Zumuncin Zamani

By Nazeefah381

7K 516 25

Labari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52

11

133 8 0
By Nazeefah381

Kusan mintuna biyar suna knocking a bakin k'ofar sashen nasa bai bud'e ba, kamar ya san da ita aka zo ya d'au lokaci kafin ya bud'e, fuskarsa a d'aure yake dubanta, yana mamakin yarda lokaci d'aya ta birkice masa kamar ba Hamdan da ya sani ba, mai son sa da jin maganarsa, ta bi ta hau maganar Didi ta zauna a kai kamar wani fad'ar annabi, idanunsa cikin nata yana k'are mata kallo, kallon da ya takurata ta sunkui da kai, gaba d'aya kallon ya saka mata wata irin nutsuwar da bata shirya yinta ba, ita kuwa Sa'ada dariya ce take son kamata ganin yarda ma suka manta da ita a wajen har sai da ta yi gyaran murya sannan Hammad ya ankare ya saki wata malalaciyar ajiyar zuciya kafin ya mik'a hannu ya amshi basket d'in abincin da yake hannun Sa'ada ya ce "Je ki abinki Sa'ada akwai aikin da
Zata min yanzu zata taho." Hamda tayi raurau da idonta kafin ta ce "Wallahi Didi tace min kada na dad'e ka ga fad'a zata min." Ya watsa mata wani irin kallo da yasa Sa'ada wata irin dariya ta so kub'uce mata ta juya da sauri ta wuce don ba su saba y'ar wasa da Yaya Hammad d'in ba, amma kallon da yake jifan Hamdan da shi abin so ne ga kowacce mace mijinta ko saurayinta ya dinga mata shi, kallo mai nuna zallar so da nuna kewa ga wanda akewa shi, hannunta na rawa ta mik'a masa flask d'in kunun "Please Yaya Hammad ka karb'a kafin kasa Didi ta tara min mutane..." "Masifar Didi da tsinuwar mala'iku wanne kika fi gudu? Idan ba zaki shigo ki je kawai." Hawaye ne ya fara k'ok'arin zubo mata kafin ta saka k'afa cikin falon gabanta na fad'uwa, ta tsaya cak a bayan kujera shi kuwa tab'e bakinsa ya yi ya cigaba da zuba abincinsa lura da yayi da ko cewa ya yi ta zuba masa yarda take a tsorace ba zata zuba ba, shi har mamakinta ma yake kada fa ta zamo masa bagidajiya ba irin Nanna da take kanainayeshi ba, da sonsa da ba son ransa take fincikar ra'ayinsa sau tari. Ya fara kurb'ar kunun idanunsa suna yawo a kanta ta ji yace "Wani sabon salo kika samu? Sai kace sabon aure ba zaki dawo nan kusa da ni ki zauna ba? Saboda kina tsoron Didi ko?" Ya taune leb'ensa d'aya kafin ya furzar da huci ya ce "Idan kika ce haka zaki min wallahi a gadon Didin zan zo na karb'i hak'kina haka kawai saboda wata bidi'a ta banza da wofi ki yi ta d'aukan zunubi da azimin nan, ke kika jiyo ni ina da wata matar yau ma rashinta ne yasa nake binki duk da ba ni na jawoki ba, ke zaki je ki yi ta kwana rungumar filo ai dama Sabonki ne tun kina budurwa."
Wani irin kallo take jifansa da shi kamar ta zunduma masa ihu jin abinda yake ce mata, ita zai gayawa wani yana da mata ai ta fisa sani dama ita ta kawo kanta har da zai tsaya ci mata mutunci, haushi da takaicin kalamansa yasa ta juya a zuciye ta fice daga falon duk da tana ji yana k'wala mata kira. Ya saki ajiyar zuciya yana jin takaicin yarda bakinsa ya ja shi ya sake b'allowa kansa ruwa ya santa sarai da d'an banzan kishi, ba waya a hannunta balle ya kirata.

