Zumuncin Zamani

By Nazeefah381

7K 517 25

Labari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
11
12
13
14
15
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52

16

113 8 0
By Nazeefah381

Zumuncin Zamani..

Na

Nazeefah Sabo Nashe ✍🏽✍🏽

(Typing: Fad'ima Sab'iu D'ankaka. Ubangiji Allah ya d'aukaka darajarki har a
Aljanna.)

08033748387.


A haka Alhaji sule jami'i mutum ne nagari Mai nagartacciyar zuciya, sab'anin matarsa da ita sam ba ta son abin da yake yi tafi son kullum ya yi ta bauta wa danginta babu wajen malamin da ba ta Kai sunansa ba, amma sam ba ta samu sa'a ba, a wannan b'angaren.ta dai yi nasarar hana shi aure, don haka ba ta damu sosai ba, ta sani idan ya mutu babu mai gadon sa daga ita sai ya'y'anta biyu maza da auta fareeda, sai yayyenta Aslam da Akbar.
Koda ya shiga gidansa senator sule Jami'i fuskarsa a d'an  had'e ya dubi madam d'insa yana cewa turo min fareeda.

Da hanzari ta mik'e don duk abinta tana shakkarsa a wasu lokutan, har d'aki ta samu Fareeda tana sanar mata kiran mahaifinta, "saura idan kin je ya tambayeki ki ce kina son wannn shegen yaron, wallahi sai na sa'bar miki."Ta fad'a tana jan kunnenta sosai
Fareeda ta d'aga kai kawaii, don ita har a lokacin tana son Hisham.
A falo ta samu Daddynta, bayan ta yi masa sannu da zuwa ya ce ba ni numberr Hisham
Da hanzari ta bud'e ta shiga fada masa.
Alhji sule ya saka  numberr a wayarsa sananan ya kira ta yi ringing sosaii kafin ya d'aga kasancewar bai San lambar ba.
Bayan musayar sallama Alhaji sule ya sanar da shi yana son ganinsa.
Hisham bai yi niyyar zuwa ba, kasancewar ya zata shima kiran sa zaiyi ya ci masa mutunci amma daga baya zuciyar sa ta amince masa yaje din yaji dalilin kiran. Idan ya so idan ya ji zai raina masa hankali kawai zai sanar da shi ya fasa auren y'arsa don ba yar gwal bace.
Sai da yayi wanka ya shirya cikin had'addiyar farar shaddarsa president, saboda ma ba ya so a raina shi yafi so a san shima a dire yake da k'afafunsa.
A tsadaddiyar motarsa ya fita ya kuma fesa Wani had'adden designer, sananan ya tafi ko a mota tunanin da yake sake yi kenan sam ba zai d'au wula'kanci da rainin hankali ba.
Ko da yaje wayar Alhaji sule ya kira ya sanar da shi yana wajen gidan. Alhaji sule da kansa ya fito waje ya taro shi, har hakan ya dinga bawa Hisham mamaki to yayi mamaki mana babban mutum kamarsa .
Da fara'a ya tare shi yana fadin "welcome my son, mu shiga daga ciki mana."
Hisham duk kunya ta baibaye shi don ganin yadda yake tunanin mutumin ashe sam ba haka yake ba.

Bayan zaman sa Alhaji sule ya sa a kawo masa drinks, Hisham kurb'a d'aya ya yi wa lemon sannan ya sake duban senator.
Alhaji sule ya fahimci shi yake Jira,don haka yace "Hisham na san kayi mamaki dana ce ina son ganinka hakane?"
Hisham ya d'aga Kai "k'warai haka ne Alhaji."

Senator ya gyad'a Kai yace. "Masha Allah,to daman ba wani abun bane na samu labarin ka sanar da fareeda su biyu zaka aura, har ta tayar da borin k'arya wai ita ba ta sanka." Yaci gaba "Mata  kenan, su ba komai a Ransu sai son zuciya in dai a ka zo batun kishiya, amma abinda ya bani mamaki da na samu mahaifinka sai na ji ya ce wai ya hana ka auren yar uwar taka ne duk a bisa wani dalili nasa mara tushe,to Hisham abinda nake so da kai ka je ka ci gaba da neman auranka...."

Da sauri Hisham ya d'ago yana kallansa, Yana son tabbatar da gaskiyar abinda ya fada.Alhaji sule ya sake girgiza kai, k'warai ni nace ka je ka ci gaba da neman aurensu duka biyun Allah ya tabbatar da alkairi babu dalilin da zai sa kana namiji a hana ka abinda ranka ke so,ubangiji da ya halicce mu shi ne ya yarje maka auren mata hud'u,idan dai zaka yi adalci tsakaninsu. Don haka na sanar da mahaifanka tilas ya amince da auranka da duk su biyun idan ba haka ba ita ma fareeda ta hak'ura don babu dalilin da gida bai k'oshi ba za akaiwa dawa, fatana d'aya ka kasance Mai adalci tsakaninsu."
Hisham zubewa ya yi a k'asa sosai yana zuba wa senator godiya,tabbas ya sake ganin girma da mutuncinsa mutumin, Ashe a zamanin nan zaa samu burbushin irinsu?

