Auren Bazata page 1

1.2K 26 1
                                    

✨AUREN BAZATA ✨

WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
      SHUKRAH

Edited page from my 2017 story,asha karatu lafiya.

0⃣1⃣

Madaidaicin gida ne wanda ya tsaru iya tsaruwa, masu hidimar gidan sai kaiwa da komowa suke.                     
Gabaki dayansu na gani  zaune a dinning table suna breakfast ba wanda ke cewa komai,amma a hakan zaka iya fahimtar they're living happily ganin yadda fuskokinsu ke cikeda annuru,a haka suka kammala
  Ammii ce ta kwashe kwanukan takai kitchen tahau wanke wa.

     30mints later

Daddy ne ya fito cikin shirin sa na zuwa daurin auren dan kaninsa wanda za'ayi a garin Karaye yana gyara links d'insa ya kalli Ammi yace "To Ammii zan wuce" ta dago murmushi kwance akan fuskarta tace "To daddy Allah ya kiyaye hanya "
"Ameen ameen sai na dawo" Daddy yace kafin ya fice daga parlor.

Tafe yake akan hanyar sa ta zuwa Karaye yanata gudu kamar dan shi akayi titin  kasan cewar titin ba cunkoson abin hawa.
       Sai da yazo dai dai inda ze shiga garin gwarzo ya taka kusa aiko tayar sa ta fashe.
"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN" shine abinda daddy yake maimaita wa, waye zai taimakeshi da sanyin safiyar nan  gashi bashida spare Tire  balle ya canja.
      Daddy yana tsaye jikin motarsa yana neman mafita tunani yake kodai ya bar motar ne yatafi gurin daurin auren?  To in ya tafi wa zai bar wa motar sa, yasan komai zai iya faruwa idan ya tafi.

****

Sauri yake tayi kasancewar yau daurin auren amininsa ya zama dole ya halarci  daurin auren.
Tundaga nesa ya hango shi kuma tabbas yaga alamar yana cikin yanayi na neman taimako kasa ya farayi da motarsa yayi parking dan gaba da Daddy sannan ya fito.

  "Sannu Alhaji" yace sanda yazo kusa dashi,Daddy ya answer da
"Yawwa sannu yaro"
"wani abu yasami motar ne?" Cewar matashin yana k'arewa motar kallo,
"Ehhh taya ce ta fashe gashi banida spare" Daddy ya bashi answer da damuwa  
   "subahanallahi Aikuwa inada spare a bayan motata"matashin yace  kafin  ya zagaya ya dauko masa tayar.
  "Bari naje nan gaba kadan akwai masu gyara sai suzo su saka maka" Matashin yace bayan ya dauko tire
   "To madallah" inji Daddy yana mai fadada fara 'arsa. Daga nan SAFEER yayi gaba shikuma daddy ya tsaya.
Befi 20mints sai gashi da Mutum biyu sun dawo nan suka shiga daura taya suka gama.

   "Nagode sosai yaro" cewar Daddy with excitement
"Bakomai wallahi ai yiwa kaine" Safeer ya answer yana k'ara yin k'asa da kansa, "ina kanufa" Daddy ya tambaya.
   "Karaye zani daurin auren abokina" cewar Safeer a ladabce, "Ai nima can na nufa"  Daddy yace yana kallon Safeer da nutsuwarsa da girmamawarsa da kuma kyautatawarsa sukasa ya shiga ransa lokaci d'aya.
Daga haka kowannen su ya shiga motarsa suka kama hanya wanda cikin lokaci kadan suka isa kuma aka daura auren dasu.

  Sai bayan da aka daura auren ne Alh. Al 'ameen sarakee Ya samu kebewa da safeer inda ya bashi complementary card dinsa
  "Ga wannan card d'ina ne don Allah gobe ka sameni a office"
Da" To nagode kuma insha Allah xaka ganni" Safeer ya answer kafin suka rabu.

  Da sallama Daddy ya shigo gidan,Ammi ta fito daga kitchen tana answer wa ta k'ara da "Sannu da zuwa Alhaji" Daddy ya zauna a d'aya daga cikin kujerun parlor'n yace "yawwa Ammii ya gidan?" tace "lafiya kalau"  daga nan ta koma kitchen ta kawo masa ruwa kafin tabi bayansa zuwa bedroom d'insa.

3 hours later....
"Shukrah kizo inji Daddy'nki yana son magana dake" cewar Ammi dake k'arewa room d'in kallo"   "To Ammii" shukra tace tana mik'ewa daga kwancen da take,tabi bayan Ammi tana wondering abinda zaisa Daddy ya kira room d'insa don on a normal days da kansa yake shigowa room d'inta in yana son magana da ita.
  Da sallama ta shigo cikin dakin cike da biyayya ta gaida mahaifinta  ya answer da fara 'arsa.
  Zuwa chan Daddy yayi gyaran murya ya fara magana kamar haka
  "Shukrah inaso ki bud'e kunnenki ki saurare ni da kyau kuma ki dauka cewa maganar da xan fada miki umarnine ba shawara ba.
    Gaban Shukrah ne yashiga bugawa da sauri sauri 'To me Daddy zai gaya mata ne wai
" Kina jina?" ya katse mata tunanin da take
"Ehhh" Kawai ta iya cewa tana sauraronshi
"Nayi miki miji kuma nan ba da dad'ewa ba zai zo ku fahimci juna" cewar Daddy in a seriously tone,
" miji kuma" Shukrah tace tana zaro idonta,
   "Alhaji miji fa kace" Cewar Ammi da itama ta rud'e
"Ehhh miji mana menene?" Daddy ya answer ta idanunsa kan TV
"Ai naji ka fadi abinda bazai yiwu bane" Ammi ta fad'a a fusace,murmushin manya Daddy yayi yace "Ai kuwa sai ya yiwu kuma ki zuwa ido ki gani" yana gama fadar haka ya mik'e ya fice daga gidan ma gaba daya.
Ammi ta bishi da idanunta a zazzare kamar zasu fad'o yayinda Shukrah ta fashe da kuka ta fad'a jikin Ammi ta k'ank'ameta.

To FAHH....

KO WANENE MIJIN DA ALH SARAKEE YA ZA'BA WA 'YARSA?
  SHIN ZASU AMINCE DA AUREN KO KUWA A'A?

AUREN BAZATAWhere stories live. Discover now