Zumuncin Zamani

By Nazeefah381

7K 517 25

Labari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
11
12
13
14
15
16
17
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52

18

119 7 0
By Nazeefah381

Zumuncin Zamani

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

Not edited.

(Jazakillah Fad'ima Sabi'u Dankaka da ki ka yi jumurin typing book one Allah ya saka miki da mafificiyar aljanna ya alabarkaci rayuwar aurenki da tarin zuri'a masu alfanu.)

Mamaki ya kama Abba ya dubi Baffa Ya ce "Dama tare ku ke?" Baffa ya d'aga kai "Wallahi tare muke takanas ya je ya d'auko I mun zo gyaran zumuncin Allah." Umma tana masa sannu da zuwa kuwa ta juya ta d'auko musu ruwan randa mai sanyi, wanda pure water ne aka saka shi a randar. Abba ya mik'a musu ruwan. "Baffa ka sha ruwa kun d'auko hanya." "Bar ruwan nan Ka ji abinda yake tafe da ni ya fi shan ruwan." Abba ya girgiza kai "koma menene Baffa ka yi hak'uri ka sha ruwan za'a san Abin yi."
Baffa ya girgiza kai yace shi kenan ba a kin ta mutum ba ni ruwan na sha, umma ce ta dawo dauke da ruwa a kwanon sha ta ajiye masa ruwan sannan ta sake gaishe shi tana tambayar iInna Habi da Yara, "Duk suna lafiya" baffa ya amsa mata sannan ya dau kwanon ruwan ya kai bakinsa ya sha, ya ajiye ya dubi Abba mustapha yace ina jin ka mustapha,me yasa ka hana wannan yaron dan albarka auren yar wajen ka?"

Nan da nan Abba mustapha ya shiga zayyana wa baffa abubuwan da suke faruwa kafin ya gama baffa fuskarsa ta yi murtuk ya hau girgiza kai yana fadin, hukumullah la,ajaban. Sam banji dadi ba tabbas zuminci ya yi karanci,yanzu a dangin nan ace don Allah ya jarrabe kada rashin sai kowa ya juya maka baya har a dunga gudun hada zuri,a da kai? Ba komaii mustapha ka godewa Allah ya bakar ka da lafiya abin da nake so da kai ka dubi girman Allah ka kai zuciyar ka nesa,ita rayuwa duniya da kake ganin ta ba komai a cikinta sai rudani Kuma idan zaka yi abu kayi don Allah kada ka taba yin abu don mutane, don girman zatin Allah kayi hakuri ka ba Hisham auren yar nan don sadar da zuminci,ka san annabi ya umarce mu da sada shi Allah yana fushi da mai yanke shi. Ka dubi girman Allah ka bashi tunda dai shi ka tabbatar ba shi da wani Hali da za a guji hada aure da shi da fatan zaka yimin wannan alfarmar ka san dai ban taba Neman alfarma a gurinka ba.

Abba mustapha ya yi kasa da kai yace baffa ka daina roko na na amince na ba shi auren saudat, Allah ubangiji ya sa hakan shine mafi alkairi.
Cikin farin cikin baffa yace to na gode mustapha lallai na amince yau uba ka dauke ni ashe kuma bayan gobarar nan nan aka dawo.
Abba yace wallahi kuwa baffa,naso zuwa na gaya maka to Al,amura ne sai a hankali,rasa mafita na yi na sayar da nawa gidan,na sai adaidaita sahu biyu, sa'eed na jan daya ni kuma ina jan daya.
Baffa cikin matukar tausayawa ya girgiza kai yace humullah la,ajaban to ubangiji Allah yasa hakan shine mafi alkairi kayi hakuri mustapha wannan abin duk mai wucewa ne wata rana sai labari
Abba mustapha yace haka ne sanan ya kalli Hisham yace to Hisham,hankalinka sai ya kwanta na amince maka auren sauda
Hisham ya sunkuyar da kai yana murmushi
Daidai lokacin sauda ta shigo gidan dawowarta daga makaranta magariba kenan, durkusawa ta yi sosai ta gaida baffa cikin murmushi yace amaryar Kenna
Bata kawo komai a ranta ba ta shige daki Tun da safe da ta tashi ta yi wanke_wanke gabanta yake faduwa sosai, ta rasa dalilin,har ta gama wanke _ wanken kafin ummanta ta dan dube ta tace sauda sana,a nake so na fara amman na rasa me zan dunga sayarwa
Sauda ta dan yi jim kafin tace duk layin nan umma babu mai awara da safe ina ga ita za ki dinga yi,
Umma ta daga Kai tace haka ne, ke ma kin ce wani abu bari abbanku ya dawo na sanar dashi idan ya amince shi kenan sai na fara don gashi bikinki ya matso tunda sunce jibi xaa kawo kudin aure.
Da sauri sauda ta dago kai tace biki kuma umma.

