Part 27/28

399 23 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
WATARANA SAI LABARI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
True Life Story
Short Story

Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

Dedicated to.
Ummin Na'eema ,Allah yabar k'auna inaji dake irin sosai d'innan.

Tnx to Bintu Baby Muktar ina gaisuwa.

Fans nadawo ayi hak'urin rashin typing danayi ayyukane sukamin yawa ,Tnx 4 d texts,msges nd call.Ina alfahari daku.
2⃣7⃣&2⃣8⃣

Kallon Mama nayi nace"....Mama meza'a daura na dare,da Murmushi tace".....ki bari Khadeeja zata dafa.

A'a Mama ki fad'amin ai nida'ita duk d'aya ne,to duk abinda kika dafa yayi.

Tashi nayi ta nunamin kitchen na shiga,komai na buk'ata akwai shi acikin kitchen d'in don haka nayanke shawarar dafa  tuwon shinkafa da miyar ganye.

Cikin awa d'aya nagama komai dayake gas d'in me biyu ne,na had'a juice d'in kwakwa nasaka a Fridge d'in dake kitchen,na wanke kayan dana b'ata na gyara komai kamar banyi girkiba na fito.

Samunsu nayi a parlour suna zauna na tsuguna nace"....Mama na gama tace"....to Y'ar albarka har kin gama sannunki da aiki to ya kika hana Khadeeja ta tayaki?,bakomai naga bata jima da dawowa daga makaranta ba.

Toh babu komai kuje kuyi alwala lokacin sallah yayi,alwala mukayi yaya Hameed yajamu sallah.


Zama mukayi kowa yana lazimi donna lura ala'adar gidance basa tashi sai bayan sallar isha'i,seda aka k'ira sallar isha'i mukayi sallah tukun Mama tace"....Khadeeja kuje Ku d'auko kayan abincin."

Tashi mukayi muka d'akko kayan abinci aka shimfid'a babbar darduma aka zauna,cikin babban tray naga anzuba abincin Mama tace"...bismillah. "

Hawayene yataru a idanuna tuno da Mahaifana danayi,don suma tare muke cin abinci.

Kasa cin abincin nayi seda Hameed yace"...Sis why are u not eating?,da Murmushi nace".....nothing yace"....then eat."

Mama tace"....kada kiji kunyarmu  kici abincinki kinga kowa ma yana ci,kallonsu Haneef tayi taga Khadeeja tana bawa  Haneef Zainab kuma tanaci dakanta."

Abincin tafara ci,su kuma suna santin abincin,Khadeeja tace"....oh Yaya Jafar ko magana bakayi,Yace"....yo so kike ina magana kafin na ankare angama da abincin."

Tace"...base adafa maka indomie ba,yace"....aii ni nadaina cin jagwal d'inki kullum sis ce  zatana  mama girki."

Dariya sukayi su duka Mama tace"....Oh saboda ka samu wata shine zakayiwa Auta butulci ko,yace"....Mama dama aii manage mukeyi tunda kin hana anti Shareefa dafa nata jagwal d'in."

Shareefa tace"....Bro nice mai jagwal?,yo ai da kad'an naki yafi na Khadeejan."

Dariya nayi nace"....to nikam Mama da Bro Hameed zannayiwa girki,sauran kuma na Deeja zamuci ko Auta."

Khadeeja tace"....eh anti kuma ni yanzu ba auta bace Haneef ne Auta se Zainab,Jafar yace"....Sis Ruhaima ki tausayamin zan iya sumewa innaci abincin Deeje."

Kuka tasa Mama kice yadaina cemin Deeje,sai an fad'a d'in tace"....zaka gane sainaje gun Hafsa nace"....kana rainani."

Hafsa budurwar Jafar ce  yace".....rufamin asiri wlh nadaina na tuba,nabi Allah na biki,dariya kowa yasa Hameed kuwa Murmushi kawai yayi yace"....yau kam karkiji wani sorry kije ki had'ashi da'ita. "

Yauwa Yaya aramin wayarka inada numbarta akaina,Jafar yace"....pls Bro karka bata,Hameed ne yamik'a mata wayar."

Tana k'arba tayi dialing d'in numbar,bayan Kamar minti 1 saita juya fuska a tab'e tace"....kasan bakada kati shine kabani wayar ko,Kamar da gaske yace"....Haba lil sis bansan babu ba amma kibari anjuma zan saka."

Jafar ne ya tuntsure da dariya yace"....a buga mugani mana,Hijab Khadeeja ta d'auka zata fita saboda basuda nisa dasu Hafsa."

Dasauri yakama hannunta yace"....am sorry Sweet sis,dakyar yasha kanta tahak'ura ta zauna ana musu dariya."

Mama tace"....zanga ranar dazaku daina halin tom nd Jerry kaida Khadeeja,dariya kowa yayi sannna aka tashi don zuwa kwanciya."

Zainab da Haneef a d'akin Mama suka kwana ,while Ruhaima take a d'akin su Shareefa.

Haka muke rayuwa cikeda jindad'i da annashuwa,anso asani makaranta amma nace banaso saboda banason wani dangina yasan ina  borno.

Duk zamana dasu basu tab'a b'atamin rai ba,saboda tabbas sunada tarbiyya ga girmama nagaba dasu.

Kuma munyi shak'uwa mai tsannai atsak'aninmu,mun koma kamar ciki d'aya muka fito ba banbanci duk abinda za'a musu sai an mana.

To watarana muna zaune   a parlour duknamu muna fira sai mukaji sallama,to dayake ninake kusa da k'ofa saina tashi don bud'ewa.

Dayake glass d'in  k'ofar da kauri na ciki na iya ganin na waje amma na waje ba dole yaga wanda yake cikiba,turus nayi ganin k'anwar mahaifina.

Da gudu na koma ciki tare da zuwa bayan Bro Hameed na b'oye fuskata,a tsorace sukayo kaina suna tambayata  shi kuma Hameed yafi kowa damuwa saboda shi Sam bayason  yaga mace cikin tashin hankali saboda yana matuk'ar son k'annensa.

A tsorace nace"....K'anwar Baba nace tazo,Hameed cikin d'aure fuska ya tashi, Mama tayi saurin rik'e masa hannu don tasanshi  akwai zuciya."

Tace"....Ruhaima kama hannun su Zainab ku shige ciki,da sauri muka shige ita kuma ta nufi k'ofa don bud'ewa."

Muje zuwa.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Royal Blood Typing
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Alk'alamin Autah✍

WATARANA SAI LABARIWhere stories live. Discover now