Tana zuwa falon ta tarar da bak'i a falon Didin atamfofine da laces da shaddodi take ta bud'ewa, sai wasu akwatina biyu da kit a gefe, kasancewar zuciyarta ba dad'i yasa ta yi k'ok'arin shigewa d'aki bayan ta gayar da bak'in mazan da suke zaune. Didi ta ce "Ke Hamda zo nan ai sak'on naki ne, KK ne ya aiko ko da yake wannan ni ya aikowa ya ce a rabawa dangi, wancan akwatinan dai su ne naki." Hamda ta koma ba don ta so ba ta hau bud'e kayan sabuwar wayar tafi tafiya da imaninta wacce take cikin kit d'in sai dantsatsetsiyar sark'ar gold wacce da gani babu tambaya dollars ta sha kuka wajen siyanta, akwatinan kuwa laces ne dandatsa-dandatsa da atamfofi super sai mayafansu HD Veils da jakunkuna uku da takalmansu, a ranta ta yi farin ciki da kayan amma yarda zuciyarta take tunzira da kalaman Hammad yasa fuskarta bata nuna ba, Sa'ada kuwa sai tsalle take tana d'aga Iphone 14 pro max tana cewa wallahi yarinya kin shigo gari. Bata tab'a komai a kayan ba ta mik'e ta shige d'aki, tana shiga ta yi wurgi da d'ankwalin kanta gashinta ya wargaje, sai sannan wani kuka mai k'arfi yazo mata, ji take da tana da hali da ta fasa auren Hammad d'in don ita tana daga cikin jinsin mata masu zafin kishi. Kuka ta yi sosai bata fito falon ba har sai da Sa'ada ta shigo kiranta Didi ta tara ayarin gidan wai zata yi rabon kayan sallahr da KK ya kawo.

Fuskarta a kumbure ta fita, duk wanda ya kalli idanunta  ya san ba k'aramin kuka ta sha ba, shi kansa Hammad hankalinsa a tashe yake dubanta ji yake da da hali da ya kai mata runguma ya rarrasheta, amma ina ko arzikin kallo bata samu ba, sai ma harara da ta wurga masa ta yi k'asa da kanta. Abbu ne ya lura da yanayinta ya ce "Zo nan Hamda me ya sameki haka? Naga kamar kin yi kuka?" Girgiza kai kawai ta yi tana k'ok'arin mayar da hawayen da suke son sake zubo mata, murya a dashe ta k'arasa kusa da Abbun tana girgiza kai ta ce "Bakomai had'e da gallawa Hammad harara." Didi ta ce "Kaima dai Ummaru da shirme ka ke, kukan me zata yi banda na farin cikin samun uba kamar KK ga uban kaya da ya d'and'aso mata ga shegiyar waya." Hamda ta zabga mata wani kallo kafin cikin takaici ta ce "Ni ba kukan da nake ba kenan, ke wannan ya dameki ai dama tun kafin Ya zo Abbu yana mana duk abinda muke so." Sosai Abbu da Ammi suka ji dad'in amsar da Hamda ta bawa Didi, idan ita ta manta gwara Hamdan ta mata matashiya kuma ya san ko nan gaba Hamdan ba zata gujeshi ba. Didi ta ce "Y'ar banza mai ido a tsakar ka, duk tsiyar Ki dai da KK d'in zaki tunk'aho.." ta sake zunb'ura baki "Ni wallahi da Abbu zan yi tunk'aho tunda shi ya yi d'awainiya da ni har na girma." "Ke kika jiyo, ba wannan yasa na tara ku ba, kai Hammad tunda Sadiya ta k'i zuwa bak'in cikin duniya ya isheta kaje ka kira min ita ko zuciyarta zata buga sai ta ga wannan kab'akin arzikin, don ina lura da ita tunda lamarin nan ya faru shikkenan Sadiya halin uwarta ya fara bayyana tare da ita, yo uwarta banda dai idan taso mutuniyar kirki ce ai da ba ta zama aminiyata ba, don ko farar k'asa aka shafe min d'aki da ita sai hassadar ta ta nuna, ta dinga nurk'ufanci kenan, sai dai Akwai kyauta, kawaici da alkunya sumumu kasau ce ta gaske.." Hammad ya datsi leb'ensa banda idanuwan su Abbu yau kam da ya ganar da Didi kurenta. Ya saka kai ya fice yana ji tana fad'in "Sai dai hararar duka dai ba zan daku ba, ja'iri mai idanuwa kamar na muzuru."

