Auren Bazata page 17

647 28 13
                                    

✨AUREN BAZATA✨
(2017)

WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
     SHUKRAH




Edited page.

1⃣7⃣

Shukrah na ganin su Ammii sun shigo ta fara k'ok'arin tashi, Mamah ce ta rik'eta tana mata sannu, da ƙyar take answer kafin take mayarda kallonta gurin Amminta with pity face tace  "Ammii Dan Allah ku taimaka min ku bawa Ya Safeer hak'uri karya kara Aure,I can't withstand sharing him with other woman,beside that wallahi na chanja hali na, I've changed kuma bazan k'ara rufe masa k'ofa ba"
Mamah ce tayi saurin rufe mata baki tana jero mata sannu
,tace "is okay Shukrah Kinga Doctor yace ki dena damuwa ki kwanta ki huta kinji" cewar Mamah da tausayin Shukrah ya cikata.

Kuka kawai shukrah tasa don ita tayi tunanin Mamah zata ce an fasa Auren ne amma sai taji akasin hakan.

Zama Mamah take gyarawa Shukrah a jikinta tana patting bayanta trying to calm her down.

Da sallama Safeer ya shigo room d'in hannunsa rike da trolley wanda ya debo kayan Shukrah a ciki, bayan sun gaisa da su Ammii ne ya nemi guri ya zauna yana kallon Shukrah da duk tayi laushi lokaci guda,
K'ok'arin tashi Shukrah keyi Amma Ammii ta hana hakan, kuka take tayi tana kallon Safeer shima kallon ta yake cike da tausayi, had'e hannayenta biyu tayi tace "Ya Safeer Dan Allah ka rufa min Asiri kamar yadda Allah ya rufa maka karka k'ara Auren nan wallahi bazan iya zama da kishiya ba bana sonta bana k'aunar ta"

Ammii ce tayi saurin doke bakinta tana harararta tace "Karki so kishiyar to kinsan bakya son kishiyar kike abinda kike?",wiping tears Shukrah tayi looking back to Ammi tace "Ammii wallahi na dena kuma ki tambaye shi" ta fad'a tana k'ara fasa wani kukan.
Mamah ce take 6ata rai tace "A'a Ammii ba haka ake ba gaskiya ki dena mata fad'a Kinga condition d'inta fa, hawan jini ai ba wasa bane".

zuwa wannan lokacin kukan Shukrah ya fara ciwa Safeer rai don Shukrah tsakani Da Allah take kukan hakan ne yasa Shi tashi ya fita daga room d'in hurriedly.

Mamah ce ta dawo kusa da Shukrah tana ta lalla6ata taci Abincin da Aysher ta kawo d'azu,while crying Shukrah tace "Mamah bazan iya ci ba mutuwa zanyi wallahi,Dan Allah ki bawa Ammii,Daddy da ya Safeer hak'uri kinji" ta fad'a tana k'ara volume d'in kukan ta wane shi aka aiko ta.

*****
Da daddare Mamah cewa tai ita zata Zauna da Shukrah, haka kuwa akayi Ammii ta tafi gida tana ganin kirki irin na Maman Safeer,kamar ba d'anta Shukrahn take 6atawa ba.

Washe gari da safe Aysher ta kawo abinci sannan ta wuce School.

9:00am Safeer da Haiydar suka shigo duba Shukrah, Gaisawa sukayi da Haiydar sannan ya fita dama Mamah da Miemie sun tafi gida don yin wanka saboda haka d'akin ya rage daga Safeer sai Shukrah,
Shiru ne ya ratsa d'akin ba wanda ya cewa Dan uwansa ci kanka,Shukrah nason yiwa Safeer magana at least ko hak'uri take bashi amma batada gut tasan itace da lefi,tana ganin ma it's too late to cry sai tayi shiru tana take fidgeting fingers d'inta har zuwa wani lokaci, gajiya tayi da kallon da Safeer ke mata ta mik'e ta shige toilet abinta.

Shima Safeer ganin they're about to get late sai ya  mik'e yaje ya samu Haiydar a waje suka fice daga Asibitin ma gaba daya zuwa office.

Ammii ta riga Mamah zuwa saboda haka ta samu damar yiwa Shukrah tatas,Sosai Shukrah take kuka tana jin inama zata iya cewa Ammii
     "Ni na shirya basa kaina shine be nemeni ba"
Amma bazata iya ba, Hakan yasa ta cigaba da kukanta kamar an aiko ta tanajin inama mutuwa tazo ta d'auketa a wannan lokacin ta huta da bakin cikin da take ciki a yanzu.


****
Wasa-wasa sai da Shukrah tayi one week a Asibiti sannan akayi discharging d'inta, Mamah ce ta dage sai ta tafi da Shukrah gidanta saboda tana kallon yadda Ammii takewa shukrahn kamar ba ita ta haifeta ba.
Haka dai suka tattara suka koma gidan Mamah, sosai Shukrah take samun kulawa gurin Mamah da Aysher, Miemie ma ba a barta a baya ba don Sosai take damun Shukrah da surutun ta kuma itama Shukrahn tana jin dad'in zama dasu, mutanen kirki ne yadda suke mata ko safeer basayiwa haka.

Sosai mutanen Mamah da Ammii suke zuwa duba Shukrah, Abokan Safeer ma sunzo, Haiydar ko dama kullum sai yazo kodan yaga sahibarsa (Miemie),Kawayen Miemie duk sunzo dan gida-gida ta dinga zuwa tana fad'a musu azo a duba Auntyn ta batada lafiya, in ba kazo ba kuwa zuwa take ta tawo da kai.

Sati biyu Shukrah tayi a gidan Mamah sannan ta koma gidan Ammii kasancewar next week zata koma gidan Safeer.

Sosai Safeer ya gyara gidansa har furniture's d'in Shukrah sai da ya changer mata, gida dai ya had'u iya had'uwa Dan da  Miemie taje cewa tayi bazata tawo ba(lols).

Wannan karon Ammii ta dage sosai take gyara 'yarta dan ta fahimci ba abinda ya ta6a shiga tsakanin su da safeer,kuma tana tsoron kar kishiya take kwace wa Shukrahn mijinta...a cewarta.

Yau saura  3day's Shukrah ta koma ji take gaba d'aya batasan komawa, tunanin taya zata soma zama da kishiya duk ya isheta,wani lokacin she wish she can turn clock back da tayiwa Safeer biyayya iya biyayya ko don Daddynta ma.

Yau ta kama wednesday kuma tun 7:00pm Safeer yazo tafiya da Shukrah kasancewar yau zata koma,Kuka take baji ba gani ko a mota bata kalleshi ba sai kukanta ta take har suka karasa gidan da take fargabar isa saboda lokacin da zatayi eye contact da co-wife d'inta will be her worst moment in life...............






Shukrah Cute🥰

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 07, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

AUREN BAZATAWhere stories live. Discover now