Auren Bazata page 10

381 13 0
                                    

✨AUREN BAZATA✨

WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
     SHUKRAH

Edited page..

   1⃣0⃣

SAFEER ne ya shigo cikin room d'in hannunsa rik'e da kaya,ya ajiye a bakin entrance  sannan ya k'araso ciki ya durk'usa kusa da Mamah suna gaisawa da Ammii cike da ladabi.
Mamah tana kallonshi sosai tace "ya me jiki?"ya kalli Shukrah kafin yace "Da sauki Mamah" tayi nodding kafin tace "Allah ya k'ara sauk'i to"dukansu suka had'a baki wajen cewa "Ameen",sai Safeer ya k'ara duban Ammii da taketa hararar Shukrah ganin ko kallo Safeer bai isheta ba bare ta gaidashi yace "Ammii ina Areef" ta dawo da idanunta kansa kafin tace "Areef yaje school" Safeer ya mik'e daga durk'uson da yayi tun shigowarsa yana cewa "To Allah ya dawo dashi lafiya." Mamah tace "Ameen" kafin Ammi tace "Safeer bazaka je office bane?" Sai da ya k'arasa yaja visitor's chair ya zauna kafin yace "Ehhh Ammii zan zauna a nan" Ammi tayi saurin cewa "A'a ba za'ayi haka ba tashi zakayi ka tafi inyaso anjima kazo kaga jikin nata"yayi shiru,ganin he's not ready to walk out Ammin ta d'ora da "Ai tama ji sauk'i" Ta k'arasa  tana hararar shukrah, don ita jira take su ke6e da shukrahn ta fad'a mata dalilin dayasa taki bawa Safeer kanta,don she's quit sure Shukrah is behind all these.Mamah da duk abinda ake batace komai ba tun d'azu tace "Tashi kaje gida kayi wanka ka tafi office kaji d'an Albarka" ya mik'e kafin yace "To Ammii Allah ya bata sauk'i" sannan ya fice.

     2:40Pm da- dai Safeer suka shigo shida Haiydar hakan ne ma yasa bayan sun gaisa da su mamah suka fita suka basu guri,Gaisawa Haiydar sukayi da shukrah cike da girmama juna, sannan haiydar ya ajiye mata bandir na 100naira ya mata sallama suka fito tare da Safeer d'in da tak'i kallo tun shigowarsu.
sai bayan magrib sannan Safeer ya tafi kai maamah da Aysher gida, sai a nan ne Ammii ta samu damar ke6ewa da Shukrah.
Ammi ta dawo kusa da Shukrah da tak'i kallonta saboda batada gaskiya,ta had'e fuska sosai tace "Shukrah" Muryar Shukrah har rawa take ta answer " Na'am Ammii" tace ba tare da ta d'ago ta kalle taba. Ammi ta k'ara had'e rai  sannan tace "dake nake Shukrah dago idonki ki kalle ni" a sanyaye Shukrah' ta dago tana kallon Ammii'n zuciyarta na harbawa da sauri da sauri wane zata fito don tsoro da fargabar. Ammi ta rik'e right ear d'inta a zafafe tace "ki fad'amin dalilin dayasa kika hana safeer kanki all this while Shukrah",tambayar tazo mata a bazata dan bata ta6a tunanin Ammii zata gane ba (Yaro yarone),ta d'ago a razane amma suna locking eye's tayi saurin kawar da kanta k'irjinta yana cigaba da bugawa da Sauri, jin tayi shiru yasa Ammii daka mata tsawa tace ". Ke ki kiyaye, ki kiyaye ni shukrah ni ba sa'ar bace da zan zauna ina miki magana ki mayar dani mahaukaciya,ki bud'e bakin ki ki bani answer kar ki kaini bango,kafura ce ke Shukrah da zaki dinga tauyewa miji hakk'i?, Ashe dama baki daukemu da daraja ba Shukrah? Mu bamu isa dakeba ashe da zamu za6a miki miji ki kar6a hannu biyu-biyu ba?Daddyn zaki watsawa k'asa a ido?Wallahi Shukrah ki bani kunya ban ta6a tunanin zakiyi haka ba da hankalin ki da komai,ace mahaifinki ya isa da Safeer da ba d'an sa ba amma be isa dake daya haifa  ba ko?" Shukrah ta fashe da kuka wane dashi aka aikota,a hankali tace "Ammi Dan Allah kiyi hak'uri,insha Allah I'll change amma karki gayawa Daddyna zaiyi fushi dani" wata muguwar harara Ammin ta watsa mata kafin ta d'ora da "To ki Sani wallahi idan mijinki yabi mata alhakin harda ke za a raba,zakiso ace mijin ki na neman mata Shukrah? Da sauri Shukrah ta girgiza kanta alamar bata so tana wiping tears daketa rolling kan Cheek's d'inta, Ammi ta saki kunnenta ta cigaba "To wallahi Shukrah kiyiwa kanki gata tun baki kaishi bango ba ya sake ki ko ya k'aro miki aure a banzaba tunda shi ba waliyyi bane,AUREN BAZATA hauka ne Shukrah" Shukrah ta girgiza kai tace "A'a Ammii Dan Allah ki yafe min wallahi bazan sake ba Dan Allah karki gayawa daddy, nayi miki Alk'awarin "ZAN GYARA KUSKURE NA". Ammi tayi kwafa tace" Karma ki gyara kinji Shukrah" Shukrah ta sauko daga kan bed d'in tayi knelling a gaban Ammin had'eda rik'o hannunta tace" Ammii Dan Allah kar kiyi fushi dani wallahi na dena hali na, insha Allah bazan k'ara halina ba".
Daga nan Ammii bata k'ara cewa komai ba, Shukrah ko kukanta ta cigaba dayi tana me data sanin KUSKUREN DATA TAFKA A RAYUWAR TA,don duk da bata k'aunar Safeer ta gane girman lefinta kuma tana so ta gyara.

kwanan su Shukrah uku akayi discharging d'inta kuma Alhamdulillahi ta samu sauk'i hakan nema yasa Ammii tace a wuce da ita gidanta.
Ammii da kanta tace Safeer ya dinga kula da shan maganin Shukrah saboda shukrah batason magani, kuma yayi mata Alk'awarin hakan"

To kullum Safeer shike bawa Shukrah maganin saboda tunda ta dawo d'in nan bata rufe k'ofa kuma har gaida shi take yi.

   jiya Shukrah ta gama shan maganin ta hakan nema yasa Safeer beje d'akinta ba kamar yadda ya saba duk dare. Shukrah ganin har yanzu Safeer bezo ba yasa taji bazata iya hakuri ba sai taje ta duba shi saboda yanzu ba lefi ta dan fara sabawa dashi kasancewar har hira yana dan yimata inyaje bata magani. d'akinsa ta nufa kai tsaye gabanta na faduwa dan bata san ya zai dauki zuwan nata ba kuma it's her first time na zuwa room d'in nasa......








Shukrah Cute🥰

AUREN BAZATAWhere stories live. Discover now