Zumuncin Zamani

By Nazeefah381

11.4K 575 25

Labari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
33
34
35
36
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52

32

208 12 1
By Nazeefah381

Zumuncin Zamani.

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

____________

Ganin kamar bai yi Maraba da kusantar da ta yi masa ba, ya sa ta koma can wata kujera gefe guda ta zauna ta nutsu sosai ta yi nisa cikin buk'atuwa da sha'awarsa fal a ranta, ga shi ba shi da lafiya, duk da Har a lokacin wata mu'amala ta aure bata tab'a shiga tsakaninsu ba.

Shigowar Mahmud ce ta farkar da ita daga tunanin da ta lula, ta zubawa Mahmud 'din ido shai'dan yana tunzira zuciyarta da wasu irin tunaninnika ayyana mata Mahmud 'din yake a zuciyarta a matsayin mutumin da zai yaye mata damuwarta. Sam a k'ira da fasali ba shi da banbanci da Hisham sai ma yarinta da ya fi Hisham 'din.

Bai lura da ita ba balle ya ga idanun data kafa masa sai dai a jikinsa idanun nata ya yi tasiri don ya ji ana kallonsa. Ya k'arasa wajen Hisham 'din yana fa'din "Yaya, bari ni na k'arasa gida tunda na ga Madam ta kasa ta tsare ga shi dare Ya yi."

Da sauri Hisham Ya ware idanunsa a kansa murya a cunkushe da b'acin ran uzzira masa da Fareeda ta yi ta kada ta tsare ta hana shi kiran Saudat ya ce "Ban gane ka tafi ba? Dama ba kwana za ka yi ba?" Da baki Mahmud 'din ya nuna masa Fareeda ha'de da fa'din "Ai na ga Big Aunty zata kwana" girgiza kai Hisham Ya yi ya na kai dubansa gareta "Ki kimtsa Mahmud zai ajiyeki a gida, shi sai ya dawo ya kwana anan 'din"

Itama idanun ta dallara masa "Ya za'a yi na tafi na bar ka Dear?" "Kin tab'a ganin mace ta yi jinyar namiji in dai yana da mai kula da shi? Ki tashi Ya kai ki gida sai ki dawo da sassafe."

Ya fa'da cikin dakakkiyar murya

Fareeda ta mik'e tana zumb'ura baki. Mahmud dubanta kawai yake yana murmushi a zuciyarsa yake ayyana "Tabbas Y. Hisham ya more da kyakykyawar mace, ina ma ni ne." "Wuce ka kaita." Ya juyo muryar Hisham 'din da ta farkar da shi daga wancan bahagon tunanin na k'iyasta kamanni da surar Fareeda a matsayin matarsa.

Suna fita Hisham Ya runtse idanunsa yana sakin ajiyar zuciya sai ji ya yi kamar an Zare masa k'aya, yanzu ne zai samu damar kiran Saudatunsa. Duk da baya son kiranta ya tayar mata da hankali Amma ya zama dole don zuciya da ruhinsa Saudatun kawai suke son gani.

Suna shiga motar suka samu bak'uncin shiru kowa da abinda ya ke kaikawo a zuciyarsa Fareeda kam a yanzu Shai'dan Ya Riga ya rinjayeta ji take tamkar ta afka jikin Mahmud ta rungumeshi tsabar yarda take jin sha'awarsa. Shi 'din ganin kamar Ya harbo jirginta kawai sai ya kasheta da kallo ido k'asa-k'asa ya ce "Ya dai Madam?" Wani irin ras ta ji tsigar jikinta ta tashi sosai jin yarda Mahmud ya kashe murya Ya ranga'da mata sunan Madam tuni wutar sha'awarta ta sake ruruwa itama ta zuba masa ido tana jingina bayanta jikin kujera da da dama data buk'aci Mahmud 'din ya kusanceta a lokacin.
Mahmud Ya saki murmushi tabbas yanayin kallon da take aika masa ya tabbatar da hasashen da zuciyarsa take masa ga wani turarenta da yake sake angizashi zuwa ga muradin zuciyarsa, da k'yar ya yi controlling kansa ya ja motar bayan ya kunna wani irin cool music.

