsa na masa wani irin suya. Mintuna biyu yana kallon Mahmud 'din Kafin ya lumshe ido ya nuna masa hanyar waje da hannunsa cikin tafasar zuciya.

Mahmud ya durk'ushe a wajen ya fara kuka "Don girman Allah Yaya Hisham ka yafe min, Wallahi sharrin shai'dan ne.

Wata irin tsawa da ya sakarwa Mahmud 'din ita ta saka shi ficewa da gudu ba shiri ya bar gidan.

Sai a lokacin Hisham ya samu damar zama dab'as a k'asa numfashinsa yana fita sama-sama tamkar ransa zai fita, ya fara tunanin wannan wane irin zamani Allah ya kawo mu mai cike da ru'dani, k'aninsa uwa 'd'aya uba 'd'aya shine yake mu'amalar matarsa suke aikata zina da aurensa saboda son zuciya. Tuni zafafan hawaye suka shigo masa ya dinga dukan kansa da hannunsa yana kaico da sanin Fareeda da ma amsa sunan matarsa da tayi.

Fareeda kuwa tana 'dakinta kuka kawai take  gaba 'd'aya duniyar ta juye mata nadama ce fal a ranta. Bata san wani hukunci Hisham zai mata ba, duk da dai ta san ba zai wuce hukuncin saki uku cur ba..  game da mahaifinta kuwa ta san ta ka'de har ganyenta ba mamaki ma ya tsine mata. Abu na gaba ko menene makomar yaronta? Sai a lokacin Wani irin kuka ya kece mata kukan nadama, Da na sani da kaico."

Da k'yar ya mik'e Ya fice daga gidan bayan ya yi wanka ya sake kayan jikinsa. Gidan su  Sauda yake son zuwa ya isar da sak'on Sauda da ya barta a abuja ko ya samuya rage ra'da'din da yake zuciyarsa amma sai ya ga gwara ya fara zuwa gidansu tukunna ya ga mahaifansa.

*****
Duk da ta yi farin ciki da ganinsa bata nuna masa akan fuskar ta ba ta ja fuskar ta tsuke tamau, so take lallai sai ta nuna masa kuskurensa na tafiya ya bar matarsa tsawon lokaci ba tare da ya waiwayeta ba. Mommynsa kenan da take zaune akan kujera hakimce a falo tana amsa gaisuwarsa kamar bata so.

Ya 'dan saki murmushin dole yana kama hannayenta. "Afuwa Uwa ta gari na san Mommy na sarai bata son Allah ya yi fushi da ni sakamakon fushin ta."

Ya san lagonta duk fushin da take da shi da zarar ya mata hakan ake neman fushin a rasa don da gaske bata son ganin y'ay'anta cikin fushin ubangiji.

Ta sauke nauyayyan numfashi "Amma dai ka san hakan da ka yi ba 'dabi'a bace mai kyau ko? Sai yanzu ka san ni Uwa ta gari ce ko Hisham? Da idonka ya rufe."
Ta fa'da tana tunanin aikin Malamin Falmata ne ya fara tasiri akan 'dan nata. "Tunda muka raba ka da waccan y'ar matsiyatan shikkenan muka rasa kanka Ai shikkenan Ta Allah bata mutum ba."

"Ba a canja hali ba." Hisham ya ayyana a ransa a fili kuwa k'asa ya yi da kansa yana zaro ha'dadden zoben gold a cikin gidan sa mai tsadar gaske ya kamo hannun Mommyn ya zura mata da bangles guda biyu "Ki sake hak'uri Mommy na." Da fara'a fal fuskarta take kallon hannunta fa'di take "Kai ba fa komai, ai itama matar taka bata damu ba rok'o a kawai ta yi na bar mata Mahmud ya dinga taya ta zama tana jin tsoro. Ai na san business ne ya b'oye ka." Ya dinga danne dariyar da take son kub'uce masa tabbas iyayensa sun kai k'ololuwa a soyayyarsu Da ku'di.

Daidai lokacin Abban nasa ya sauko yana gyaran murya yana ganin Hisham ya 'd'inke annurin fuskarsa Hisham Bai damu ba don shima ya shiryo masa tsaf.

"Barka da asuba." Ya fa'da yana 'd'an rusinawa. Ba tare da ya amsa gaisuwar da yake masa ba  ya ce "Ai na zata ba ni da darajar da zaka gaishe ni isashshe wanda ya kawo kansa duniya." "Ka Yi hak'uri Daddy wallahi abubuwan cigaba ne suka taso min shi yasa na tafi ba tare da shiri ba."

"Cigaba, cigaba kullum zancensa kenan cigaba, cigaba da mu ba ma gani." Ya fa'da yana gatsine fuskarsa.

Hisham dariyarsa ta kasa b'oyuwa wannan karan Sai da ya murmusa a zuciyarsa ya ce "An zo wajen."

Ya zaro wayarsa a aljihu yana danne-danne yana jin Daddyn ya cigaba da mita "-Au 'dan iska ma ka mayar da ni ga shashasha na yi ta yi kenan to bari....."

Cak ya tsaya yana kallon wayarsa da alert ya shigo masa milllion biyar ce Hisham 'din ya tura masa. Baki washe ya ce "To, To yanzu na ji batu, tabbas yanzu na san amfanin tafiyarka, Ubangiji ya yi albarka, ai kin gani ko Laraba tun farko sai da na Gayá Miki ba mamaki wani lamari ne mai girma ya tare ahi to kin ga zancena, Ai Hisham yaro ne na gari mai jin maganar magabatansa."

