Zumuncin Zamani

By Nazeefah381

7K 517 25

Labari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
11
12
13
14
15
16
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52

17

124 8 0
By Nazeefah381

Zumuncin Zamani.

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

(Typing: Fad'ima Sabi'u D'ankaka. Allah ya raya mana Meenah Yasa musulunci ya yi alfahari da ita.)

Ko da asuba Yan'uwansa da suka tashi ba su ganshi ba Basu kawo komaii a ransu ba, saboda sun san shi da hanzarin tafiya masallaci don haka Abban yace yanzu haka ya tafi masallaci,malam Khalil kenan, akwai ibadah sosai zuciyarsa ta d'anfaru da son addini don duk ya fi ku." Babu Wanda ya ja da zancen Abba murmushi kawai su ka yi, don sun San gaskiya ya fad'a.

Hankalinsu bai fara tashi ba sai da 12:00 na rana ta yi ba khalil babu dalilinsa, don haka Abban ya d'an tashi hankalinsa don yasan Khalil din bai tab'a aikata haka ba, ya kira mahamud yace maza mu fita neman sa ko ma ina yake don Khalil bai tab'a aikata haka ba." sa'eed ne ya fito daga d'akin su a guje yana hawaye ya ce "Abba Y.Khalil guduwa ya yi ka ga takardar na ganii ina shara.
Abba hannunsa na rawa ya karb'a,ya fara karantawa, shi ma hawaye ne ya fara suntiri a fuskarsa su Saudat da Umma sak suka yi suna son su ji me Abban zai ce.
Yana gama karantawa ya goge k'wallar idanunsa ya kalli umma ya ce khalil ya ce ki yafe masa ya kasa jurewa ya tafi nema.
Saudat kuka ta saka ita ma haka umma.
Abba yace ku yi masa addu'a don Allah ku daina kuka, Allah ya kare min khalil a duk inda yake, ubangiji ka bashi sa'a a kan duk abinda yake nemaa Allah kada ka nufe shi da aikata mummunarsana'a, fashi,mafiya, ta'addanci zamba cikin aminci, ubangiji ka kare min Shi."
Umma ameen kawaii take cewa, hawaye yana bin fuskar ta ce na yafe maka Khalil, daman ba ka yi min komai ba, Allah yasa wa  abinda duk zaka je nema albarka." Saudat kuka take sosai, ita ma da nata burin a ranta.

*******

Babu inda Hisham ya yanke sawarar su had'u sai a makaranta, ya san tana da lecture yau don tunda yake kai ta makaranta ya samu time table dinsu
A jikin wata bishiya ya yi parking zuciyarsa nata bugawa don gani yake saudat d'in sam ba za ta saurare shi ba, Yana d'aga kansa kuwa bayan an fito daga lecture din ya hango ta cikin nutsuwa take tafiya, da sauri ya fito daga mota nan da nan idon y'an matan Jami'a ya fad'a Kansa,  sai dai sam Hisham bai lura da su ba, har sai da ya je gaban Saudat ya tsaya Yana ta zabga mata murmushi.
Saudat ta gimtse fuskarta don sam yanzu ba ta son alak'anta da shi . Tana son sa amman ba za ta iya aurensa ba saboda tana gudun tijara da wula'kancin danginsu.
Hisham ya zuba mata Ido ganin sam ba ta yi murna da ganin sa ba yace "My Angel lafiya? ko ba ki yi murnada ganina ba?"
Ta sake had'e rai sosai ta ce "Y.Hisham ina son gaskiya alak'armu ta tsaya daga nan saboda sam had'inmu da kai ba Zai tab'a yiwuwa ba, ni ma yanzu na yi nazarin haka, kowa ya tsaya a inda Allah ya ajiye shi."

