Part 4

540 39 1
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
WATARANA SAI LABARI.
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
True Life Story.
A Short Story.

Written By.
Khadeejaht Hydar.
Young Novelist.

✍✍✍✍✍✍✍✍
GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION.
✍✍✍✍✍✍✍✍

❄We are bearers of soo golden a pen,We write assiduously perceive no pain, so magical our creative golden pen, Be hold our words, A product of our pen savour our words for it will cause u no pain.❄

Dedicated to
ABDOOL.
Wish u Allah Khair nd Rahma.

4⃣
Haka nake rayuwa dagani sai Baba na sai Haneef da Zainab,to Alhamduliilah Muna samun kulawa agunsa.

Bayan wata biyu da rasuwar Mama tafiya takama Baba zuwa Borno aka barmu a hannun kawunmu,Babu abinda yake mana sai muzgunawa shida matarsa ga horon yunwa dukda Babanmu yabar masa komai dazamu buk'ata kafin ya tafi.

Akwai wata rana da safe bayan muntashi ga babu abinci saina yanke shawarar zuwa gun kawunmu don sake fad'a masa cewar bamu da abinci,ina zuwa na tadda shi da matarsa da y'ay'ansa suna breakfast da abinci mai rai da lafiya.

A sanyaye na shiga na tsuguna chan gefe dasu nagaidasu,a wulak'ance matarsa tace"....Malama miya kawoki gidan mutane da safennan?,A hankali nace"... Daman bamu da abinci ne kuma na fad'awa Kawu tunjiya naji shiru jiya da daddare ma garri mukasha muka kwanta.

Wata tsawa ya dak'amin yace"... Toh don ubanki nizanna ciyardaku ne?, kud'in da ubanki ya bari ya k'are don haka sai kisan yadda zakiyi."

Murya na rawa nace"... Dan Allah Baba kayi hak'uri ka bamu abinci kaga Haneef yunwa yakeji sai kuka yake,a zafafe yace"... Yimin shiru  munafuka Mara tarbiyya anki abaku abincin."

Tashi nayi zanwuce Matarsa tace".....ga wannan tajefomin wani guntun breadi d'auka nayi badon kainaba sai saboda k'annena don ni Allah yamin zuciya gashi banason wulak'anci,Fita nayi ina share hawayena na nufi gida.

Ina zuwa na had'a ruwa mai sanyi da sugar nabasu tare da  basu breadin nikuma na hak'ura,haka suka sha na musu wanka saboda yanzu sun daina zuwa school saboda Baba  bayanan kuma akan idanuna yabasa kud'i.

Rungumesu nayi ina tunanin mezamuci da rana balantana ni wacce yunwa duk ta galabaitani,haka muka wuni babu abinci sai ruwa damuke tasha,se da yamma Matar kawunmu ta aiko mana da tuwo d'an k'adan Wanda baze ishemu ba,haka nad'anci kad'an na barmusu.

Haka na kwanta ina kukan zuciya Wanda yafi na zahiri ciwo,ina tunanin  yadda mahaifiyarmu tabarmu lokacin damuke buk'atarta.

Haka muka kwashe  watanni uku muna cikin wannan hali babu taimakon kowa,mutanen dasuke nuna suna son Mamarmu a lokacin tana raye sun juya mana baya,rayuwa tamana k'unci babu kowa garemu sai Allah da Baba,duk munbi   Mun rame kamar ba muba..

Juyamin bayan da mutane suka mana bai dameniba irin yadda yayata da k'anwata suka gujeni suke nunamim tsana k'arara.

Muna zaune  a tsakar gida sai mukaji sallamar  Baba, Da gudu muka tashi mukaje gunsa,kallonmu yake musamman ni.

Bayan mun zauna ko ruwan dana kawo masa baisha ba yace"....Ruhaima meyafaru naga gidan haka kuma meyasameku duk kuka rame?,a hankali nafad'a masa halin damuke ciki ranshi inyayi dubu ya b'aci.

Beyi magana ba illa fita da yayi,baifi minti talatinba  ya dawo da abinci ya zauna mukaci muka koshi,rabona danaci abinci na k'oshi tun wata uku dasuka wuce."

Seda muka gama ya tattara mu yace"... Mu shige d'aki shima haka yawuce d'akinsa,bayan kamar minti ashirin saiga kawu yazo."

Tundaga tsakar gida ya fara kwala mata k'ira,da sauri ta fito duk a tunaninta Baba bayanan, shek'ek'e yake kallonta yace"....Ke mara kunya gashi wa jefa mata ledar dak'e d'auke da bread k'arami yace"... Wannan shine abincinku na rana da dare."

Kafin nayi magana Baba ya fito yace".... Nagode Ibraheem Nagode sosai daman so nake na tabbatar da zargina,yanzu daman in Allah yamin rasuwa bazaka iya rik'emin y'ay'a naba,haba kabani Mamaki  ai ni azatona yarana yarankane Ashe bahaka bane to Alhamduliilah nagani da idanuna.

Kunya takama Kawu kamar zai shige k'asa,Amma se ya fukse yafara zazzaga bala'i,Hannuna Baba ya kama muka shige tare da barmasa ledar Breadinsa agun.

Muje zuwa.

Share.
Like.
Vote.

WATARANA SAI LABARIWhere stories live. Discover now