Saura k'irisa dariyar Hisham ta bayyana musamman Ganin yarda soyayyar ku'di ta bayyana b'aro-b'aro ga iyayensa. Hajiya Laraba ta ce "Ai shikkenan" tana nuna masa bangles da zoben da yake hannunta "Nima ga nawa abin arzikin."

Abban ya gyara zama "Gwara da ka dawo ma, dama ko baka dawo ba ina shirin nemanka Siyasa fa zan shiga gadan-gadan zan nemi kujerar surikinka Senator Sule Jami'i." Hisham ya waro ido "Siyasa kuma Abba, kuma har kujerar Senator ba ma 'dan majalissar jiha ba?"

"K'warai kuwa siyasa, ni da abokaina muka tsyar da shawarar na nemi kujerar wancan banzan mutumin mun gaji da k'anann wulak'ancin da yake mana don Yana da ku'di."

Hisham ya waro idonsa jin yana kiran Baban Fareeda uban gidansa Da banza, to me ya faru haka?

"Abba kujerarsa ta fi k'arfin ka, ba zaka iya takara da shi ba, don kujerarsa ta manyan masu ku'di ce da suka ci suka bawa ku'din baya..."

"Kai dakata Hisham bana son bak'in baki, nace maka bani da ku'din ne? Ina da over 100 million a account 'dina kuma kaf 'din su zan iya zuba su a siyasa don na cimma burina."

Hijab ya 'dan ha'diyi yawu don yana tunanin a iya primary election ka'dai ku'din Abban sai sun narke, sai dai ganin ya hassala yasa bai furta ba ya mik'e yana fa'din "To Abba fatan alheri, Allah ya taimaka ya yi jagora nima daga nan Abuja zan nufa kwana biyu zan yi na koma can k'asar."

"Masha Allah, Ubangiji ya taimaka, ka ce ba ka nan za'a yo takarar ta mu, sai a dinga mana addu'a Daga can 'din kuma a dinga watso mana na campaign kada Ka yi b'auro Idan na ci kaf kwangiloli kai zan dinga ba wa."

Hisham ya saki murmushi Kafin ya ce "Allah ya taimaka"

Mommy ta dubeshi kafin ta ce "Matarka fa?"

Hisham ya guntse fara'ar fuskarsa Allah ya sani ko suna Fareeda baya son ji balle zancenta.

"Ta sanar da ni ta fi son zamanta a nan, don haka na bar mata Duk abinda take buk'ata da isashshiyar Visa yadda idan ta buk'aci zuwa zata yanki ticket ta bi ni."

"Ai kuwa ba ka isa ba, k'afarka k'afar matarka." Mommy Laraba ta fa'da da mabayyanin b'acin rai kwance a fuskarta.

"A kan me? Ba kuwa inda zai je da ita tunda ita ta buk'aci zaman nan 'din, na lura sam yarinyar nan bata da mutunci daga ita har ubanta matsiyata ne, nan gaba ma idan ya ga ba zai iya zama da ita ba ya sakar musu y'ar su da kaina zan samo maka y'ar wani k'usan gwamnatin na aura maka, musamman Idan na k'waci kujerar Ubanta, da bakinsa fa Ubanta ya kira ni da 'DAN MAULA, don na je gidansa ina son ganinsa,  shine ya aiko yaran gidansa wai ya ce barci yake shi ba ya son maula, ai kuwa hakan yasa muka yi alk'awari ni da abokaina ko za mu yi yawo tsirara sai mun k'waci kujerar Sule Jami'i sai mun k'wace kujerar da yake tak'ama da ita zai ga Maula iya ganinsa."

Hisham dariya ya yi sosai, wannan karan sam ya kasa danne dariyarsa a zuciyarsa ya ce "An zo wajen dama ya san wannan ranar za ta zo ko mu da'de ko mu jima Ai bahaushe ya ce Idan Da kwa'dayi da wulak'anci... duk arziki irin na Abba sai ya saka ido akan na y'an siyasa har da son a auri y'arsa duk ba don Allah ba saboda ku'di saboda ya dinga ba shi kwangila ga shi nan an yi 2-0 ba wan ba k'anin, ga abin kunya da ta janyowa danginsu ita yarinyar da suke son.

Ya gyara zaman hularsa bai furta komai ba illa "Allah ya kyauta, na barku lafiya ." Ya sa kai ya fice yana jaddada girman ubangiji a ransa da yake sakayya yanzu tun a duniya..

A mota kuwa Sai da ya yi dariyarsa son ransa, Kafin ya ja motarsa zuwa gidan su Sauda duk wani b'acin ran da ya taho da shi ya zagwanye saboda dariyar da iyayen nasa suka ba shi.

Continue Reading

You'll Also Like

205K 7K 66
When Thea Nightingale enters her senior year she didn't expect to see the boy who had died over a month ago in the same room as her, also the hatred...
82.9K 4.4K 59
labarine da ya kunshi rikitacciyar soyayya da ramuwa,Wanda masoyan suna son juna Amman sun kasa gasganta haka Wanda har suka kusa su rasa juna hmmmm...
6.2K 234 25
labarin soyayya mai ciki da darussa iri iri mai masu tsayawa a zuci..masoyane suke nuna ma juna tsana marar adadi rana d'aya lokaci d'aya kiyaiyar ta...
2.3K 99 16
wannan sanyin illa zaiyi miki acancikin ki, ai ita mace da ɗumi aka santa, ai ballagaza ita ke illata ƙanta da ƙanta sai sanyi ya kamaki kizo kisani...