SHA DAYA.

4.3K 639 95
                                    

~~~~

Tafiyar motar a wane irin yanayi ne da Jidda ba zata iya fassara shi ba, ta kasa gane gudu suke ko kuma akasin sa, tunda ga abubuwa nan suna wucewa cikin matsanancin gudu amma kuma a cikin motar kamar a hankali suke tafiya saboda yadda komai yake dum-dum.

Kuma har a lokacin tana takure a kan kujerar ta kasa ko motsi sannan in banda sanyin A.c da k'amshin turaren nan nasa ba abinda ke shiga kwakwalwarta.

Ga duhun magriba ya fara lullub'e gari a lokacin, ga k'afarta da ba takalmi duk ta tako shinkafar da aka zubar a k'asa sanda ya jawo hannunta zuwa waje, don haka tana son ta mik'a hannu ta karkad'e su amma tsabar tsoron yadda ingarman jikinsa ke zaune a gefenta yasa ko kwakwaran motsi ta kasa. Fuskarta na juye kawai tana kallon window, kuma da alama shima bai ko kalli inda take ba tuk'insa kawai yake.

Bata san inda suke bi ba amma hankalinta ya nuna mata cewa hanyar barin gari ne tunda ta fara ganin k'arancin gine-gine da kuma al'umma, sai kwallar data share sau ba adadi tun daga fitowarsu daga cikin masarauta ta sake taruwa a idonta...

Ina zasu je?
Ina zai kaita?
Shikenan tayi sallama dasu Baddo?
Wannan wace irin k'addara ce, dame zata ji ne wai?

Hawayen ya gangaro kan kumatunta a lokacin da sallar da maza keyi a gefen titi ta nuna mata cewa magriba tayi tunda gari ma yayi duhu, sai tunaninta ya lissafa mata cewa shima zai iya tsayawa yin sallar, kuma zata iya samun hanyar guduwa in har ya tsaya d'in don ko ya k'ulle k'ofar motar zata iya ta dukan gilashin har wani a waje ya ganta ya kawo mata d'auki.... Amma sai duk wannan tunanin ya rushe a lokacin da motar ta hau kan gadar flyover ta barin gari...

Ta san hanyar sarai, don hoton wajen na manne a tunaninta tun a ranar da suka shigo garin ita da su Baddo bayan rasuwar mahaifiyarta, flyover ce mai kyau data sha adon tarin fitilu, hakan yasa ta kasa mantawa da ita tun wancan lokacin, bakinta ya had'iye wani busashshen yawu sannan wata kwallar ta sake taruwa sanda hasken fitila ya dallare fuskarta...

Shikenan rayuwarta kuma ta shiga wani babin, sai yadda ubangiji ya k'addara da ita!

Zuciyarta ta matse sannan wani d'aci ya cika k'irjinta, sai ta rantse a cikin ranta cewar duk abinda zai faru daga yanzu itama zata kare kanta, ai ba laifinta ne kad'ai ba har da nasa shima, tunda ya kasa hana mahaifinsa abinda su duka biyun ke nadama tun a yanzu. Ta san tana d'an shakkarsa amma duk da haka bai isa ya cuce ta cikin sauki ba, ko namanta zai ci to lallai ba zai ci shi ta dad'i ba.

Suna sauka daga flyover idonta ya nuna mata duhun dajin bishiyu fal a kowanne b'angarensu, ta k'ara tabbatarwa cewa sun bar gari kwata-kwata.

Allah ya isa!

Bakinta ya furta a hankali sannan tayi kwafa, kwafar dake nuna cewa ta shiryawa koma me yake jiranta a gaba, tunda ya ruguza hasashenta na cewar sakinta zai yi, to zata bi shi a sannu har ta fahimci manufarsa akanta kafin ta san irin matakin da zata d'auka itama. Ta yarda cewa zuciyarta na da wannan k'arfin gwiwar, rauninta kawai shine zata je inda babu Baddo balle Jamila da Sadiya...

Tana wannan tunanin ne sai ga k'arar wayarsa wanda ya cika shirun motar, hakan yasa lissafinta ya tsaya cak sanda muryarsa mai zurfi ta amsa kiran.

Ina jinka...

Sautin muryarsa na farko ya kara tuna mata kusancin zamansa da nata, don da yake fuskarta a juye take sai take jin da kamar sun d'anyi nesa da juna ne, saboda haka tayi saurin matsawa ta k'ara mannewa da jikin k'ofar motar kafin sauran maganarsa ta biyo baya.

Eh, I'm on my way...

Na gaya maka su Habibu sun taho tunda safe...

Yayi shiru kafin ya sake fad'in

Zanen Dutse Complete✓Where stories live. Discover now