Chapter One

41 2 0
                                    

🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️
🍃🌹
DUNIYAR MU AYAU
🍃🌹
🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️ 🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️

Story and written By

Khadeejaht Hydar Young-Novelist

The experience writer of 👇

IHSAN
UQUBAR UWAR MIJINA
WATARANA SAI LABARI
PRINCE AIRAN AND MAIMOON
KANKI KIKA CUTA
SABREENA SABEER

And now with the most useful one👇

DUNIYAR MU A YAU
(Tragedy,life challenges).

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Ban yarda wata ko wani ba su juya min littafi ba.

Ga masu son samun wannan littafin updated ba tare da neman jira ba a duk lokacin da nayi post to a neme shi a wattpad, kuyi follow sannan ku danna vote akan kowane pages na littafin DUNIYAR MU A YAU

Follow and vote on👇

WATTPAD
YoungNovelist4

Blog:
https://khadeejahthydaryoungnovelist.blogspot.com/?m=1

INSTAGRAM
Khadeejaht-hydar -youngnovelist

TWEETER
@Young Novelist II

FACEBOOK
Khadeejaht Hydar YoungNovelist

BAKANDAMIYA
Khadeejaht Young-Novelist Hydar

GMAIL
NanaKhadeejamusa@gmail.com

Ban yarda wani ko wata ba ya juya min littafi ba.

Kaɗan daga littafin DUNIYAR MU A YAU.

Chapter One (I)

Wallahi tallahi Mama ki daina ganin wai ina miki magana cikin kwanciyar hankali kawai ɗaga miki ƙafa nake saboda sam ni ban saba da takura ba, haba kullum ke cikin takurawa mutum kike haka kika ga Ummin su Balkessu take yi? Wlh ita sam bata takura ma ƴaƴanta kamar yadda kike yi, ni gaskiya nagaji Allah kika ƙara takura min zanbar miki gidan taƙarasa maganar tana mai murguɗa ɗan ƙaramin bakin ta. Cikin takaicin halin ƴar tata Mama tace "yanzu Fatima ni kike gayawa magana haka kamar ba nice na tsuguna na haife ki ba, Allah ya shiryaki dake da ƴan uwanki gaba ɗaya amin. Yayarta mai suna Ummul-Banee tace: "Yanzu Mama kike faɗaawa wannan maganar sai kac... bata ƙarasaba Fatima ta katse ta da cewa: "dalla Malama ki rufemin baki kafin mu kwashi ƴan kallo a gidannan wa zaki gayawa magana shekara nawa kika bani da zaki dinga min faɗa ke ma kiji da naki agun, munafuka kawai tana gama faɗar haka tabar gidan tana tauna chewing gum ji kake ƙes ƙes tana tauna,inda sabo Ummul-Bani ta saba da zagin Fatima don haka ko a kanta bata ɗau maganganun taba.

🌞

"Assalamu alaikum,ah wa'alaikumus salam ah Fatima kece shigomana kika tsaya kamar baƙuwa,tace"ina yini Mama ina Balkeesu?,"tana ciki mana tana aikinnata zaman ɗaku sam bazatana fita irinnakiba daga makaranta sai gida,ƙanwar Balkeesu mai suna Salma ta ƙarbi zancen da cewa"ai ita Anti Balkeesu kullum sai yima mutane wa'azi wai ita ta Allah ita da wannan ƙawar tata Hajara amma ke Anti Fatima ba ruwanki ke simple ce aci life kawai kinfira daban acikinsu sai isa kike birgeni,Mama tace"ai yafi ni banson mutum yayita kauyanci waishi ala dole yafi kowa sanin Allah.

