Zumuncin Zamani

By Nazeefah381

7K 517 25

Labari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
31
32
33
34
35
36
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52

30

149 10 4
By Nazeefah381

Zumuncin Zamani

Na

Nazeefah Sabo Nashe

08033748387

https://www.wattpad.com/1326143648?utm_source=ios&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Nazeefah381&wp_originator=vN8yhkTgvkG79FD7P8g%2B8QdvQVOSpRT2VWhGFEfjPLJt98qVYhGfWCF3NlVNN%2Bf0AYbiFUyU4V5qxl1T21VwcwfUZsJAWfQjWmqzhggjbTIA9%2BG8LVeqZFBzXRwAbzJ5


_________________________

Khalil ya dafa kafa'dar Hisham cikin tausayinsa ya ce "Calm down Hisham, ka bi umarnin Abba da mahaifinka. Saudat ba itace autar mata ba kuma rashinta ba zai saka ka samu nak'asu a rayuwarka ba. Balle kai da kake da Balarabiya a hannu."

"Enough Khalil, kai ma na lura kana bayan Abba ko? Kana bayan a raba mu idan banda haka me ya kawo wannan banzar maganar? Ai shikkenan...." Daga haka ya shige mota cikin k'unan rai. Mahmoud da wani mugun speed shima ya ja motar. Ya ba'dawa Khalil da ke tsaye k'ura alamar raini. Khalil ya bisu da kallo ba tare da ya damu da abinda Mahmud 'din ya yi ba damuwarsa Hisham da condition 'din da ya gan shi a ciki. 

Suna hawa titi Mahmud 'din ya juyo cike da takaici ya ce da Hisham 'din "Yaya Hisham, yanzu dama ba ka saki Saudah ba?"

Wani irin banzan kallo Hisham 'din ya jefeshi da shi, wanda ya saka shi yin shiru babu shiri. Hisham ya saki tsaki ya ce "Don ubanka ban saketa ba, kuma billahillazee na ji wannan maganar nan sai ka gane kurenka. Rubbish kawai!"

Mahmud gum ya yi da bakinsa, ga tsurku na cinsa ga shi babu halin bayyanashi, don ya san halin Hisham sarai I yunwar cikinsa, duk wasu ku'di da suke shigo masa da wani fankama da tak'ama da ya ke yi duk daga Hisham 'din yake samu, ya san idan ya fa'da kashinsa ya bushe don Daddysu ba ku'dinsa ake ci ba. Ku'din lukudi ne da shi.

Yana parking Hisham ya fito yana ha'da rai "Ba ni keys 'dina, kuma don ubanka ina jiran ka fa'da ka ji? Kada ka fasa." Yana fa'dar hakan ya wuce ya bar shi a tsaye.

Cikin zallar takaici Mahmud ya ware hannu ha'de da tab'e baki a fili ya furta "Kai ka ji yo, ana maka gata kana sake lik'ewa 'd'iyar talakawa, ni mai zai kai ni auran y'ar talakawa na yi wahala da ita na yi da iyayenta? Har a lokacin yana takaicin yarda shi ba'a ha'da shi da 'yar senator ba, da shi aka ha'da da ita da ya gama jin da'di duniya da lahira, harkar manya kawai zai dinga nunawa. Ransa ya b'aci, don yayan nasa ya garga'deshi da kada ya fa'da da Wallahi yau sai ya fa'da.

Hisham ransa a ha'de ya shiga falonsa, kamar yarda ya zata Fareeda na zaune tana dakon jiransa kamar mayya duk da kurarin ajin da take da shi da take. A fili ya ja tsaki don a rayuwarsa sam baya son naci shi yasa har yanzu tun zuwanta gidan bai bata hak'kinta ba, yana son ya ga k'urewar ajin nata da take tak'ama da shi kuma ya gani 'din. Tilas ya k'ak'alo murmushin dole  don ya bata kulawa a matsayinta na matarsa. "Madam ya gida?"

Wani kallo ta watso masa ya sani na tsabar jin haushinsa ne. Shi da kansa ya san ba ya kyauta mata don baya bata kulawa a matsayinta na matarsa duk a dalilin ita ta janyo aka nisanta shi da Sauda. Tausayinta ya 'san rinjayeshi ya zauna daf da ita ha'de da kamo hannunta ya saka kansa a bayanta yana shinshinar k'amshin turaren Oud Abyad da ta saka a jikinta. Cikin taushin murya ya fara da rarrashi da son janyo ra'ayinta. "Am sorry Madam, aiyuka ne suke min yawan da bana samun nutsuwar kulawa da ke. Kin san tun kafin aurenmu na sanar da ke busy man ne ni, so don Allah ki dinga taking abubuwa easy mhmnm?"