Idanunta a lumshe suke ta ji Mahmud 'din ya ja burki hakan yasa ta bu'de ido tana sauke kallonta a kansa. Cikin murmushin da yake yaudarar y'an mata da shi ya ce "Bari na samowa Big Madam Ice cream
Ko?" Fareeda jiki a kasalance ta sakar masa murmushi ita ma ta ce "Kada ka je ka kwaso min tarkace let me follow you." Suka shige wajen Ice cream 'din yarda suke tafe suna gugar jikin juna idan ka gansu sai ka zata mata da mijinta ne.

__________

Sau kusan uku wayar Saudan tana ringing har ta mutu bata 'd'auka ba, ya kai dubansa kan agogon wayar da sauri Ya ware ido tabbas yarda ya san Sauda da saurin barci ya san tuni ta yi nisa a barci. Amma bai hak'ura ba ya cigaba da danna mata kira. A cikin barci ta dinga jin k'arar wayar da sauri ta bu'de idanunta ta janyo wayar ta mik'e zaune da sauri ganin Hisham ne akan wayar, don da tunaninsa ta kwanta da shi kuma ta yini cur ganin wuni guda bai kirata ba abinda bai tab'a yi ba. Cikin muryar barci ta masa sallamar. Muryar da ya ji ta tsarga masa har cikin k'arshen zuciyarsa. Ya saki ajiyar zuciya don sosai yake son muryar Saudatunsa shi yasa a koda yaushe muryar take sanya masa kasala don haka bai fiya amsa wayarta a gaban kowa ba don ko ya ya ya ji muryar tata sai ya lumshe idanunsa. Ya ji tamkar Ya fasa wayar ya rungumota jikinsa.

"Saudatu na Ina kika shiga ne yau baki nemeni ba?"

Madadin ta amsa masa wani kuka ne Ya ziyarceta ai kuwa ta fashe masa da kukan da ya ji shi Har tsakiyar ransa. Da sauri ya ce "Am sorry, bana son kukan nan gaya min menene Ya faru mhmn?"

Ga mamakinsa gaba 'd'aya yau Saudat ta jingine kunyarsa da take ji Ya ji tana fa'din "Na gaji Y.Hisham, wallahi soyayyarka zata hallaka ni, please ka yi wani abu na dawo kusa da kai, ina wahala sosai har ina mamakin wani irin so nake maka, please kada ka bari su raba mu."

Hisham ya runtse idanunsa wani dad'i annashuwa da farin ciki suna kwaranya a zuciyarsa Ya dinga cizon lab'bansa don ya tabbatar da gaske ne ba mafarkin da Ya saba yi ba. Jin da gaske ne Ya tabbatar son sa ya kai limit 'din da yake so a zuciyar Saudatunsa haka dama yake fata a yanzu ne Ya kamata Ya bijiro mata da k'udirinsa ya san ba haufi zata amince sai dai kash ga shi kwance a asibiti babu hali.

Saudat jin bai amsata ba sai ta yi tunanin ko ya amince zai rabu da ita ne don haka ta saka kuka, kukan da ya saka shi Ya dawo hayyacinsa ba shiri Ya ce "Enough Saudatuna saurara ki ji ji, Babu mai raba mu sai mutuwa itama In sha Allah tare za mu Mutu ko? Ke tawa ce For ever na fiki shiga cikin halin k'unci tunda Abba ya yi furucin rabuwarmu zuciyata bata huta ba nake aikin neman mafita, a garin dawowa daga gurin Baffan wudil ma na samu accident kin gan ni a asibiti..."

Ji ya yi kawai Saudat ta kece da kuka tana fa'din Innalillahi! Y. Hisham baka ji ciwo ba amma?"

Ya saki 'dan hucin murmushi ya ce "Ki sha kuruminki angonki bai ji ciwo ba sai dai na samu rauni a k'afa ina asibitin k'ashi"

Da sauri ta ce "Allah yasa ba karaya ba ce." Ya ce "No gocewar k'ashi ce, shima da sauk'i."

"Wani asibitin kake? Ana idar da sallahr asuba zan taho."