Yana saka kai d'akin Mahmah ya ji tana waya tana fad'in "Sakna nace miki yanzu fa zan je don na ji ance duk ta tara mutane wai za tayi rabon kayan sallah, to yanzu zan je wallahi nace and Atabau bana son auren....." Hammad ya tura k'ofar idanunsa zube cikin na mahaifiyarsa yana jin takaicin yarda Salma take neman jirkita masa zuciyar Mahmahnsa mai adalci, baya son laifin da yake tsakaninta da Ammi ya shafi aurensa da Hamda, su d'in ma k'ok'arin sa kullum su fuskanci juna su zauna lafiya duka-duka duniyar ma nawa ce, ya saki ajiyar zuciya yana zama a kujerar da take gefen gadon a hankali ya ce "A sani na dake Mahmah uwace da za'a yi alfahari da ita, duk gidan nan an shaida cewa ba kya barin kishin da ke tsakaninku da Ammi ya shafi mu y'ay'a, abubuwa nawa kika shanye sai yanzu da rayuwar ta zo gangara za'a samu wasu can daga gefe su zuga min ke Mahmah, don Allah kada zuciyarki ta amince da zugarsu su zo su saka ki ki yi abinda zai zubar mana da
K'imarki da mutuncinki da
Ake gani, kowa fa ya shaida hak'uri da juriyarki a zaman aure wanda muke fata ya dalilin haka Ubangiji ya yi miki sakamako da jannatul Aaliyah. Don Allah Mahmah ki janye wancan furucin da na ji kina yi a waya ko ma da wa kike yi na tabbata Ba shawara mai kyau yake baki ba wacce duk wani mai sonki zai ba ki, ki d'auki Hamda kamar y'a insha Allahu ba za ki yi dana sanin aurenmu ba, sai kin yi alfahari da haka sai kince gwara da aka yi, kuma ni Mahmah wallahi ko wa na aura ba zan bari ta rainaki ba, Zan jajirce wajen kare martabarki da k'imarki, kuma in dai tana sona dole ta miki biyayya." Sosai zuciyarta ta samu nutsuwa har ta ji tana jin kunyar abinda ta so aikatawa duk da Allah ya dubi zuciyarta bata aikata ba, ita kanta ta san ba halinta bane sharrin shaid'an ne da karakainar zuciya suka so dulmiyar da ita, ta godewa Allah da ubangiji ya kawo Hammad ya ankarar da ita abinda zuciyarta da tunaninta suka so su gusar mata, Sai ta samu kanta da jin kunyar Hammad d'in shi kansa ta yarda yana d'an cikinta shi ya zauna yana tunasar da ita abinda ta manta, kaiconta da ta so jawowa kanta da zuri'arta abin kunya, da da wani idon zata dubi Hamda yarinyar da ta rik'eta tamkar Uwa take ganin daraja, k'ima da mutuncinta, sau tari Idan Uwarta ta tunzirota tana kuka idan Didi bata nan, nan wajenta take zuwa ta samu sauk'in zuciya. Ta gyara zamanta tana sakin wata ajiyar zuciya ta murnar rashin aiwatar da k'udirinta ta tabbata da mutuncinta ya zube a idanun duk jama'ar gidan. Hammad ya saki murmushin samun nasara kafin ya mik'e da kansa ya yafa mata mayafin yana fad'in "Alhamdulillah, Da Allah yasa ki ka fahimceni yanzu ma Didi ce ke nemanki, kowa ya halarta banda ke."  Ta mik'e jikinta a sanyaye ta bi bayansa zuciyarta tana jin farin ciki a hankali ta furta "Madalla da kai ubangiji madalla da samun Y'ay'a na gari ko da su kad'ai aka barni ba abinda zance sai Alhamdulillah!"