Runtse idanunta ta yi kawai sai ga hawaye sun fara gangaro mata, maimakon ta yi magana zame jikinta ta yi ta shige bedroom saboda takaicinsa ma ba zai barta ta yi magana ba.

Hisham ya bita da kallo yana son bin ta amma zuciyarsa ke masa garga'din ya k'yale ta, a yarda ya ga fuskarta ya tabbatar ta shak'a da yawa. Ya san yana bin ta ta samu hanyar dank'ara masa bak'ak'en maganganu wanda ba zai iya jurar jin su ba. Don shi mutum ne da baya son raini, don haka yake takatsantsan da duk abinda zai iya janyo masa raini. Musamman yau da yake jin zuciyarsa cike taf da bak'in ciki da wuya ya iya jure Kalma 'daya tak da zata b'ata masa rai.

Fareeda juyi kawai take akan tamfatsetsen gadonta da ya k'awatu da wasu irin shimfid'u na alfarma tsimayin jiran zuwan Hisham kawai take don a yarda ta lura yau kamar zai iya kusantarta tunda har ya ha'da jikinsa da nata kuma ta tabbata ya shak'i k'amshin sihirtacciyar humrar.
Sai dai har k'arfe 'dayan dare babu shi ba alamarsa har barci ya kwasheta cikin takaicinsa ta kuma ci alwashi a kansa matuk'a da gaske.

Tunda barcin ya 'dauketa sai k'arfe 8:00 na safe sannan ta farka. Da hanzari ta yi wanka ta shirya dalilin tana son zuwa gidan su gwara ta je ta zauna da mahaifiyarta su duba wacce zata fishshesu. Don ta sha alwashin kai sunansa wajen Malamin Mommynta kamar yarda tuntuni Mommynta take bata shawarar hakan ita kuma ta kafe akan ra'ayinta gani take zallar kyanta ya isa ya ja hankalinsa gareta.

Tana shiga 'dakin nasa ta ga fayau, har ya Riga ya fice kamar yarda ya saba ficewa da sassafe. Bak'in ciki kamar ya kashe ta. Da sauri ta shiga dialling numberrsa,  ringing biyu ya 'daga cikin karkasashi ya ce "My Madam how fa? Kin tashi kenan?"
Cikin masifa ta ce "Me ya dameka da tashi na? Ka ga Hisham gaskiya am tired n gaji da bak'in cikin da kake k'unsa min."

"Look Fareeda! Bana son jin kowacce banzar kalma daga bakinki zaman lafiya nake nema ni. Amma ke na lura baki da manner of speech kada ki manta am your Husband right?"

"Kai 'din ka sani ne? Ni fa bari ka ji na fa'da maka ba zan juri wulak'anci daga wajen 'da namiji ba..." Itama ta fa'da a hassale.
Hisham ya saki murmushi kafin ya ce "Ina jin ki, wulak'ancin me na miki?" Tsaki ta yi sosai wanda ya ji shi har tsakiyar kansa kafin ta ce "Wannene ma baka min ba."

Hisham ya saki murmushi kafin ya ce "Enough, idan na dawo ma yi maganar am little busy bye." D'id ya kashe wayar ya barta da waya a kunne zuciyatta na tafarfasa. Cikin takaici ta tura masa text

"Na wuce gida..."

"Kada ki je..." shima ya bata amsa a gajarce tana tsaki ta tura masa amsa "Wallahi sai na je." Ya dinga bin rubutun da kallo yana mamakin taurin kan Fareeda yarda ba'a isa a tank'wasa ta ba, baya son ta fita saboda baya son ta je ta jiyo labarin bai saki Saudat ba ya san akwai k'ura. Tana iya zuwa ta fa'dawa Mommynsa a zo a yi b'atacciya.

"Idan ki ka fita a bakin aurenki."

Fareeda ta dinga bin sak'on nasa da kallo tana ware ido kamar a mafarki wai ita namiji yake wa haka? Kuka ta saka sosai tana kiran Mommyn. Mommyn tana 'd'agawa ta sanar mata matsalarta ta ce "Bar ni da shi ba sai kin zo ba, Zan zo da kaina Fareedah, ki bar ni da shi dama akwai sak'on da nake son na kawo miki ki yi amfani da shi daga agadez aka kawo min." Cikin farin ciki ta ce "Thank you Mommy, Am waiting.." ta kashe wayar tana dariya ranta fari k'al tana da tabbacin ta samu Hisham ta gama.



***********

Saudat na zaune tana fifita gawayin da yake cikin kurfetin, so take ya kama ta yi ta 'dora sanwar abincin amma ya k'i kamawa saboda komai yinsa take a sanyaye, duk da kazar-kazar 'd'inta yanzu ta zama Salamatu.

