Part 2

945 45 1
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
WATA RANA SAI LABARI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
True Life Story.
A Short Story.

Written By.
Khadeejaht Hydar.
Young Novelist.

✍✍✍✍✍✍✍✍
GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION.
✍✍✍✍✍✍✍✍

We are bearer's of soo golden pen,We writers assiduously perceive no pain, so magical our creative golden pen,Be hold our world's,A product of our pen savour our  words for it will cause u no pain❄

Dedicated to.
D best mother who give birth to mah twin sis hrt u Muah.

2⃣
Haka muke rayuwa take tafiyarmana wani gamin dad'i wani gamin wiya,saboda muna fuskantar rashin k'auna daga k'anin mahaifinmu.

Mamarmu takan kwantar mana da hankali dacewar komai zai zama tarihi.

Kullum zancenta bai wuce mu had'a kanmu ba  mu zamo tsintsiya mad'aurinta d'aya,to anya burinta zai cika kuwa toh muje zuwa.

A ranar wata talata muka tashi da jimamin rashin lafiyar mahaifiyarmu,inda a lokaci d'aya ta canza kamar ba itaba nan muka garzaya asibiti da'ita.

Gwajin farko aka tabbatar mana da tana d'auke da ciwon zuciya,Wannan maganar tayi matuk'ar girgizani ni a zatona sai mutum yana saka damuwa aransa tukun zai kamu da ciwon zuciya,Uhm Ashe bansan mama tana d'auke da damuwa  a cikin ranta ba.

Alokacin inada shekara ashirin kuma duk nafi shak'uwa da Mamata don haka kullum ina cikin kukan jinyarta damata addu'ar samun sauk'i,haka muka shafe watanni a asibitin babu ci gaba.

Kawunmu ya bugana y'an uwan mahaifinmu cewa ga Babanmu Yana ta b'ata kud'insa akan mama kuma ba'asamun cigaba,Haka suka bugo muna asibiti sukace  ma Baba  wai akoma da Mama gida ana mata maganin gargajiya.

Haka muka koma gida mukaci gaba da jinyarta abinde  ba'a magana don yanzu mama komai saide mu mata,Haka nake kullum ina tare da'ita some times nayi kuka harna gaji ganin irin wulak'ancin da kawunmu da wasu daga cikinsu ke mana.

Babanmu kullum cikin kwantar mana da hankali yake musamman ni saboda lokaci d'aya na fita hayyacina,Kullum aikina shine yin sallar dare don Neman agajin Ubangiji.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
A kwana a tashi yau rashin lafiyar Mamanmu yacika shekara d'aya, Kuma a rannanne  ciwonta ya tsananta ba yadda take.

Muna zuwa asibiti aka sanar mana da zuciyar Mama ta kumbura tashinta sede wani ikon Allah,haka muka sha kukanmu har muka hak'ura.

Gida muka koma da'ita don likitocin sunce mukoma gida zasuna zuwa dubata,Muna dawowa b'angarenta d'aya ya daina aiki wani tashin hankali muka shiga.

Washe gari  yakama Juma'a Ranar data kasance ranar bak'in ciki gareni ,Ranar danayi bankwana da farinciki nayi bankwana kwanciyar hankali,Nayi rashin wani babban bango a arayuwata.

Ranar da matsaloli suka fara shigowa rayuwata,ranar da y'an uwa da wasu jama'a suka k'ini suka gujeni.

Aranar mukayi mata wanka muka bata abinci tasha magani,sai muka fita don yin wasu ayyuka,Bayan kamar minti 30 sai na shiga d'akin don dubata saboda haka kawai naji inason ganinta kuma sai naji gabana na fad'uwa abinda baitab'a faruwa daniba.

Da shigata d'akin naganta a zaune abin yabani mamaki don rabonta da zama ma har mun manta a hakanma muke d'agata,da sauri na k'arasa nace"... Mama waya tadaki tace".... Babu kowa dakaina na tashi."

Wani farinciki ne ya lullub'eni ganin a samu lafiya da fara'ata nace"... Mama mezan kawo miki,Ashe wannna Murmushin danayi bankwana nayima Murmushin a rayuwata,harna tashi tace"...Ruhaima zonan.

Juyowa nayi na zauna da Mamaki don bata k'iran sunana,Zama nayi a hankali takama hannayena biyu ta rik'e tace"... A duk inda zaki samu kanki ki zamo mai sanin darajarki ta y'a mace,ki kasance mai hak'uri da juriya a duk inda kika samu kanki,ki zamo jaruma ki rik'e k'annenki hannu biyu kinga yayarki gidan wanj take ki  kula da k'annenki nabaki amanarsu."

Hawaye na share nace"....toh Mama amma meyasa kika fad'an irin wannan insha Allahu zaki rayu damu har muyi aure,Murmushi tayi tace"... Jekiyi aikinki Kinji Allah yamiki albarka.

Tashi nayi inajin dad'in tasamu sauk'i,likitan dake dubata ne yazo Bayan shigarsa da kamar minti 10 sai ya fito yana waya yace"... Alhaji Allah  yayima Matarka rasuwa."

A razane na d'ago na kalleshi  da sauri kuma na shige d'akin,taradda Mama nayi rai na Neman fita,da sauri na k'arasa tare da k'iran sunanta.

Murmushi akan fuskarta bakinta na motsi Nayi saurin kai kunnena,a hankali tace"....Ruhaima Allah yayi miki albarka kin kasance y'a mai biyayya Kuma Insha Allah bazaki tozartaba,ki rik'e k'annenki Amana Kada ki bari suyi maraici."

D'ip naji shiru a razane Na d'ago zuciyata na harbawa da sauri da sauri,Jijjigata nake ina kuka nace"... No Ummiee karkimin haka pls don't go karkitafi kibarmu lokacin damuke buk'atarki,please Ummi karki tafi i can't do without you I can't leave without you plss don't goo.

Da gudu  na fita a k'ofa mukayi karo  da Baba jikinshi na  fad'a ina kuka  nace"... Dan Allah Baba kacema Mama Karta tafi Dan Allah,Da gudu naje tsakar gida  na d'auki k'aramin k'anina Wanda baze wuce shekaru uku ba  nashiga d'akin dashi.

Sauk'esa Nayi nace"... Dan Allah Mama ki tashi            kinga Haneef yana  son ganinki pls ki tashi,Yaya ta da k'annena duka sai kuka suke jama'ar dasuka shigo duka hawaye suke don tausayamana.

Toh Muje zuwa.

Royal blood typing

WATARANA SAI LABARIWhere stories live. Discover now