Alhaji sule ya mik'ar da shi sosai yace bakomai Hisham kaje ka ci gaba da shirye shiryen ka In sha Allah nan da wata gudan za a yi komai a gama tunda babanka ya ce ka gama gidanka. Àllàh ya sa ayi a sa'a

Daga haka suka yi sallama. Hisham tun a mota yake kiran saudat, sai dai tana ta ringing sauda din ba ta d'auka ba. Hakan ya sa ya yi tunanin ko tana lecture don haka direct gidansu saudat din ya wuce saboda ya sake basu hak'uri ya kuma sanar da Abbansu ya amince da auren. Ya kuma sanar da su kudurinsa na kada su tashi hankalinsu shi zai yiwa saudat komai tunda ya san ba su da hanyar da za su aurar da d'iyar tasu nan da wata d'aya.
A k'asan layin ya yi parking sai dai gabansa ya fadi!! ganin a kori kura a k'ofar gidan nasu cike taf da kayansu Hisham girgiza kai ya yi had'e da saurin fitowa daga mota.
Gaba d'aya su khalil suna kofar gidan har da Abban nasu, duk kansu sun gan shi a ciki_ciki suka gaisheshi, shi din ma har k'asa ya durk'usa ya gaida Abban babu komai a fuskar abban da walwala ya amsa masa yace, Hisham ba ka jin magana ko? Ba abbanka ya hana ka zuwa nan ba? Ko kuwa da amincewar sa kazo? Hisham ya d'aga kai cikin sanyin jiki yace da saninsa nazo abba,amman don Allah Abba ina zaku naga ana fito da kaya?
Abba girgiza kai ya ce" Yanayin rayuwa Hisham ya sa zamu sanja muhalli."
Shiru Hisham din ya yi yana tunanin tabbas Abba mustapha siyar da gidan ya yi za su koma gidan haya. Amman don ya tabbatar da zarginsa sai yace Abba wani gidan kuka sake kenan?"
Abba ya d'aga kai had'e da son ya b'oye sirrinsa ya kuma basar da zancen had'e da cewa "Bari muje Hisham kada masu motar su gaji da jira."
Tsit Hisham ya yi daidai lokacin da ya hango sauda tana share hawaye. Yana kallo suka shiga adaidaita sahu amman ya kasa katabus. Sai can ya yi saurin ya shiga motarsa yabi bayansu don ya ga inda suka koma a zuciyar sa yana yi wa danginsa addu'ar shiriya. Sam babu Allah a Al'amarin rayuwarsu.
A bakin wani lungu suka tsaya sai a lokacin Abba ya lura da shi yace "A'a Hisham dama ka biyo mu ne?"
Hisham ya d'aga kansa kawai ba tare da yace wa Abba komai ba, illa bin gidan da ya yi da kallo a zuciyar sa yana tunanin wai wananan kwarrarrababben gidan anan zasu zauna,. Duk tak'amar arziki irin na danginsu gidajen kuwa kowa ya mallake. Su na gani na fada , banda wanda aka saka haya a ciki, amman a rasa mai taimaka wa wannan bawan Allah.
Cikin tsananin tunani da yake sam bai san har sun gama kwashe kayan ba tare da ya sani ba. Sai da Abba ya matso ya dafa shi yana murmushi, yace "Hisham tunanin mai kake?
Firgigit ya d'ago ya kalle shi kafin ya saki wata ajiyar zuciya yace "Abba dan Allah ina neman alfarmar ku bar gidan nan,ina da gida mai kyau a badawa layout, wallahi babu wanda ya san nawa ne, kuzo ku koma can ku zauna Amman wallahi Abba sam nan bai dace da ku ba."
Abba girgiza Kai cikin tausassan kalamai ya ce "ba komai Hisham, ita rayuwar duniya da kake gani ba komai a cikin ta hudusun fana'un ce. Komaii na cikinta zai k'are.imanin mutum ne kawai ba ya canja wa. Don haka a duk yarda ubangiji ya bar ni gode masa nake, saboda na san ba wai k'iyayya ba ce tasa ya aikata min hakan hasali ma babu wanda yake so na sama da son da yayi min Hisham ba zan koma gidanka ba, saboda ka san Abban ka yayi furucin idan ka sake taimaka mana bai yafe maka ba to bana son fushinsa ya sauka a kanka, kayi hak'uri ba zan sake karb'ar taimakon ficika daga wajenka ba. Hakan ma da kayi nagode maka Allah yayi maka albarka ya kare ka daga sharrin duk abin k'i, ina so ka zama mai jajircewa wajen yi wa mahaifinka biyayya."