Hisham ya k'ura mata ido zuciyar sa na zafi ya ce "Sauda kada ki yi min haka, na samu na shawo kan kowacce matsala sannan yanzu ki sake zuwa min da wata har kike cewa kowa ya tsaya a matsayin sa? Don Allah saudat kada ki k'ara min zafi."
D'aga masa hannu ta sake yi cikin zafin rai ta ce," Y. Hisham ka k'yale ni kaje ka auri zab'i n iyayanka ni ma zan nemi daidai da ni takala d'anuwana na aura"

Shiru Hisham ya yi mata yana mata kallon mamaki da jin furucin da yake fitowa daga bakinta Yana kallo har ta b'ace masa amman ya kasa katabus zuciyarsa ce take masa wani irin k'una, ko a mota ya dad'e shiru yana tunani,da kyar ya ja motar ya wuce.
Gidan su saudat d'in ya tafi ya sake dosar Abba da zancen.
Har cikin tsakar gidan ya shiga ya tarar da umma zaune ta zuba uban tagumi don tunda Khalil ya bar gidan ta rasa sukunin zuciyar ta, da sallamarsa ya shigaa umma ta d'ago kai cikin sakin fuska ta ce "A'a Hisham ne" shi d'in ma cikin murmushi yake ya ce Wallah Umma ya sake bin gidan da kallo yana sake jin rad'ad'i a  ransa.
Umma ta mik'e ta shimfid'a masa tabarma yana zama ya gaishe ta ta amsa cike da kulawa, sannan ta ce "Dafatan lafiya ko?"
Ya d'an rusunar da kai kafin ya ce  lafiya umma Abba yana nan ne?"
Umma ta girgiza kai kafin ta ce yanzu ya fita ina jin ya biya d'auko Sauda ka san yanzu adaidaita sahu yake ja"
Da sauri Hisham ya d'aga kai adaidaita sahu ummah?  Ido yana kawo ruwa ya fad'a. Umma ta ce  "To ya za'a yi Hisham, rayuwar kenan,duk ta yadda tazo wa mutum ya karb'e ta kawai mun gode wa Allah ma da ya bar mu da rai da lafiya wasu ma suna can cikin rashi Kuma ba su da lafiya ba magani babu abinci, su kuma su ce me Hisham?" Cire hularsa ya yi yana goge zufar da take keto masa daidai lokacin Abba mustapha ya shigo sanye da rigarsa ta shadda tsaf da shi mutum mai kamala, Saudat ce a bayansa,tana ganin Hisham ta tsuke fuskarta tsaf ta yi wa ummn sannu da gida, ta d'an kallo Hisham ta gaishe shi.
K'ura mata ido kawai ya yi ba tare da ya amsa ba.
Saudat ta shige d'aki ranta fal k'unci ita kam yanzu sam babu burin aure a ranta, burinta ta yi karatu mai tsayi yadda zata tallafi iyayenta.
Abba ya gyara zamansa sosai yace Hisham d'an albarka yau Kuma ranar aiki na ganka da rana haka?"
Hisham cikin sanyin jiki yace "Abba  ina wuni?"
Abba ya ce "Lafiya lau Hisham ya na ganka haka in ce dai lafiya ?" dariya umma ta yi tace ka ganshi Nan tunda nace masa kana jan adaidaita sahu yake Hawaye."

Abba yayi murmushin yace Hisham kenan to mutum ya ya iya da kudurar ubangiji, kullum ina gaya maka rayuwa duniyar haka ta gada SAMU da  RASHI don haka kada ka sawa kanka damuwa wata rana sai labari.
Hisham ya girgiza kai gaskiya Abba  ba zan iya barin ku a wannnan halin ba"
"Ni kuwa Hisham ba zan iya karb'ar naira biyar a hannunka ba saboda ina son in nuna wa mahaifinka ba sai da kai zamu rayu ba,bakin da Allah ya tsaga ba ya hana shi abinci. Ba wai ina gwasale taimakon da kake son yimin bane a,a ina yabawa da k'ok'arin ka kawai, kuma ko bayan idonka ina fada kai mai kaunar mune, don haka ka saka a ranka har abada ba zan manta da tarin kulawar da ka bamu ba. Yanzu ka share hawayenka ina son in san me yake tafe da kai"
Hisham ya d'auke k'wallar da take idonsa sananan ya rattabawa Abba mustapha yadda suka yi da senator