Ummanta ta fito daga 'd'akinta sanye da hijabi, ta watsa mata kallo tana fa'din "Yanzu Saudatu har yau ba ki kai ga hura wutar nan ba, balle ki 'dora sanwar abincin nan kina nan kina aikin tunani?"

Saudat ta 'dan turo bakinta "Ni fa Umma ba tunani nake ba, hura wutar nake ke kan ki fa gawayin nan yana wahalar da ke fa."

Umma ta tab'e baki ta ce "Ke kika sani, kin ga ni na yi nan, ki yi dai da hanzari kada Abbanki ya 'debo rana da yunwa yazo ya tarar baki gama ba mashiririciya."

Daga haka ta saka kai zauren gidan sai dai da sauri ta dawo ganin mutane na shigo da kaya. Da sauri ta ce "Lafiya? Ko b'atan  kai kuka yi?" D'aya daga ciki ya ce "A'a nan aka ce mu kawo, ko ba nan ne gidansu Saudat ba?"

"Nan ne mana, ku shiga?" Cewar wata hakimar mace.

Umma Maryam ta bita da kallo, ta shaida ta Yayar Hajiya laraba ce, mahaifiyar Hisham, sai wasu su biyu da alama k'annenta ne, sai cika suke suna batsewa. Jikin Umma a sanyaye ta juya cikin gida hakan ya basu damar shigo da ragowar kayan. Su kuma matan Suka bi sahu suka shiga cikin gidan.

Tsaye suka yi suna bin gidan da wani banzan kallo suna tab'e baki. Umma Maryam ma tsaye kawai ta yi tana kallonsu ta kasa ce musu komai illa bin su da ido zuciyarta kamar ta dare don bak'in ciki.

Hajiyar ta juya ta kalleta, "To ga tsiyarku mun kawo muku, tunda ku ba ku da zuciyar da za ku je ku 'Debo kuna jiran a zo kome, abinda baku sani ba Hisham har abada ya rabu da y'ar ku don haka mu ka yi hob'b'asa mu muka hutar da ku muka kawo muku, dama don bak'in hali ko lefen ba ku kai mata ba ko kuwa shi kuka siyar ku ka mata kayan 'd'akin oho.. wannan dai ku kuka sani, hamdala ga Jallah da jininmu ya rabu da jinin tsiya. Umma ko 'a' kasa ce musu ta yi tsabar bak'in ciki, har Suka fice daga gidan . Turus ta bi garu ta zauna kawai ta runtse idonta. Saudat kuwa kuka ta saka sosai mai cin rai tausayin kanta da na iyayenta ya kamata. Tsawon lokaci Umman idonta a runtse kafin ta bu'de ta saukesu a cikin na Saudat. Har kallon ya 'dan firgita Sauda ta shiga rarraba ido.

"Kin gani ko Saudat? A haka Abbanki yake so na daina nuna tsanar Hisham a haka yake son na amincewa aurenku? Dubi fa wulak'ancin da suka mana?"

Saudat gum ta yi da bakinta ta kasa furta komai. Ita kanta yanzu ji take rabuwarta da Hisham shi yafi mata alheri kafin ta haifi yara su zama borori.

Sai yamma Abban ya dawo da yake ranar asabar ce akwai fasinjojin biki, ya 'dan zo da fara'arsa sai ya ci karo da kaya a zaure turus ya yi yana duban kayan, a tsakar gidan ma ya sake tarar da wasu. "Tab'd'jam kaya dai ya shaida su kayan Sauda ne, hakan yasa jikinsa ya yi sanyi duk wani karsashi da ya shigo da shi na samun yalwar ciniki tuni ya bi iska, jikinsa ya yi sanyi duk yarda ya so da mutuwar auren ashe ba abinda ya fi mutuwar auren y'arka ciwo? Ya zauna yana duban Umma.

"Maryama  wannan kayan wa ya kawo su? Ko ke ki ka yi gaban kan kika 'Debo su? Wato baki yarda da abinda na ce ba ko?"


Jikar Nashe.❤️❤️❤️😊🙏

Continue Reading

You'll Also Like

16.7K 881 32
DR UMAIMAH USMAN BULAMA,Mace yar kimanin shekara ishirin da tara , Babbar surgeon A asibitin CITY TEACHING HOSPITAL , Aure Uku, ƴaƴanta uku . Mace m...
2.3K 99 16
wannan sanyin illa zaiyi miki acancikin ki, ai ita mace da ɗumi aka santa, ai ballagaza ita ke illata ƙanta da ƙanta sai sanyi ya kamaki kizo kisani...
11.4K 1.5K 61
Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta cikin mummunar kaddara, irin kaddarar da b...
219K 16.1K 20
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...