ASHIRIN DA HUDU.

4.9K 903 184
                                    

~~~~

Wannan shine babi mafi tsawo a duka labarin nan, ina fatan hakan zai wanke zuciyarku.☺️

***

Hoto ƙarya ne!

Abinda Salwa ta ambata kenan a lokacin da tayi arba da fuskar Madaki kuma numfashi ya tsaya a maƙogwaronta, don yana da wani irin kwarjini da kamala wanda ya fito karara fiye da yadda take ganinsa a idanunta. A lokacin da yayi murmushi wa Aliyu dake nufar wajensa kuwa, sai da zuciyarta ta buga cikin ƙirjinta sannan a take wani gefe na ƙwaƙwalwarta ya tuna mata da nata kammanin, kamannin fuskarta... Musamman wasu ƙananun ƙuraje da suka fito akan kuncinta duka biyu.

Sai kawai ta juyar da kanta gefe sanda muryar Khadija kewa Aliyu daya ruga magana cewa kar taje ta hau kansa, a lokacin ne kuma idonta ya sauka a gefem, gefen gadon... Inda duk da ɗimbin abinda take ji take zuciyar ta gaya mata cewa yarinyar da take kallo itace wannan halittar dake cikin jerin abubuwan da take son kawar wa a duniya, amma yarinya kamar wannan? Ta yaya hakan zai yiwu? Ta yaya za'ace da wannan abar take gasa wajen mallakar sunan Matar Madaki? Ta yi zaton zata ga irin wayayyun matan nan ne da suka goge da duniya ta hanyar kudi da kuma dukkan wata wayewa ta zamani, amma wannan? A lokaci guda sai taji wani dunƙulen abu ya zarce cikin busashshen maƙogwaronta.

Akan wannan yarinyar da bata da ko kyau balle daukar hankali ta rikita nutsuwarta? Akanta ta ɓata dubunnan kuɗaɗenta da har aka tafka wannan akasin? Akan wannan yarinyar da baifi cikin kwana ɗaya Namama ya tarwatsa ta da dukkan ahalinta ba? Allah ya sani ba irin nadama da takaicin da bata yi ba a lokacin da ta samu labari abinda ya faru, wanda ta danganta komai da rashin ƙwarewar mutanen kawai ba don wata ƙaddara ba.

Saboda tun a Abuja sau nawa tana ganin ana gudanar da ayyuka irin wannan kuma ba'a taba samun wani akasi ba sai akan nata? Zuciyarta taso ta kumburan tun a jiyan da Khadija ke gaya mata abinda ya faru bayan fitar Mubarak, amma da ya dawo ya shaida musu halin da ya baro shi a ciki cewar al'amarin da sauƙi sai itama ta sami nata sauƙin a zuciyarta.

Tana ganin watakila hakan ma ya zame mata wata hanyar da zata fara aiwatar da kudirinta akansa, watakila tunda bai raunana da yawa ba, hakan somin hanyar nasararta ne, musamman a yanzu da tayi ido biyu da yarinyar sai ta sake raina komai, take ganin cewa ba sai ta tashi hankalinta ta sake wahalar da kanta a karo na biyu ba... Babu abinda yarinyar ta sani kuma babu abinda zata iya tare mata, don in ba aikin ƙaddara ba kamar yadda Mubarak ya siffanta ta yaya ma za'a haɗata da Madakin? Ai ko makaho idan ya shafa zai san cewa banbancin a baiyane yake! Mata irinta masu wayewa da sanin rayuwa su suka dace da maza irinsa ba wannan ƴar abar da wani sai ya duba sau biyu tukunna zai ganta ba.

Baki da wata matsala! Gefen zuciyar tata ya ayyana hakan a ranta, yana gaya mata cewa an sami wannan akasin ne don ta daina wahalar da kanta, tabi komai a sannu... Ibrahim ba zai taɓa son wannan yarinyar ba kamar yadda itama ba zata san darajar abinda ke hannunta har ta iya karkato da hankalinsa kanta ba...

Khadija na ta ƙoƙarin gaisawa da yarinyar data miƙe rike da plate ɗin abinci a hannunta yayin da har a lokacin Madaki ke murmushi wa yaran, ya miƙowa Aliyun hannu suka yi musabaha kamar wanda ke gaisawa da sa'ansa... Wani ƙullutun abu ya taru ya sake cika maƙogwaronta fam, tayi ƙoƙarin haɗiye yawu amma wannan karon ya kasa tafiya, tana jin kamar zuciyarta ce ke ƙoƙarin tahowa ta fito... Ina Naja'atu take ne? Tazo ta gaya mata tunda suke yawace-yawacensu akwai namiji irinsa da suka taɓa gani, sai dai maza wanda za'ace sun fi shi a kyawun fuska amma ba kamala da kwarjini ba, to ta yaya kuwa ba zata yi dukkan ƙoƙarin ta akan ta mallake shi ba?

Tana tsaye a kofar har a lokacin babu wanda ya lura da ita, kamar ta daurewa komai ta karasa ciki sai kuma taji cewa bata shirya ba, sun taho ne da dan guntun firgicinsu na halin da zasu zo su tarar dashi a ciki, amma tun da har ya warke haka yana iya gane mutane da wannan murmushin... To sai ta shirya tukunna, sai ta shirya a yanayin da kowannensu zai ga darajarta, kowannesu zai ga ƙimarta, Salwa ce ita! Wadda ke shirin hawa matsayin matar Madaki, don haka Madakin ba zai ganta a haka ba sai a yanayin da ko daga mafarki ya tashi zai ga banbancinta da wannan baƙar yarinyar da bata ko hango ta a cikin idanunta!

Zanen Dutse Complete✓Where stories live. Discover now