Umma ta dan saki fuska tace to ya zaayi sauda kana taka ne Allah yana yasa abbanki ya amince wa Hisham aurenki saboda takanas ya dauko baffan wudil,kuma ba komai yaron nan Hisham ya cancani a bashi aurenki don ya yi mana halacci,ke kanki kin sani sai dai ki bawa wani labari don haka don Allah kada ki sa komai a ranki ki yi addaua Allah yasa hakan ya zamo alkairii a rayuwarki...
Turus sauda tayi,hawaye male_male a fuskarta yanzu shi kenan ta tabbata Hisham zata aura? Ta sani shi kenan tayi sallama da farin ciki a rayuwarta matukar ta shiga cikin danginsu inda ba a son su ba a san darajar da kimarsu ba.

Umma ta xuba mata ido ita kanta tana tausayawa yarta tata sai dai babu yadda za tayi ba kuma abinda za tayi mata da ya wuce ta bita da addaua kiyi shiru sauda inshallah hakan alheri zai zamo miki.
Sauda mikewa kawai ta yi ta shige daki,duk da zuciyar ta tana son Hisham amman sam ba ta burin aurensa.


Senator sule Jami,I ya dubi Hisham bayan ya gama koro masa jawabin yadda suka yi da Abba mustapha sannan yace to Alhamdulillah,abu ya yi kyau zan sanar da mahaifanka a kai kudin aure gobe ba na so kai ka yi masa magana ka barni da shi.
Hisham ya rusunar dakai Yana zuba godiya.
Senator ya dafa bayansa yace kada ka damu Hisham ni da na dauke ka, don haka ka godewa Allah kawai

Hisham ya mike yana yi masa sallama,daga haka senator ya dau wayar sa ya danna kira alhaji hamxa.
Bugu daya ya dauka tamkar wanda yake Jira,bayan gaisuwa a tsakaninsu senator yace yana son ganin sa alhaji hamza bai dauki wani dogon lokaci ba ya bayyana a office din sule Jami,I
Senator ya dubi shi fuskarsa babu alamar wasa yace Hamza an gama da maganar mustapha,ya amince da bawa Hisham auren yarsa......
Hamza da sauri ya ce ba dole ya amince ba,tunda mu zai mora.
Dakata!!! a fusace senator ya dakatar dashi ba wannan maganar ce ta sani na kira kaba maganar aure nan da wata daya tana nan babu fashi,don haka a gobe nake so ka aika a kai kudin neman auren zuminci Allah ne idan kaga dama ka rike shi kai ka sani idan ba ka rike ba kai da Allah aure ne dai babu fashi kaji ni da kyau.

Alhaji hamza shi ma ya dan hade rai yace shi kenan Àllàh ya kaimu goben A zuciyarsa yace ya fara gajiya da wannan mulkin mallakar na sule Jami,I tamkar wani ubansa,amman akwai lokaci

Daga nan alhaji hamxa gidan kaninsa lawal ya tafi don ya sanar dashi yaci saa kuwa ya same shi a gida bayan doguwar gaisuwa alhji hamza yace lawal gobe za ka kai kudin auren Hisham.
Alhaji lawal ya dago kai yace ban gane ba yaya banda wanda aka Kai?
Alhji hamza ya yi tsaki kai dai bar Hisham da shegen jajibe _jajibe wai yar gidan mustapha zai hada ya aura ita da yar wajen honorable din

Alhaji lawal ya zaro ido Yana kallon alhaji hamxa yace wane ne mustapha kuwa? Shi Kuma Hisham ina zai Kai mata biyu a lokaci dan hadama?

Kai ma dai ka fada,babu yadda ba muyi da yaron nan ba sam ya kekashe kasa ka rabu da shi wanda bai ji bari ba ai bazai ji hoho, kafirin taurin kai ne dashi wai yar gidan mustapha namu yake so
Alhji lawal ya sake zaro ido yace kai haba yaya kai Kuma kana ne ka amince masa siyan tsiya da kudinsa?

Alhji hamza ya sake zabga tsaki yace barshi kawai har hadi ni yayi da honourable shi kuma ya rantse idan ban amince ya aure su biyu bato shima ya fasa ba da yarsa, don dole na amince amman a zuciyar ta fa akwai wani kuduri na daban, na amince ne ya aure ta bayan auren kawaii sai na saka ya sake ta,ta dole Kuma tun kafin ya shafo mun tsiya, don haka yanzu na yi wa adamu waya ga #20000 a kai kudin auren.