Shiru Abban saudat yayi cikin juyayin abinda zai gayawa Hisham,da nauyi ya dubi idonsa ya sanar dashi ba zai bashi y'arsa ba, duk da tarin kulawar da yake ba su, amman ya zama dole ya sanar da shi don bazai iya ba shi sauda ba. kansa ya dade a k'asa kafin ya d'ago yace Hisham ba wai zan hana ka auren saudat ba ne a son raina,sai dai dalilina mai k'arfi na bana son sauda ta yi rayuwar rashin y'anci,kai kanka ka sani ba mu da farin jini a danginmu, don Allah don annabi inaso kayi hakuri ka janye son auren saudat a ranka, hakan shine farin cikinmu,kai ma kuma farin cikinka,ba zai zame maka alheri ba kai ma,tunda mahaifinka baya so, sannan gaskiya ba na so sauda ta yi kishi da y'ar mai kud'i ko ba komai mata akwai gore gore.
Tsit Hisham ya yi yana sauraren maganar Abba don gaskiya ya san gaskiya ya fad'a,amman sam ya san zuciyar sa ba za ta iya hak'ucewa auren Sauda ba.
A hankali ya d'ago Kai ya kalli Abban sai dai ya lura sam ba maganar wasa a tare da abban yanzu ba zai saurare shi ba,
don haka jikinsa a salub'e ya mik'e ya ce "shikkenan Abba nagode sai anjima.
Abba ya bi Hisham da kallo, shi kansa ya san bai kyauta ba,bai kuma yiwa Hisham adalci ba, saii dai a nasa hasashen ya tabbatar hakan da ya yi shine masalaha.
Senator sule Jami,I fuskarsa a d'aure ya sake duban y'ar tasa yace tilas ki aure shi wallahi tunda zab'nki ne ba wani ba ne ya zab'o miki shi, kuma kin sani bana magana biyu."

Fareeda ta d'ago kai cikin shagwab'a tace Abba mu biyu fa ya ce zai aura.....
Abban tsaki ya ce to shine mai akanki aka fara kishiya? Gidan mu nawa kika gani ina ce babata ita ce ta hudu, wannan ma ai shirme ne kishirya kike tsoro? To kunyi agreement da Allah ne a kan ke kadai zaki zauna?"
Fareeda ta girgiza Kai
Senator sule ya ce don haka wallahi ki kiyaye ni, aure kamar an yi na angama, kuma taren Zai had'a ku, tashi ki bani wuri.
Ya juyo ga hajiya sa'a ya nuna ta da yatsa,ke Kuma ki kiyayeni, wallahi don na san tabbas ke kike zuga ta....
Ni kuma alhaji

"Ke d'in.... Har wata mutuniyar arziki ce da za ki kasa zuga ta to wallahi ki kiyaye ni, har kina ikrarin tunda ba ki zauna da kishiya ba y'arki ba za ta zauna da ita ba, to ke ma kwanan nan zan miki sai na ga k'aryar cika baki."
Tsit hajiya ta yi zuciyar ta na bugawa a zuciyar ta tana neman tsari da kishiya, tayi rau_rau  da ido tana duban senator, ta ce "Don
Allah kayi hak'uri na ga ranka ya b'aci sosai amman ni wallahi ba ni na zuga ta ba"
Alhaji sule ya yi tsaki yace "hak'uri na d'aya ki sa y'arki ta janye k'udirinta ta amince da auren nan idan ba haka ba wallahi ni gaba d'aya zaku sha mamakina." daga haka ya mik'e ya fice.
Hajiya ta saki ajiyar zuciya , bayan tabi bayansa da kallo sosai take shakkar mijin nata don tasan shi kaifi d'aya ne, Amman kuwa sai ta ci mutuncin hajiya laraba don ita duk ta jawo mata take ta ji ta sake tsanar auren, Amman ba komai haka zata sake lallabar y'arta ta aure shi, in yaso daga baya sa san abin yi.

A d'aki ta sami fareeda a kwance ta zabga uban tagumi, ba komai yake b'ata mata rai ba sai tunanin wai ita ce zata zauna da kishiya bayan cika bakin da take yi a makaranta na ba za ta yarda ta zauna da kishiya ba, yanzu ta san k'awayenta dariya za suyi mata, wananan ne yake b'ata mata rai don so kam tana yiwa Hisham,son da ita kanta ba ta san yawansa ba.
Hajiya sa'a ta dad'e akanta a tsaye amma ba ta sani ba saboda yar tata ta lula tunani,sai da ta d'aga k'afarta sanann ta yi firgigit ta d'ago,hajiya sa'a cikin kulawa tace fareeda tunanin me kike haka?
Cikin hawaye da shagwaba fareeda ta ce yanzu mummy kina kallo zai had'a mu mu biyu ya aura?"