🌞
"Wash Anti wlh nagaji kinga irin exam ɗin damu kayi kuwa wlh dakyer muka sha,kai Anti Lubna banfaɗa maki ba yau nayi kamu kaiii sai kingan shi anti kamar ba indiye don kyau sunansa Abdul-Lateef ,cikin dariya wacce aka ƙira da Anti Lubna tace"yau kuma Auta kece da yaba saurayi lalle wannan guy ɗin ya taki sa'a Allah yasa na ƙwarai ne bamai yaudara bane,cikin dariya auta wacce sunanta Hajara tace"amin anti kinga yau Balkisu da Fatima basuda paper basuzo ba saini kaɗai,amma Anti kinsan me?,Lubna tace"a'a tace"yace nabasa numbata naƙi kuma ban nuna masa gidan mu ba ai banyi laifiba ko?tace"bakiyiba inhar dagaske yana sonki to zai nemeki karki damu,tace"tnx Anti Umma tana bacci kenan tunda banji motsintaba kodai bata dawo daga makaranta ba,"a'a taje maƙwabta zata dawo yanzun kije kiyi wanka ga abincin ki nan kina gamawa kutafi hadda kar Balqeesu tazo tana jiranki kinsan ta da sammako,tana dariya tashige ɗakinta don watsa ruwa tana ta gaggawar Balqeesu tazo tabata labarin Abdool Lateef don batada ƙawar daya wuce Balqeesu da Fatima da Ummul bani amma halinsu yafi zuwa ɗaya da Ummul Bani da Balqeesu sai isa sukafi shaƙuwa.

Suna hanya zasu tafi hadda su biyar Ummul Banee da ƙanwarta Fatima ,Balqeesu da ƙanwarta Salma sai Hajara ƙanwar lubna wanda ita bata zuwa saboda tagama haddarta tana koyarwane a wata islamiyya,Jere su uku wanda suke kai ɗaya suke tafiya sai Salma da Fatima waenda suma suka kasance sa'oin juna suna tasu firar a baya,su Hajara sunada shekaru 19 sai su Fatima masu 17 sai shegen tsayin ƙafa,haka suna surutunsu har suka ƙarasa makarantar tasu wacce takasance babba,su ukun suka tafi ajinsu su biyu ma haka.
Bayan sun kammala karatunsune suka fito zaman jiran su Fatima don dama suna rigasu kammalawa,Hajara takallesu cikin zumuɗi tace"albishirunku,suka ce goro tace"uhm wlh yau nayi kamun wani haɗaɗɗen guy sunansa Abdul-lateef Balqeesu zanso ku gansa ,cikin zumuɗi sukace wow aina kenan,tace"jiya mana bayan nagama paper nafito naganshi a bakin store tofa shine yaketa bini a mota nan de tafaɗa musu komai,Ummu tace"kai meyasa baki basa numbar ba ai da kinbasa wlh,Balqeesu tace"gwara ma dabaki basaba inyanasonki zai sake nemanki,Hajara tace"wlh hakama Anti lubna tafaɗa jiya,nan de suka zauna suna fira har su Fatima suka fito suka kama hanyar gida.