Cikin takaici ya saki ajiyar zuciya don Ya fita muradin haka sai dai ba dama, ba dama ta bayyana kanta a San suna tare "Saudat na fi kowa son ki zo 'din sai dai ina tsoron ha'duwarki da mutane, tunda kinga su Daddy suna zaton bama tare ki yi hak'uri kin ji?"

Cikin takaici Saudat ta kashe kiran tana hawaye ita ce Y. Hisham baya son gani saboda wani dalili mara tushe, wato baya son fushin matarsa.

Da sauri Hisham Ya sake kiranta sai dai da k'yar ta 'daga "Fushi ki ke Saudatu na? Baki fahimceni bane.."

"Ban fahimceka ba Y. Hisham, kuma wallahi sai na zo ko da za su ha'du su yi gutsi-gutsi da ni ba zan jure rashin ganinka ba ace Har sai ka warke wallahi ba zan iya ba."

Hisham ya razana da jin furucinta sam baya son zuwanta saboda komai zai iya faruwa, don haka ya yi k'asa da murya "Ki bari dear kin ji na fiki son mu ga juna tunda kika ji na ce haka akwai dalili.."
sake kashe wayar ta yi tana cono bakinta.

Shi kuwa murmushi a hankali Ya ce Saudatu Rigima Ya tura mata sak'on waya.

"Shikkenan Allah huci ran Gimbiya. Zan turo a 'd'auke ki hakan Ya yi miki? Nagode da kulawa ki kula min da kan ki.  Sweet dreams baby."

Tana karanta text 'don tana murumushi ta kaiwa wayar sumbata tana jin kamar lab'ban Hisham ne. Ta lumshe ido.

Shi dai Hisham ba yarda zai yi da ita ne, amma sam zuciyarta bata amince da zuwan nata ba sai dai ya zai yi da rigimar Saudatunsa.

Saudat da k'yar ta mik'e da asuba dalilin rashin isashshen barci, idanunta sun yi luhu-luhu.

Sai da suka yi sallah suka yi Azkar sannan ta samu Umma da Abbanta ta gaishesu ta kuma sanar da su zancen hatsarin da Hisham 'din ya yi

Salati suka saka gaba 'dayansu. Hankalin Abba Mustafa ya tashi jikinsa na rawa musamman jin cewa a hanyar wudil ya yi hatsarin ba ya haufi maganar Sauda ce ta kai shi kada fa ya zama silar Ajalin 'dan mutane dalilin takura masa da ya yi sai ya sakar masa y'a.

Cikin fa'da Ya ce "Shine tun jiyan ba ki gaya min ba Sauda? Wane asibiti ne?"

Sauda ta yi k'asa da kanta kafin ta ce "Ni ma ban sani ba, cikin dare ya gaya min yace min dai yana asibitin k'ashi.

Abba Mustafa bai bi ta kanta ba ya mik'e yana zura takalminsa ha'de da k'walawa su Sa'ad kira lokaci 'd'aya kuma yana danna kiran layin Hisham.

Bugu ka'dan Hisham 'din ya 'dauka bayan sun gaisa ya sanar da shi asibitin da yake da numberr 'dakin da komai. Abba Mustafa ya tasa y'an Samarinsa suka fice, suka bar Saudat tana jin tamkar ta bi su sai dai ba hali.

Umma ma ta bi su Zaure tana fa'din "Don Allah a yi masa sannu kafin na samu mu je In sha Allah idan zaka koma ko da gobe ne."

Tana ganin fitarsu ta zubawa Saudat ido cikin takaici ganin tana hawaye ta ce "Ko bin su za ki yi ne? Oh ni Maryama Allah wadaran naka Ya lalace yaran zamani kenan idan banda iskanci ana shirin rabaki da mutum kina sake nanik'e masa uban ma waye ya ce ki yi waya da shi? Bari ki ji in gaya miki dole ki rabu da shi wallahi ba kukan hawaye ba ki yi na jini ma shashashar banza kawai b'ace min da gani."

Jikinta a sanyaye ta mik'e ta bar Umman na kiciniyar ha'da abin karyawa ita kuma ta fara shirin sharar gidan.