Hajiya sa'a ta girgiza kai tace fareeda hak'uri za ki yi kinga mahaifinki ya d'au zafi ki yi hak'uri ki aureshi daga baya za mu san yarda za'a yi.."



______Awa daya Hisham ya yi a hanya ya isa garin wudil d'in, Allah ya sa yakan ziyarci baffan wulid d'in,yau kam da ya sha kunya. Yana  parking ya samu yaro ya turo shi cikin gidan don ya yi masa iso.
Yaron bai dawo ba sai da dattijon arziki, yana ganin Hisham ya saki fara'a yana fad'in AA Hisham kai ne da yammah nan? To ka k'araso daga ciki sai kace wani bak'o? Hisham d'in  ya bi bayansa suka isa cikin gidan Inna  Habi matar baffan da sauri ta shimfid'a masa tabarmar kaba "kai kuma da yamman nan in ce ko dai soyayyar tawa ce ta motso maka."
Hisham murmushi kawai ya saki don shi sam bai iya wannan wasan ba.
Ya zauna sosai a kan tabarmar sannan ya gaishe da su duka suka amasa cike da walwala,baffan wudil yace Hisham lafiya kuwa naga baka saba zuwa a wannnan lokacin ba, ka fi zuwa da azimi, sallah babba da mauludi haka ne?  Hisham ya d'an  d'aga kai baffa dama wata matsala ce tafe da ni.

Baffan ya gyara zama yace ina sauraron ka Allah yasa zan iya magance ta don na lura yanzu y'an uwanku sun zama masu zumuncin zamani ba sa jin maganar talaka komaii girmansa sai ta mai kud'i, yanzu duk yawan dangin nan rabon da in ga an tako nan gaisheni  har na manta, sai ko idan ni na matsu naje gaishe su, Shima ba za'ayi min tarbar arziki bq duk a dalilin ni ba mai hali bane a matsayina na k'anin mahaifinsu,idan suna da hangen nesa ai sa so su gaisheni daga kai sai mustapha ne zance kun rike ni mutum don kam mustapha yana zuwa a kai Akai......

Hisham ya gyad'a kai yace hak'uri za kayi baffa, abin da ka fad'a haka yake wallahi abin sake tab'arb'arewa yake a kullum, yanzu ma abin da yake tafe da ni kenan" ya shigaa ba baffa labari.
Baffa tsit yayi bayan ya gama saurara,.kafin ya ce hmmn hukumullahi la,ajaban, abin ya zo da sauk'i tunda matsalar akan mustapha ne, na san mahaifi ya d'auke ni ina gaya masa kuma zaiji Allah ya sa wannnan auren naku ya zama sillar shiryuwar zumuncin dangin nan, don kam ina tunanin yarda zan mutu na bar dangin nan cikin tab'arb'arewar zumunci. Kullum addu'ata Allah ya daidaita lamarin.
Hisham ya ce amin baffa.
Baffa ya mik'e bara na zo yanzu sai mu wuce na je na samu mustapha, gobe inshallah sai na dawo."
Daga haka ya shige d'aki, lokaci kad'an ya fito yana kallon habi yace bara muje gyaran zumincin Allah."
Inna habi tace Allah ya sa a dace malam
Hisham ya yi mata sallama suka fice daga gidan.
Hisham bai tsaya a ko,ina ba sai kofar gidan Abba mustapha,baffa ya dube shi don son karin bayani yace nan mustapha ya dawo kuma?
Hisham yace nan ya dawo baffa
Baffa ya fito cikin sanyin jiki da tausayin halin da ya tarar da mustapha fada yake yi Yana hukumullahi la,ajaban.... Yana sake tausaya masa shi kuma mustapha tasa kaddarar kenan? Daga wannan sai wannnan? tabbas yana cikin jarrabawar ubangiji,sai dai Allah ya basu ikon cinye jarrabawar.
Da sallama suka shigaa gidan Abba mustapha,jin muryar baffa yasa Abban sauda saurin fitowa daga d'aki,yana cewa baffa Kaine da magaribar nan?
Ita kuwa umma sai k'ok'arin shimfid'a tabarma take. Baffa ya zauna sai a lokacin Abba ya lura da Hisham a lokacin ya sha jinin jikinsa sai dai ya basar yace A,a Hisham ko tare kuke ne?
Baffa yace ai shi ya d'auko ni takanas ta kano banji dadin abinda ka yi ba mustapha.
Abba mustapha yace baffa ka bari ka sha ko ruwa ne sai mu tattauna......