Alhaji lawal yace shi kenan ka dai yi kokarin raba su tun kafin ya goga maka tsiya,ana murna ya taso da kashin arxiki zai jinginu da masu kashin tsiya, bar ni da shi na san maganinsa alhaji Hamza ya fada yana sake girgiza Kai.


Sauda a hankali ta amsa kiran umma,ta fito daga daki duk wannan kazar_ kazar din babu shi idonta kozai _ kozai alamar taci kuka ta koshi
Umma ta dube ta tadan bata rai, yanzu sauda haka da kike yi fisabillahi ya dace duk kinbi kin kwarzabi kanki a kan karamar matsala? Sai kin janyo wa kanki cuta? Ai shi kenan,kiyi ta yi idan kina ganin hakan ya fimiki, ki wuce kije Hisham ne ya Aiko yana kiranki, saura kije ki nuna masa bakin rai. Umman ta fada tana shigewa daki.

Saudat bata yi jinkirin fita ba saboda ta lura umman ta dau xafi da yawa.
Yana cikin motar sa,don haka ta ja ta tsaya a kofar gidan, fuskarsa ta a hade, kasancewar da wuta hakan yasa Hisham ya gano ta, murmushi ya saki ya fito daga motar dan ya san Mulki ne ya motsa mata kenan Hisham sai lallashin.
Yana Isa gabanta ya hau leken fuskarta yana sakin murmushi yace ran gimbiya ya dade,ba a yi farin cikin da gani na bane.
Kicin_ kicin ta sake yi da ranta tace ya zaayi na yi farin cikin da ganin ka bayan kana shirin rusa min nawa farin cikin?
Hisham ya nuna kansa yace NI SAUDA "
Ta murtuke fuska hade da fadin kai din y Hisham dan Allah ka janye daga maganar neman aurena!!!

Ni gaskiyah baxan iya ba,sauda Naga samu naga Rashi ya fada yana kwaiwakyon salon muryarta.
Hakan yaja sauda ta saki murmushi, don kam ya bata dariya, Shima murmushi ya sake kafin yace koke fa my angel har na ji Dadi.don Allah ki zo mu shiga mota akwaii maganar da zamu tattauna.
Sauda ta makale kafada ka fadi maganar ka kawai anan ina jinka..
Ya zuba mata ido yanzu sauda ba zan nemi alfarma ki yimin ba? Shi kenan many thanks to you daga haka ya juya.
Tunanin tayi sam ba ta kyauta ba, don haka tabi shi.

Har ya shiga motar ita ma ta bude murfin motar ta shiga ya dan dade bai juyo ya kalle ta ba,sai can ya juyo ya kura mata ido tsawon mintuna har sauda din ta dan tsargu ta sunkuyar da kanta sai can ya ja ajiyar xuciya ya ce ina murna sauda na kusa mallakar ki a matsayin matata,sai Kuma ki nuna min ke ba ki so hakan ba? Sauda kin san wahalar dana sha kuwa kafin a amince min auranki amman kiri kiri ki nuna min ke baki so ba, kin kyauta kenan?

A hankali ta dago ta kalle shi, gabadaya sai ta ji ya bata tausayi,ta tabbatar Kuma ba ta kyauta ba, Hisham mutum ne da ya cancanci a soshi ko ba komai a kafatanin masu kudin danginsu shi kadai ne ya ba su kulawa,ba kyamace suba,duk da takaucinsu idan yazo gidansu abincin da suka ci shi yake ci, ruwan da suka sha shi yake sha, mutumin da ya yi maka haka anya ya kyautu kayi masa butulci? Ta tabbatar ba laifinsa ba ne na iyayensa ne, Kuma ko ba komai ta tabbata tana son Hisham,son da ya tsaga kashin ta yake zagaya wa cikin jininta.
 
Ta lumshe Ido ta bude tar sai taga su akan Hisham ta san saki murya tace y Hisham ka yi hakuri don Allah. Ba wai.bana farin ciki bane,ina tunanin rayuwar da zan fada ne har ga Allah,amman ya wuce kawai ka yi hakuri.
Sai a lolacin Hisham ya saki murmushi Yana leken fuskarta,yace sauda,kalle ni
Sam kasa kallon sa tayi I
Ina so ki sani,ni zaki aura ba dangina ba,kuma na yi miki alkwari duk rintsi duk wuya, babu abinda zai sa na juya miki baya!!!

Sauda ta saki murmushi tace ni ma nayi maka alkawarin kyautatae maka fiye da zaton ka, fatana daya ka bani gamsasshiyar kulawa.
Bayan hakan bai dade ba yayi mata sallama tare da alkawarin kashegari zaizo da yammah su tattauna tsare tsaren bikin mu!!!

