Auren Bazata page 11

552 14 0
                                    

✨AUREN BAZATA✨
(2017)




WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
     SHUKRAH

Edited page

1⃣1⃣

Jiki a sanyaye Shukrah ta tura k'ofar room d'in Safeer ta shiga da sallama a bakin ta,yana zaune  a bakin gado da laptop d'insa a gabanshi da alama aiki yake,ya d'ago da fara'arsa jin sallamarta ya answer mata sallamar yayin da take k'arasawa cikin room d'in walking majestically. A hankali ta zauna  a k'asa daga gefen gadon dai-dai k'afarshi,ai kuwa da sauri yace "A'a Dan Allah karki zauna a k'asa in gadon ne bazaki hauba saboda ni bari na sauka na bar miki" ya k'arasa while gathering his stuffs,murmushi Shukrah tayi tana wasa da fingers d'inta tace "A'a wallahi kayi zamanka nan ma yayi" da ladabi tayi maganar wanda yasa Safeer ya kalleta da matuk'ar mamaki don he know how rude she was during their stay kafin tayi rashin lafiy,be ce komai ba sai zaman da yayi a gefenta yana me cigaba da abinda yakeyi.  shiru ne ya biyo baya yayin da Shukrah ta shiga k'arewa d'akin kallo cike da sha'awa,d'akin yayi mata kyau komai na room d'in coffe& milk ne,iya tsaruwa ya tsaru kamar d'akin wata amaryar sai dai d'akin a hargitse yake sosai kamar ba a ta6a gyarawa ba(Abinka da d'akin namiji). Safeer ne ya katse ta ta hanyar cewa "Yi hak'uri ban kawo miki komai ba ko" tayi murmushi tace "Lah bakomai wallahi" ta d'an d'aga shoulder's d'insa yace "Naga ai kina ta k'arewa d'akin kallo kin ganshi a hargitse ko, abinka da d'akin gwauro sai hak'uri".
Wata kunya ce da takaichi suka had'u suka rufe Shukrah, da ace ta kasance mata ta gari kuma 'ya me biyayyah da ita ya dace ace tana gyara d'akin tun asali Amma batayi ba har wani cewa yake wai dakin gwauro sai hak'uri, k'arfin hali tayi sannan tace "bawani d'akin gwauro insha Allah gobe zan gyara room d'in da kaina in ka tafi offiice".
Bece komai  ba sai tunanin daya fara gaskiya Shukrah ta gyaru, Allah ya k'ara shirya ta ya fada a ransa,
Shukrah tana kallon gefe tace  "Dama naga baka zo bane shine nace bari nazo naji ko lafiya" ta k'arasa tana d'agowa tana kallon sa. Ya mayar da hankalinsa kanga sosai yace "Lafiya kalau wallahi aiki ne ya rike ni kula naga ma kin gama shan maganinki" Ta sunkuyo kan laptop d'in tace "Aikin me?" yace "Wallahi wani contract na construction d'in fly over  muka samu shine naketa fama" tace "To Allah ya taimaka, Amma fa ta zanu" yayi dariya yace "uhmm wannan dai zolaya ne ni ina na iya wani zane,muna dai karambani ne" cikin jin dad'in hirar tasu tace "Bawani zolaya ka iya ne shiyasa na fad'a" Yayi nodding yace "Ai shikenan".
Haka dai suka cigaba da hirar su sama-sama har 10:00pm Shukrah ta mishi sallama, tayi tunanin zece ta kwana a nan amma ga mamakin ta sai bece ba.

washe gari 70:30am Safeer ya gama shirinsa na zuwa office ya fito palour rik'e da briefcase d'insa. sam be kula da Shukrah dake zaune ba sai da ya kai bakin k'ofa yaji tana masa magana.
    "Ya Safeer breakfast fa"
   Hannunka ya daga yana kallon wrist watch d'insa kafin yace "Shukrah yanzu in nace zan tsaya gaskiya makara zanyi ki ajiye min inna dawo zanci"
Kamar zatayi kuka tace "Dan Allah ka tsaya kaci ko kad'an ne karka tafi da yunwa" cike da mamakinta yace "karki damu innaje chan zanci" ta rik'e hannunsa tana langa6ar kanta gefe tace "Dan Allah ya Safeer ka tsaya kaci bazaka dade ba"
Safeer yana son chi amma bayason ya sake da ita don ba wani yarda da tuban ta yayi ba har yanzu sai ya k'ara kallon wrist watch d'insa yace "I'm already late Shukrah,but I promise to come back for lunch" tace "O'o ni yanzu zaka ci",6ata rai yayi sannan ya d'auki hanyar dinning,Da sauri ta karaso wane zata fad'i ta ja masa kujera ya zauna sannan tayi serving nashi.  Abincin yayi masa dad'i sosai yanaso ya yaba amma ya danne zuciyar sa har wani yamutsa fuska yake,ya manta when last yaci abinci me dad'in wannan don na restaurant d'in kawai managing yake amma baya waking masa taste bud d'insa up kamar abincin Shukrah.
Ture plate d'in yayi bayan ya gama sannan ya mik'e,Shukrah ma mik'ewa tayi ta d'auki briefcase d'insa ta rakasa har bakin motar sa, sai da taga fitar motar sannan ta dawo ta cigaba da gyare-gyarenta.
Har room d'in Safeer sai da ta gyara as promised.
Coconut rice da egg sauce tayi ta saka a flask sannan tayi fruit salad tasa a Fridge kafin ta tafi room d'inta hurriedly ta fad'a toilet ta  tayi wanka sannan ta fito ta zauna ta tsara kwalliya.6:20pm Shukrah ta k'ara gyara makeup d'inta sannan ta fito palour ta zauna jiran Safeer.