Awa daya Hisham ya yi a hanya ya isa garin wudil din, Allah ya sa yakan ziyarci baffan wulid din, yau kam daya sha kunya,yana packing ya samu yaro ya turo shi cikin gidan don ya yi masa iso.
Yaron bai dawo ba sai da dattijo arziki,yana ganin Hisham ya saki fara,a yana fadin AA Hisham kai ne da yammah nan? To ka karaso daga ciki sai kace wani bako? Hisham din ya bi bayansa suka isa cikin gidan inna habi matar baffan da sauri ta shimfida masa tabarmasa kaba kai kuma da yammah nan in ce ko dai soyayyah tawa ce ta motso maka.
Hisham murmushi kawai ya saki don shi sam bai iya wannan wasan ba.
Ya xauna sosai a kan tabarmar sananan ya gaishe da su duka suka amasa cike da walwala,baffan wudil yace Hisham lafiya kuwa naga baka saba zuwa a wannnan lokacin ba,kafin zuwa da axumi, salla babba da mauludi haka ne?  Hisham ya dan daga kai baffa dama wata matsala ce tafe da ni.

Baffan ya gyara zama yace ina sauraron ka Allah yasa zan iya magance ta don na lura yanzu yanuwanku sun zama nasu zuminci zamani ba sa jin maganar talaka komaii girmansa sai ta mai kudi, yanzu duk dangin nan rabon da in ga an tako nan gaisheni shi har na manta,sai ko idan ni na matsu naje gaishe su, Shima ba zaayi min tarbar arxiki bq duk a dalilin ni bamai hali bane a matsayina na kanin mahaifinsu,idan suna da hangen nesa ai sa so su gaisheni daga kai sai mustapha ne zance kun rike ni mutum don kam mustapha yana zuwa a kai Akai......

Hisham ya gyada kai yace hakuri za kayi baffa, abin da ka fada haka yak, wallahi abin sake tabarbarewa yake a kullum yanzu ma abin da yake tafe da ni nan ya shigaa ba baffa labari.
Baffa tsit yayi bayan ya gama saurara,.kafin ya ce hammm hukumullahi la,ajaban, abin ya zo da sauki tunda matsalar akan mustapha ne, na san mahaifi ya dauke ni ina gaya masa kuma zaiji Allah ya sa wannnan auren naku ya zama sillar shiryuwar zuminci dangin nan.
Hisham yace amin baffa.
Baffa ya.mike bara na zo yanzu sai mu wuce na je nasamu mustapha,gobe inshallah sai na dawo.
Daga haka ya shige daki, lokaci kadan ya fito yana kallon habi yace bara muje gyaran zuminci Allah.

08033748387

Continue Reading

You'll Also Like

205K 7K 66
When Thea Nightingale enters her senior year she didn't expect to see the boy who had died over a month ago in the same room as her, also the hatred...
77.4K 3.5K 32
labarin BURINA labarin Zainab (Zee) da Khalil ( IK) da Abdallah (Alhaji) labarin soyayya ban tausayi da nishaɗi.
Gentle touch By K

General Fiction

49K 1.1K 32
It had been mere months after her eighteen birthday, when she was pulled from the safe haven of her life and forced into the fantasy the women had cr...
2.9K 387 31
Fyaɗe aka yi miki. Shi ne abinda zuciyarta ke ƙara nanatawa. Ban san waye ba, ban kuma san dalilinsa na aikata haka a gareni ba, ni a sanina bani...