Sun samu jikin nasa da sauk'i sai k'afar tasa da ta kumbura sosai da sosai. Yana ganinsu ya yi k'ok'arin tashi Abban ya dakatar da shi "Kwanta abinka Hisham ya jikin naka?" "Da sauk'i ya fa'da yana sake mik'awa Abban hannu kamar yarda Abban ya saba gaisuwa da shi. "Ma sha Allah, Allah ya k'ara afuwa sam ban sani ba sai 'dazu k'anwarka take gaya min." Hisham ya dinga jin tamkar ya gyarawa Abban sunan da ya kira Sauda da shi wai k'anwarka ina ma laifin matarsa.

Daddynsa ya turo k'ofa ya shigo yana ganin Mustafan ya dinga ha'da rai kamar ya ga babban abokin gabansa. Ganin haka Abba ya yiwa Hisham sallama suka fice.

Suna fita kuwa Daddyn ya dira masa fa'da kamar zai ci babu "Wato har yanzu baka ji magana ta ka rabu da mutanen nan ba ko? Allah na tuba ban tab'a ganin mutum mai nacin Mustafa ba ana korarka kana sake nanik'ewa an sakar masa y'ar ma ba zai bar mu mu huta ba, to wallahi zan sake jaddada maka kwabo ka sake taimakon Mustafa da shi nan yafe maka ba."
Shi dai Hisham rufe idanunsa kawai ya yi yana jin hargagin mahaifin nasa.



_____________

Zaune suke a tsakar gida Umma Maryam ta zabga tagumi da hannu bibbiyu. Wunin yau sir a wannan halin ta yi shi, tun sanda suka idar da sallahr asuba Abba Mustafa ya fahimci halin da take ciki, Amma bai mata magana ba sai yanzu da ya gama Azkar na yammacin la'asar ya dubeta "Wai ni Maryama yau lafiya ki ke? Ko Har yanzu zancen Saudatun ne bai bar zuciyarki ba?"

Umman ta girgiza kai "Ko ka'dan Malam, ni abinda ya dameni daban, zancen yaron nan a kwana biyun nan kullum sai na yi mafarkin sa wallahi sai nake ganin ko ba lafiya ba."

Abba Mustafa ya shanye tasa damuwar don ya kwnatar mata da hankali ya ce "K'alau Sa'eed yake In sha Allah, addu'armu zata riskeshi a duk inda yake kin san dai kaifin addu'ar iyaye ga y'ay'ansu ko? To ki k'addara sumul Sa'eed zai dawo mana In sha Allah.

Sakin ajiyar zuciya ta yi ta ce "Allah yasa Abban Sauda."

Abban ya fice yana jaddada "Khairan In sha Allah, ni na fita."

"Allah ya bada sa'a Abban Sauda Allah ya tsare." Ta fa'da tana mayar da kallonta kan Sauda da take fitowa daga 'daki tsaf da ita cikin kwalliya har da su jambaki, sai sannan Umman ta lura da wani irin gaske da ta yi sai shek'i take. Cike da mamaki Umman take kallonta "Yanzu Sauda group discussion 'din da zaki ne kika fecewa wannan kwalliya haka?" Diriricewa Saudan ta fara yi Umman ta tab'e baki. Har Saudan ta kai zaure ta k'wala mata kira. Gaban Sauda ya fa'di ta fara addu'ar Allah yasa Umman bata gano asibiti zata je ba.

Sab'anin tunaninta sai ta ga Umman ta mata kallon sama da k'asa ta ce "Yaushe rabon da ki ga al'adarki Saudatu?"

Continue Reading

You'll Also Like

220K 17.1K 22
On Hold Wanna visit rajasthan than read this special book about my love Rajasthan 💗
9.9K 325 25
labarin soyayya mai ciki da darussa iri iri mai masu tsayawa a zuci..masoyane suke nuna ma juna tsana marar adadi rana d'aya lokaci d'aya kiyaiyar ta...
1.5K 225 13
Cuando pueda verlo, ¿seguirá deseándolo? El multimillonario Ohm Thitiwat había perdido la vista al rescatar a una niña de un coche en llamas y la úni...
35.3K 2.8K 18
A historical fiction about a lost 🤴 Prince that came back after many years as a commoner