Balqeesu tace"Hajar sunan da suke yawan ƙiranta kenan tana cewa wlh banaso amma harta saba,kalli wani haɗaɗɗen guy a tsaye da sauri Hajar da Ummu suka kalli inda take musu nuni kafin suyi magana yabar jikin motarsa yaƙaraso cikin fara'a yace"gimbiyata sanna da fitowa fatan anyi karatu lfya,cikin mamaki Ummu da Balqeesu ke kallonsa to dawa yake magana,cikin kunya Hajar tace"ina yini,"lfya ya amsa tare da cewa sannunku ykk ,"lfya suka amsa,cikin barkwancinsa yace"am Abdul Lateef by name daganin alama ƙawarku bata muku bayani naba sai isa nagabatar da kaina agunku kusan da zamana,cikin farinciki suka gabatar masa da kansu su biyun don already su Fatee sun wuce gaba,barin motarsa yayi yafara binsu da mamaki Hajar tace"bawan Allah daka koma mu ƙarasa kabar motarka ba kowa mungode,cikin tsantsar sonta daya shigesa yace"karki damu don zan raka gimbiyata aiba wani abun bane in an sace motar ma saiki sayamin wata,murmushi tayi tace"kodai Daddyn ka yasaya ma sabuwa ba,dariya yayi yace"oh ni banda kuɗin sayan mota sai Daddy yasayamin kenan,gyaɗa kai tayi alamar eh,yace"to ngd su Balqees na gaba sai yaba Abdul-lateef suke don guy ɗin ya haɗu ba ƙarya dagani ɗan masu kuɗi ne don kama daga motar sa har kayan daya saka kuɗi ne,saurayine matashi mai jini a jika dogo ne sosai mai faffaɗan ƙirji baida hasken fata saɓanin Hajar datake fara sol mai doguwar fuska da ƙaramin baki,shi kuwa yana da ɗan gemu wanda ya haɗe da sajensa ya ƙarama doguwar fuskarsa kyau,yaɓada ushirya yanada haƙora ƙanana a jere ga bakinsa pink shar,saida ya rokosu har ƙofar gidansu Hajar don gidansune layin farko ,zata shige ciki yace"Haba Qalbee dan Allah ki bani numbarki ina ƙiranki don nasan rabon samunkine yadawo dani Nigeria ba komai ba,dakyer yakyar bi numbar ta agun su Balqees dayake tanada ƙaramar waya saida ya ƙira yaji yana ringing acikin jakarta tukun yayi murmushi yace"kawo muga wayar taki,miƙomasa Ummu tayi tana ma Hajar dariya ,saving ɗin numbar yayi da SURURI(Kwanciyar hankali na)tukun yamiƙa mata wayar ya musu sallama ya tafi yana mai ɗaga mata hannu,su Balqees suka ce"Wow Hajar aiyafi yanda kike faɗa kyau kai Masha Allah,Allah yasa mijin kine amin,Hajar tace"amma ku ƴan iska ne daga haɗuwa da mutum zakuna zancen aure to Allah sawwaƙa maku de ni kunga ku wuce gida yamma tayi gobe ma haɗu a hadda,Ummu tace"oh kinga mun manta ance gobe muje school kinga ba zancen mu haɗu a hadda ,tace"shikenan saimun haɗu Allah yakaimun ku gida lfya,haka suka wuce gida suna kewar juna kamar karsu rabu kamar kullum de bacci ke rabasu.

Kai Abdool wannan fa kai Allah ya zankaɗa halitta anan wannan ai sune kalar matan Aljanna wannan sweet sixteen 16 ce zatayi daɗin shanawa,wata wawiyar harara ya gallawa abokinsa Yusuf yace"amma wlh kai banzane ko wacce yarinya ce abar shanawa da ƴar kowama saikayi rayuwar banza wlh inade faɗamuku daku gyara halayyarku,abokinsu wanda yake gefe yace"Guy karka raina mana hankali yanzu faɗamana cewa zakayi wannan yarinyar bazaka kwashi kayan daɗintaba kana ganinta sharab sabuwar nuna kace bazaka shanaba ai kai kaga nan dai kalar wayayu amma kanka a rufe yake ai ni nasamu kalar yarinyar nan ai sai inda maina ya ƙare ba rana ba dare zanna gyarata ne,ɗakin ya barmusu yana mai takaicin halin abokan nasa wanda basuda aikin yi sai lalata rayuwar yara waenda Allah ya jarabta da waenda suka bi hanyar shaiɗan da masu son kuɗi.

Ku biyoni donjin wannan labari mai cikeda tausayi da darrusan rayuwa,miye ra'ayinku akan Novel ɗinnan na tsaya ko inci gaba da baku lbarinnan mai cikeda al'ajabi........

Young-Novelist✍️.
Karku manta ku danna vote akan kowane post na DUNIYAR MU AYAU,DA Sabreena Sabeer a wattpad ɗina YoungNovelist4,ina matuƙar gdya da masu FOLLOW da VOTE..

DUNIYAR MU AYAUWhere stories live. Discover now