BIYU.

5.1K 1K 26
                                    


~~~~

Ranar da Maijdda ta fara sako k'afarta cikin masarautar KIYARI bayan rasuwar mahaifiyarta da sunan zama ba ziyara irin ta baya ba, kakarta Baddo wadda ta kasance babbar Jakadiya ta sake biya mata bayanin tsarin masarautar wanda a baya bata fiye maida hankali akansa sosai ba don bai shafe ta ba.

Tayi mata bayani dalla-dalla na yanayin gidan sarautar da kuma iyalan dake cikinsa... Wanda har a lokacin bata ga amfaninsa a wajenta ba sai a yanzu da take son sanin waye mutumin data hak'o wani b'ari na k'addararsa jiya.

Mai martaba Ahmad Uba Kamsusi shine d'a na farko a wajen mahaifinsa cikin 'ya'ya tara wanda cikinsu uku ne kawai maza, ma'ana k'anne biyu ne kawai dashi maza duka sauran mata ne. Bayan rasuwar mahaifinsu sanadiyar wata 'yar mashashshara, sai ya gaji mulkin a matsayinsa na Babban d'a kamar yadda yake a al'ada da kuma addinance.

K'annensa mata duka sunyi aure kuma bayan su mazan ma duka suna da 'ya'ya wanda suke sa'anin na mai martaban. Iyalan Sarki guda uku ne, amma banda Fulani wadda ta kasance uwargida, za'a iya cewa sauran guda biyun a suna suke kawai matan sarki amma basu da cikakken iko game da abubuwa da yawa.

Fulani Hafsatu, mace ce wadda kallo d'aya zaka yi mata ka sanya ta cikin jerin manyan mata masu iko, izza, dukiya da kuma ji da kansu. Fara ce k'al mai d'auke da 'yan k'ananan billen da akewa lak'abi da 'tsugunna kaci doya' idanunta na d'auke da wani irin kwarjinin dake sadda gwiwar duk wani na k'asanta, fuskarta kawai ta ishi mutum cikakken bayanin kalmar nan ta 'isa'.

'Ya'yanta biyar sune a jere cikin lissafin manya a gidan, Saifudden ne Babba wanda yake rik'e da sarautar 'Turaki' don haka ake kiransa da hakan, sai Nadiya mai bi masa, Umarul-Faruk ya biyo baya kafin Aisha (Amaryar da ake biki) da kuma autarta Safina.

Haj. Maimuna, matar Sarki ta biyu tazo ne sanadiyar giftawar rasuwar mijinta wanda yake aboki ga shi Sarkin kafin lokacin da ya karb'i mulki, kwarai Fulani ta tada hankalinta lokacin auren kuma babu irin fafutukar da bata yi ba don canja k'addara amma k'arfin ikon wanzuwar 'ya'ya uku ya danne duk wata dabararta. Na'ima itace Babba a 'yayan Haj. Maimuna sai k'annenta Amira da Amina. 'Ya'yan Haj. Maimuna uku tare da mijinta na farko, maza biyu mace d'aya wanda suke can wajen dangin mahaifinsu, amma a masarautar Allah bai bata namiji ba.

Nene Hadiza, mace ta uku a turakar mai martaba tazo ne a matsayin kyauta ga Sarki daga wani aminin mahaifinsa Hakimin katsina a lokacin da ya hau Sarauta, don haka ita d'a d'aya gareta wanda bai kai shekara goma ba mai sunan Sarkin da kansa Ahmad.

Dukkanin wad'annan matan suna rayuwa ne a cikin gidan masarautar amma babu ruwan kowacce da kowacce, gwara ma tsakanin Maimuna da Nene Hadiza anyi shiri kad'an a baya wanda ya ruguje daga ranar da Nenen ta haifi d'a namiji. Amma Fulani, bata bi ta kan shirgin kowacce balle kuma 'ya'yansu, ta tattare komai daga ita sai nata kawai, sannan ita ke da iko akan kusan komai da ya shafi cikin gidan sarautar kuma duk yadda kowacce a cikinsu ke ji da kanta haka suke hak'ura subi tsarinta, don in ba Mai martaba da kowa ke shakkarsa ba, Fulani bata saurarawa kowa.

Hakan yasa zamantakewar gidan ta tab'arb'are saboda idan ba lokuta irin wanda mai martaban kan tara su gabad'aya a rumfarsa ba, za'a iya cewa wani zai shekara ma bai ga d'anuwansa ba saboda hadaniyar komai da shige da fice tana b'angaren Fulani ne inda su ba zuwa suke ba.

Tun kafin zuwan Jidda har kuwa bayan fara rayuwarta a gidan, wannan itace irin rayuwar gidan sarautar KIYARI kamar yadda kowa ya sani.

Abinda a yanzu bata sani ba shine waye IBRAHIM AHMAD MADAKI? Meye alak'arsa da Fulani da har take b'ata lokacinta wajen binne asiri akansa? Kuma har a irin wannan lokacin da take cikin hayaniyar aurar da 'ya? Me yasa ma ya samu sunan mai martaba a sunansa amma kuma babu jigon sunan zuri'arsu na 'Kamsusi'?

Zanen Dutse Complete✓Where stories live. Discover now