Auren Bazata page 15

376 12 0
                                    

✨AUREN BAZATA ✨
   (2017)

WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
    SHUKRAH


Edited page.
1⃣5⃣

10:40pm Safeer ya shigo cikin gidan, Shukrah ya gani kwance a palour kamar zai tasheta sai kuma ya fasa ya mata addu'a ya shafa mata a jikinta sannan ya wuce room d'insa yayi wanka kafin ya kwanta.


ASUBAH.
Karar bud'e entrance door d'in da Safeer yayi ne ya tashi Shukrah  daga baccin da take, suna had'a ido ta wani d'auke kanta don wayarsa ta jiya ce ta,shiga dawo mata,da sauri ta shige room d'inta tayi banging door, shi kuma ta6e baki yayi,yayi gaba abinsa kasancewar an tada  sallar.
6:50am Shukrah ta gama shirinta tsaf ta  d'auki car key d'inta ta fito palour janye da trolley d'inta,fitowar Shukrah yayi dai-dai da fitowar Safeer daga room d'insa, ko kallo be isheta ba ta wuce abinta ta fita daga palour'n,yayinda shi kuma ya bita da kallo surprisingly.

***
Shukrah ta shigo cikin gidansu janye da trolley,a kitchen ta gano Ammii tana hada breakfast Kawai sai ta sa mata kuka sosai,
A rikice Ammii take tambayar ta wani abun aka mata ne? Ko wani abu ya samu Safeer, Amma ko kulata batayi ba saima cigaba da kukan ta da tayi,
ganin haka yasa Ammii ma bata ce komai ba ta cigaba da aikin ta, zuwa can kukan Shukrah ya fara cimata rai, batamasan sanda ta daka mata tsawa ba, "Dalla malama kin cikamin kunne da kuka kina jina in kukan kike sha'awa ki fita ki bani guri kije kiyita yi tunda bakida abunyi,tun dazu sai tambayar ki nake me akai miki kinmin shiru",stubbornly Shukrah tayi pouting tace "Ammii Aure fa ze yi" Surprisingly Ammii tace "Waye zeyi Auren wai?" Shukrah tayi wiping tears dake rolling kan Cheek's d'inta kafin tace "Ammii Ya Safeer ne zeyi Aure, jiya a gabana tayi mishi waya wai tana son ganin shi shine ya tafi ya barni" tana kaiwa nan ta sake fashe wa kuka sosai,as if she care's about him.Ammi da takaicin rashin hankalin Shukrah ya isheta ta ta6e baki tace "To sai me? aini wallahi ya burgeni, haushin ma daya bani baze wuce rashin sakin ki da beyi ba, Ai naso ma sakin ki yayi ya huta tunda ke bakida kirki bakya jin magana kin raina mu ko?" Da Sauri Shukrah ta had'e hannayenta biyu pleadingly tace "Ammii wallahi shine......" sai kuma tayi shiru ta cigaba da kukan ta,Ammi ta harareta tace "Shine me?" ta k'arasa a d'an fusace,kasa cewa komai tayi  sai ma k'ara sautin kukan ta da tayi,Ammi tayi mata pointing k'ofa tace" Tashi ki fita ki bani guri kafin na kwad'a miki mari wallahi", Tashi tayi ta fita tana cigaba da kukanta,kusan chin k'aro sukayi da Daddy taja baya da sauri,shikam da mamaki yake kallonta ganinta a gida a wannan lokacin yace "Ke lafiyar kuwa?",muryarta na rawa tace "Daddy Ya Safeer ne zai k'ara Aure",6ata rai Daddy yayi kafin yace "To shine me?" ya tambaya irin ko ajikin san nan,jin tayi shiru yasashi cigaba "shine saboda tsabar rashin hankali kikasa k'afa kika fito? To da kika zo nan me zamuyi miki?ko so kike nayi forcing d'insa ya fasa saboda na isa dashi? ai wallahi kad'an kika gani, badai ke kince ban isaba? Har Safeer yamin biyayya ke ki kasa min ko? Ai duk abinda kike ina sane dake zuba miki ido kawai nai naga iya gudun ruwanki gashi tun ba aje ko inaba kin fara kuka da idanunki"
Shigowar Safeer ne ya katsewa Daddy maganar da yake, ya d'urkusa har kasa suka gaisa da Daddy Sannan Ammii da jin sallamarsa ya fito da ita daga kitchen.
Daddy ya mayar da hankalinsa kan Safeer yace "Yawwa Safeer yanzu nake shirin kiranki ai sai gashi kazo" Safeer yana shafa,kansa yace  "Eh Daddy naga Shukrah ta tawo gida ne kuma ni ba wani abu ne ya had'a muba, lafiya kalau muka rabu jiya amma yau naga ta d'auko Trolley ta tawo",murmushin takaici Daddy yayi kafin yace "Eh wai zuwa tayi dan shashanci tana kuka wai zakayi Aure",Safeer ya k'ara yin k'asa da kansa,
"Wace yarinyar ce zaka aura?" Daddy ya tambaya, "A office dinmu take" Safeer yace ba tare da ya d'ago ba,"Masha Allah ni da kaina zan nema maka aurenta kaji dan Albarka, tashi ka tafi office karka makara kaji" Daddy yace
"To" kawai yace sannan ya mik'e yana satar kallon Shukrah ita ko sai zabga masa harara take wane idonta zai fad'o k'asa,ya fita yana murmushi.
Sai a nan Daddy ya kalli Shukrah yace "Kuma ki tashi ki d'auki kayanki ki koma gidan mijin ki kafin in 6ata miki rai wallahi" a d'an fusace yayi maganar amma ko motsi Shukrah  batayi ba sai kukanta take baji ba gani,A tsawace kuma Ammi tace "Zaki tashi ko sai na kwad'a miki mari,useless"
Jiki ba kwari ta mik'e taja trolley ta fice daga palour'n tana cigaba da wiping tears.
Kamar kullum yau ma tayi girkin ta bayan ta gama ne tayi wanka ta tsara kwalliya tanaso taje gidan Ibtee amma kuma bata tambayi Safeer ba gashi batada number shi balle ta kirashi ta tambaye shi,
Tana nan zaune Safeer ya shigo gidan da sallamar shi, Kamar bazata Answer ba sai kuma ta Answer,ta mik'e da kyar ta kar6i briefcase d'insa da polythene bag daya shigo dashi ta kai komai muhallinsa ta dawo ta zauna abinta.