A falon kowa ya hallara, ta samu zuciyarta da tsinkewa ta fad'i tunanin da tuni a cikin jama'ar nan zata zo ta zuba rashin mutunci. Didi ta zuba mata ido cikin takaici ta ce "Ba shakka Sadiya, wato nema ki ke duk wasu d'abiu na Sakina da ta zubar da su, ke ki tattara ki yayima ki zubawa kan ki, ana yabonki Sallah za ki kasa alwala, idan banda haka mutun nawa na aika kiranki ki ka yi burus da ni sai yanzu da d'anki ya je ya lallab'o ki  sannan za ki zo ko?" Girgiza kai Ta yi kawai had'e da zama cike da kasala ta ce "Ki yi hak'uri Didi, ba k'in zuwa na yi ba bana jin dad'i ne." Didi ta girgiza kai "Ko da na ji, nan ina nan ina mamakin yarda ki ke nema ki canja daga ainahin sunanki na Halimatu wato mai hak'uri, ai duk wata Halima da hak'uri aka santa idan ba so ki ke ki zama masifatu ba, yo fisabilillahi waye bai san kalar hak'urin da kika yi a gidan nan ba, k'iri-k'iri Umaru ya dinga banbanta ki da abokiyar zamanki kai wallahi Umaru ina jiye maka tashi ranar alk'iyama da shanyayyen jiki Idan Sadiya bata yafe maka hak'kintaba kai da matarka." K'asa Abbu ya yi da kansa yana jin kunyar yaransa Su Hammad da suke zube a wajen, wani abu ne na tausayin Sadiya ya taso tun daga yatsansa ya lullib'e idanunsa, kunyarta yake ji sosai da ta yaranta, yau kam Didi ta b'aro masa aiki ta kuma ankarar da shi abinda ya dad'e yana son gyarawa son zuciya da sharrin shaid'an had'e da bin k'awace-k'awacen duniya ya hana shi ankarewa, sai yau da Didi ta taso da maganar takaicin kansa ya kamashi ya kasa had'a ido da kowa a d'akin musamman Sadiyar da ta sauke nata idanun a kansa tana son taga yarda zai yi, Ba shi da laifi a wani b'arin Sadiyar ce ta janyo koma mai ya faru, wata zuciyar kuma na k'addamar masa da laifinsa da hasko masa tarin kuskuren da ya tattafka a tsawon zamansu da Sadiyar, ya wajaba kam a gareshi ya nemi yafiyar ta kafin abinda Didin ta fad'a ya tabbata a kansa ya tashi da shanyayyen b'arin jikin, yana kallon idanun da Humaid ya zuba masa ya tabbata Ba tun yau yaron yake rik'e da shi a ransa ba, don duk ya fi su Hammad zafin zuciya. Ya gyara zamansa idanunsa cikin na Sadiyar yana sakar mata da murmushi zuciyarsa na hasko masa tarin kyawawan halayenta da nagartarta duk da ta b'angare d'aya take da cikas hakan ba zai zama hujja a gareshi da zai kasa yi mata adalci ba, d'auke kai ta yi tana fuskantar Didi da ta fara Rabon sufofinta, zuciyarta fes ta tabbata daga yanayin murmushin da ya sakar mata sak'on Didi ya isar masa burinta ya yi aiki da hakan su yi zamansu lafiya cikin aminci da k'aunar juna, abu d'aya ne Ba zata iya wannan kwamacalar soyayyar ta zamani, za dai ta k'okarta wanda ta ga zata iya, tausa, shafa masa mai amma banda duk wani kalar barikanci da Sakna take yi, wannan kam ta barwa yara ita da kanta ta yarda da maganar bahaushe da ya ce 'In An girma a san an girma'

Jikar Nashe taku ce!

❤️❤️❤️❤️❤️🙏

Continue Reading

You'll Also Like

136K 9.6K 16
in which a boy leaves small notes on a girl's desk because he's too shy to actually talk to her in person
82.8K 4.4K 59
labarine da ya kunshi rikitacciyar soyayya da ramuwa,Wanda masoyan suna son juna Amman sun kasa gasganta haka Wanda har suka kusa su rasa juna hmmmm...
1.4M 127K 62
RATHOD In a broken family, every person suffers from his insecurities and guilt. Successful in every field but a big failure when it comes to emotio...
Alina By ihidethisapp

General Fiction

1.5M 37.2K 75
The Lombardi family is the most notorious group in the crime world. They rule both the American and Italian mafias and have many others bowing at the...