Hawaye ne kawaii yake zarya a fuskar Hisham yana jin ciwo sosai, ba ciwon komai bane kuwa sai na rashin yadda zai yi ya taimaka musu. Tabbas bai yi dacen iyaye ba, tunda har za su Hana shi aikata alheri.
Abba mustapha ya dinga ba shi hakuri yana mamakin tausayi irin na Hisham. Tabbas zuciyar sa mai kyau ce Allah kenan mai fidda rayayye a cikin matacce, da kyar ya sashi ya shiga mota ya tasheta sam ya kasa ganin Saudat balle ya sanar da ita. Maganar da ta kawo shi, zuciyar sa cikin matukar kunci ya ja motar, ba gida ya tafi ba wani park ya tafi saboda yana buk'atar kad'ai cewa.

Abba mustapha kuwa yana shiga gida yabi y'ayyansa da kallo, gaba d'aya suna zaune sun zuba uban tagumi musamman khalil da idanunsa suka kad'a suka yi jajir, Abban ma ya sake bin gidan da kallo,sam ba shi da fasali gaba d'aya,d'aki biyu ne falle _ falle a gidan, sai Wani takurarren d'aki a soron gidan, da kuma kicin din langa_ langa shi ma d'in dan mitsili. Ya san abin da yake damun y'ayan amma sam sai ya basar, ya kalli sa'ad yace ya aka yi sa'adu ka samu kuwa ka tambayo adaidaitan?"
Sa'ad d'aga kai ya yi murya a dashe ya  ce "Eeh na tambayo Abba #950,00
Abba yace Masha Allah, to yanzu abinda za'ayi sabo za'a Siya guda d'aya a sayi tsoho d'aya. Idan ya so Kai ka ja saban tunda kai yaro ne nikuwa tsohon zanja"
Sa,ad yace Abba ai da kai ka ja sabon sabida kada tsohon ya wahalar da kai"
Abba ya ce "Babu komai ba abin da zai faru In sha Allah saii alheri" ya fad'a yana murmushi.
Khalil mi'kewa yayi kawai ya fita, Abba ya dubi sauran yace khalil zuciyar sa yau K'una take na san da yana da hali da ya cire mana wannan talaucin. Abin da nake so da ku kawai ku dage ku saka tsoron Allah a zuciyarku, ubangiji ya sa hakan shine mafi alkairi a tare damu, don wani kud'in ma masifa ne.
Umma ta ce,  "k'warai kuwa malam, Allah dai ya sa mufi k'arfin zuciyoyinmuu..."

Cikin dare khalil ya kasa rintsawa ya dinga ware ido yana kallon d'akin da ya kira akurki wanda suke k'untace sosai a cikin don Y.Mahmud ma sai a zauren gidan ya yi shimfid'a ya kwanta, kamar wanda aka mintsina ya yi saurin mi'kewa, jakar kayansa ya bud'e ya d'au kala biyu,sananan ya d'ebi takardun makarantarsa, daga haka ya samu doguwar takarda da biro ya fara rubuta:
Assalamualaikum
Iyayena yayana da k'annena,ina mai neman afuwa a gareku, wallahi zuciya ta ta kasa jure yanayin da muke ciki na tsananin talauci a kullum nakan yi kuka idan na tuna babu halin taimakonku,ga shi mun gama makaranta Amman babu aikin yi. Abin ya ta'azzara a zuciya ta a yau don sam na kasa rintsawa. Hakan ya sa zuciyata ta shawarce ni da na fita nema kawaii don Allah Abba da Umma ku yafeni idan na b'ata muku rai"

Daga haka ya ninke ya ajiye sadaf _sadaf ya mik'e ya bar d'akin mahamud yayansa ya tsallake daman k'ofar gidan sayawa aka yi . Saboda iska ta dinga shigarwa mahamud don haka khalil ya fice fit ba tare da sanin kowa ba.


Jikar Nashe ina godiya da adduoinku lafiya tana samuwa. Fatana mu yi aiki da alherin cikin littafin mu yi watsi da sharrin da ke cikinsa.

Continue Reading

You'll Also Like

16.8K 882 32
DR UMAIMAH USMAN BULAMA,Mace yar kimanin shekara ishirin da tara , Babbar surgeon A asibitin CITY TEACHING HOSPITAL , Aure Uku, ƴaƴanta uku . Mace m...
82.9K 4.4K 59
labarine da ya kunshi rikitacciyar soyayya da ramuwa,Wanda masoyan suna son juna Amman sun kasa gasganta haka Wanda har suka kusa su rasa juna hmmmm...
11.5K 1.5K 61
Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta cikin mummunar kaddara, irin kaddarar da b...
136K 9.6K 16
in which a boy leaves small notes on a girl's desk because he's too shy to actually talk to her in person