sai 07:12 Safeer ya shigo cikin gidan Shukrah ko najin horn d'insa ta nemi nutsuwar ta ta rasa fargaba kawai take karya wulakanta ta tunda tasan ita ta siya wa kanta,gani take kamar cusa kan yayi yawa amma batada wani option daya wuce hakan don batason 6ata ran Daddynta da yayi mata komai a rayuwa.
baki sake yake kallonta da mamaki tayi kyau sosai kamar ya d'auke ta amma ya dake ya cigaba da,kallonta har ta k'araso inda yake tace  "Sannu da zuwa ya Safeer ta fad'a yayin da take k'ok'arin ta kar6i briefcase d'insa,ya mik'a mata yana cewa "Yawwa Shukrah ya gidan?" tace "Alhamdulillahi"
  daga nan ya shige d'akinsa itama tabi bayansa,kan gado ta ajiye masa jakarsa kamar ta tsaya ta had'a masa ruwan wanka amma tana tunanin kar yace ta fiye shishshigi,amma kuma sai wata zuciyar tace mata 'To inma kin masa shishshigin meye? Ba mijin kibane?ai lada zaki samu' sai ta Juya tayi hanyar toilet d'in ashe wai har ya shige bata saniba tana tunani. Ganin haka sai ta k'arasa jikin,wardrobe d'insa ta ciro masa kaya ta ajiye a kan bed tana addu'ar Allah yasa ya saka kayan data d'auko masa.
Kitchen ta koma ta d'ebo flask din abinci ta zo ta jere su a dinning, sannan ta dawo palour ta zauna tana jiran fitowar sa. Daddad'an kamshin turaren da taji ne yasata d'agowa tana kallon shi da mamakin sai taga kayan data fito mai yasa. zama yayi had'e da d'aukan remote yana canja Chanel. Tayi k'arfin halin cewa   "Ya safeer taso muci abinci" ta saci kallonta kafin yace "Alhamdulillahi Shukrah naci abinci a gidan Mamah kafin in shigo" takaici ya kamata,data tuno lokacin da tayi wasting wajen masa girki amma ya watsa mata k'asa a ido sai ta fashe da Kukan da batasan dalilin saba, take kuma ta k'ara data sanin halayyar ta a baya.
Safeer  a rude yake tambayar ta "menene?ko na fad'i wani abu dabe miki dad'i bane? yi hak'uri ki dena kukan to, ko saboda naje gidan Mamah ne kike kuka?" Da sauri ta girgiza kanta alamar "A'a" with confusion yace  "To menene?" sai ta,sauko k'asa tayi knelling a gabansa tace  "Ya Safeer Dan Allah kayi hak'uri ka yafemin abinda nayi maka a baya kaci abincin nan"
shiru yayi kamar me tunani kafin yace "To naji zanci abincin shikenan" "Eh" tace da murnar ta ta tashi a debo flasks din takawo palour ta shiga serving d'insa. Can ta tsinkayo muryar Safeer yana cewa "kingani kin 6ata makeup d'inki garin kuka ko, d'azu kinfi kyau wallahi"'ya fad'a ba tare da ya saniba. fuskarta dauke da murmushin jin dadi tace "Ai na dena kukan yanzu".
komai bece ba saboda wani haushin kansa yakeji na yaba kwalliyar ta da yayi,shi baya son sake mata don kar yazo ya fara jin wani abu a kanta yayi requesting tazo tayi turning blind eyes to his request don haka yake baya baya da ita.
A hankali ya dinga cin abincin yana enjoying each lauma har ya gama yasa juice,Shukrah ta kwashe kayan da suka 6ata taje kitchen ta wanke kafin ta dawo parlor........










Shukrah Cute🥰

AUREN BAZATAWhere stories live. Discover now