Part 23/24

397 24 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
WATARANA SAI LABARI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
True Life Story
Short Story

Written By
Khadeeja Hydar
Young Novelist

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

Dedicated to
My Baby Pie(Meenerl)
Missing U lyk kilode.

2⃣3⃣&2⃣4⃣

Sunan yaron Ibrahim amma ana k'iransa Khaleel,d'an Alhaji jubreel ne suma mutanen Borno no amma su Shuwa ne,to a lokacin kafin su tafi waje suna mutunci da gidanmu.

Wannan kenan.

Akwai wata mata mai suna Maryam y'aranta duk Matane  duka sunyi aure d'ayar zaman babu dad'i,se Babbar Budurwar dake gabanta mai suna Hafsa.

To matar irin masu hassadane da kyashi,tanajin Khaleel yace"....ze nemi duk inda Ruhaima take ya aureta yasa taje tasamu Mahaifiyar  Khaleel wacce takasance k'awa a gunta."


Bayan sun gaisa tace".....Hajiya menake ki haka agari meke shirin faruwa a zuri'arki,da mamaki Mahaifiyar Khaleel takalleta tace".....meke faruwa ne Hajiya Maryam ki fahimtar dani dalla-dalla".

Gyara zama tayi tace"....to naji zancen wai Khaleel yanason yanemo Ruhaima Y'ar gidan marigayya ya aura kuma kin zuba masa ido,Murmushi tayi tace"....Allah Sarki Ruhaima Y'ar kirki marainiyar Allah."

Uhmm aida Ruhaima take Y'ar kirki banda yanzu,guduwa fa tayi taje tana karuwanci bayan kuma babu abinda ta rasa.

Idanu ta zare tace".....dagaske kika Hajiya maryam tace"....ah to aii bazan miki wasa ba,amma akwai Y'ar gurina meze hana yanemeta,tace"....kai nagode kuwa Allah yabar zumunci tace"...wlh ba komai aii yiwa kaine,Ibrahim aii nima d'a nane.

Uhmm duniya kam ayide mugani.


Washe gari da safe kuwa aka bamu abinci mukaci muka k'oshi,daganan ta tambayeni meyafaru nazo ban sanar ba?,nafara fad'a mata abinda ke faruwa kenan saiga k'iran kawu.

Bayan sun gaisane yafara zayyano mata k'arya da gaskiya,tana gama wayar tace"....daman karuwanci kikeyi to asirinki ya tonu ba'anan gidan ba kuwa wato shine kika gudo baki fad'amusu ba se a tasha suka tambaya suka San kinzo nan to wlh yanzu base anjuma ba zaki barmin gidana."


Kuka na fashe dashi inabata hak'uri nace".....wlhh Mama bahaka bane a wani daji muk.....bank'arsaba ta wanke ni da Mari tace".....tashi kifitarmin daga gida shegiya irin zina."

Tashi nayi zan fita ta jefomin kayanmu tace"....maza can gasu gada amma badaniba,tak'ira su Zainab tace".... Ku bita taci gaba da saida jik'inta tana ciyar daku,Allah wadare da irinku."


Uhm Duniya Budurwar  wawa.

Fita nayi na share hawaye kar mutane suna kallona,gidan dangin Mama ta na nufa,se addu'ar karsu koreni suke.

Muna zuwa a sanyaye na shiga kuma agajiye saboda banda kud'i da k'afa mukazo ga Nagoya Haneef,ga Zainab ga jakarmu.

Da sallama na shiga gidan,amsamin akayi tare da mana lale zama mukayi aka bamu ruwa mai sanyi,mu kasha.

Haka muke rayuwa agun Y'ar uwar mahaifiyata,Alhamduliilah muna samun kulawa dukda wani gamin ana hantararmu,amma haka muke jurewa muke zama tunda bamuda gun zuwa.

Bayan wata biyu nasamu aiki a unguwarmu,saboda abubuwa sunfara canzawa saboda yadda ake kawomata k'orafi daga inda na baro.

To abinda ake fad'amata yafara tasiri akanta,saboda yanzu ta sauya Abu kad'an zamu mata tafara ruwan bala'i da masifa,nikuwa seda nayita bata hak'uri.

A lokacin danafad'a mata nasamu aiki,k'iri-k'iri ta nuna bataso,nikuwa nak'i barin aikin saboda nasan watarana tabbas zata koremu.

Wani gamin saina zauna ina  tunanin wai ni yaushe sauk'i zezomim a ,yaushe zan zama mai  Y'anci.

Muna haka wata rana muna zaune se akayi sallama akace ana nemana,uhm Ashe daman tana jira ne,bayan na dawo saboda bandad'eba ni kwata-kwata bana kula maza.

Tace".....andawo daga karuwancin?,a firgice nace".....Inna karuwanci kuma aina?,tace".....ubanki kike tambaya wlh kin kusa barinmin gida donni baza'ayi abin kunya agida naba,wayasan adadin cikin dakika zubar ma wlhh nikam baza'a haifarmin shege ba."

D'aki na shige inata kuka seda nayi me isata tukun nayi alwala nayi nafila nafara rok'on sassauci gun Ubangiji,seda nad'an samu relief tukun na kwanta tare da fatan dacewa a duniya da lahira

Uhm nace"....Ruhaima take it easy INNA MA'AL USRI YUSRA(LALLE KOWANE TSANANI YANA TARE DA SAUK'I)
Fad'ar Allah S.W.T.

Muje zuwa::KU KASANCE TARE DA YOUNG NOVELIST.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
ROYAL BLOOD TYPING
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Inajiiii da Comment d'inkuu fans.

Alkalamin Auta

WATARANA SAI LABARIWhere stories live. Discover now