Koda ta koma gida dakinta ta shige,sai a lokacin take jin tsananin farin cikin na samun damar mallakar burin ranta. Tana son Hisham son da sam baya misaltuwa.ta rintse ido tana tunanin ta kusa amarcewa da mijinta tunanin ta,ya tsaya cak da ta hasasho waye zai mata kayan daki, kasancewar ta sani iyayenta basu da shi kuma basu bawa kowa ajiya ba,gashi biki wata daya zaa saka.!!ta lumshe ido a hankali ta furta Allah ka fitar damu daga wannan bakin talaucin ta sani Allah Mai jibintar lamarin mutane ne, ubangiji ka jibinci Al,amuranmu.

A kashe gari umman sauda ta fara awarar siyarwa duk da ba son ran Abban sauda ta fara ba, ta bashi hakuri hade da sanar da shi alfanun haka,ga misali zaa gayyace ta biki,zata so ta mikawa uwar bikin dan hasafi yara xasu ziyarce ta, akwai bukatar ta basu kudin mota don haka a nata hasashen sana,a ta zama dole,saboda kuwa duk wadatar mijinka akwaii lokacin da zai gaji da bani bani idan kuwa kina sanaar kin wuce wulakanci namiji komai shine balle marar shii

Sauda dinma da wuri ta tashi kasancewar lahadi ce ba ta da lecture, ita ce take suyar awara a soron gidan.karfe9:00 na safe ta ji tsayuwar mota a kofar lungunsu ba tayi kokarin mikewa ba, don daman hijabintaa a jikin ta,tana jin muryar sallamar ta tabbatar b.lawal ne kanin mahaifinta ilai kuwa tana daga Kai ya sakar mata wani mugun kallo ya tabe baki yace ke kuma me kike wanann tallah, shi kuwa Hisham a hakan yake son ki

Sauda ta sake sunkuyar dakai kawai ta yi abin kam yayi mata ciwo ba ta gama sanye wanan bakin cikin ba b amadu yace " ba shi ya jiyo ba tunda an gaya masa ya kiji,sai a rabu dashi wanda baiji bari ba ai bazai ji hoho ki shiga kiyi mana sallama da mustaphan.

Ta wuce tana jin lokacin da suke cewa lallai tsiya takai tsiya ko yaushe ya dawo wannan kwarabebben gidan? Allah yq kyauta
Jikinta a salube ta shiga gidan tana kokarin goge kwallar da take kokarin zubo mata. Ta dubi umma tace wai su b lawal suna sallama da Abba.
Umma ta mike tana cewa" to bari na gaya masa kin gama awarar ne?
Ta kare!! Kawai tace, tana shigewa daki, kuka ne ya kwace mata sosai ta kunshe bakinta cikin matukar bakin cikin ba ta son umman ta taji kukan.

Abbanta yafito yana fadin oh yanzu don bani da shi a rasa mai karbar kudin auren yata duk a dangin sai ni da kaina.
Umma tace,kayya malam, Kai ma ka sam ba za su karba ba,don kawai basai don kada a dora musu wahala
Abba yace ai shikenn ya sa Kai yaefice daga gidan

A tsaye ya gansu gabadaya cirko_ cirko nan ya dan saki fuska yana cewa,sannunku da xuwa ya fada yana shimfida musu tabarma.
Babu wanda ya amsa har suka zauna Abba ya sake cewa muntashi lafiya alhaji lawal?

Duk da yake kaninsa yayi kokarin daraja shi don daga shi har amadu ya girme musu sosaii lawal fuskarsa a gimtse yace mustapha dama ba wani abu ya kawo muba sai don kawo kudin auren yarka" tare da sanar da kai an yanke biki nan da wata daya,kuma shi Yaya hamza yace a sanar da kai baya bukatar a Kara lokaci.
Mamakine ya kama Abba sabida kiransa da mustapha gatsal da ya yi, amman ya kira Hamza da Yaya hamzaa duk da shi din ya girmi hamza tsaf ya Shanye mamakin sa yace ubangiji ya kai mu

To Fa!

Continue Reading

You'll Also Like

Gentle touch By K

General Fiction

48.9K 1.1K 32
It had been mere months after her eighteen birthday, when she was pulled from the safe haven of her life and forced into the fantasy the women had cr...
3K 213 22
Tunaninta da duk wata nutsuwarta sun ta'allaƙa ne akan abinda takewa kallo a matsayin MURADIN RANTA, Sedai saɓanin zuciyar ABOU HATEEM wadda take a...
136K 9.6K 16
in which a boy leaves small notes on a girl's desk because he's too shy to actually talk to her in person
219K 16.2K 20
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...