Yau Shukra sai wani share Safeer take shi kuma ya dage yanata bata labarin office, sai nunawa yake kamar bema san tana fushi ba ya cigaba da bata labarin har zuwa lokacin bacci a nan ne kowa ya tashi ya shige room d'insa.

*****

Yau kwana 3 kenan Safeer na fita zance, abin na matuk'ar damun shukrah Amma idan ta tuna cewa itace ta 6ata rawarta da tsalle ta kanyi kuka, in ta zauna ma sai dai tayita istigfari tana rokon Allah ya yafe mata.

Yau ta kama friday Safeer ne ya fito cikin shirinsa na zuwa office Shukrah ya tarar a palour idonta duk ya kumbura dan kukan da tayi,a hankali yaji tace "Ya safeer An tashi lafiya?" sosai yaji tausayinta ya kamashi,yace "Lafiya k'alau Shukrah,Wani abun ya farune naga kina kuka? Ko kin gaji da zama dani ne?"
Girgiza kai tashiga yi tana goge hawayen da ke gangarowa daga idonta tana kuma k'ok'arin hadiye kukan dake son su6uce mata,sai yace
"Ko gida kike so ne?" da sauri tace "Eh ka kaini gida gurin Ammii" tana kaiwa nan tana fashewa da kukan dake cinta,ya shiga girgiza mata kai yace  "To naji zan kaiki amma ki bari sai na dawo daga office",a hankali tace "Toh Amma ina so in shiga mak'ota gurin Ibteesam wadda na gaya maka tazo ranar",yace "is okay ki gaishe ta,sai na dawo" ya nufi entrance,tabi bayansa da kallo kafin tace "A dawo lafiya",sai da ya fita sannan yace  "Allah yasa".

Sai gurin 10:00am Shukrah ta fita zuwa gidan Ibtie.

Sallamar Shukrah ne yasa Ibteesam fitowa daga bedroom ai tana ganin Shukrah ta fara murna tana mata sannu da zuwa,
Bayan Ibteesam ta cika Shukrah da drinks suka fara hira, sosai yarinyar Ibtee ta shiga ran Shukrah kamar ta kwace ta ta tafi da ita, sai addu'a take itama Allah ya kawo mata masu Albarka.
Sai gurin 03:00pm sannan sukayi sallama Shukrah takoma gidanta,Sosai taji dad'in zuwanta gidan Ibtee kasancewar ta gaji da zaman gidan ita kad'ai, shiyasa ta matsu ayiwa su Miemie hutu tazo mata.

Da yamma kuma Safeer ya kai Shukrah gida Amma Ammii bata wani sakar mata fuska ba, sama sama take kulata, sai dare sannan Safeer yazo ya d'auketa suka tafi.
Abin duniya  ya ishi Shukrah ganin cewar bikin Safeer ya matso sosai sai wani sabga yake yana wani rawar kai, wani karin abin takaichi ma shine Safeer daya kar6o kayan da zai sa ran DAURIN AUREN closet d'inta ya kawo ya ajiye.

**
Yau saura sati biyu bikin Safeer saboda haka ya kawo wa shukra invitation cards ko zata gayyaci kawayenta...............

AUREN BAZATAWhere stories live. Discover now