SHA SHIDA

4.1K 621 59
                                    

~~~~

𝓜𝓪𝓭𝓪𝓴𝓲.

Jidda ta karanta rubutun dake jikin 'yar ƙaramar takardar a karo na biyu sannan ta sake kai idonta kan kayan, ai bata yi zaton yana da sauran burbushin imani irin wannan game da ita ba, tayi zaton tunda ba zai sake ta ba zai azabtar da ita da yunwa ne ko wani abun yadda in bata mutu ba watarana da kanta zata gaji ta gudu.

Ƙamshin abincin dake cikin ledojin nan ya bugi hancinta, babu shiri ta bude leda ta farko dake gabanta, wata irin jollof ɗin shinkafa ce data sha vegies kala-kala da kuma hanta a ciki, yawu ya taru a bakinta saboda ƙamshin da take yi, a ɗayar ledar akwai wani kwanson dake ɗauke da haɗin salad dana snacks da kuma wani cike da pepper chicken mai kyau a ido, sai ta tabe bakinta kadan tana ƙarewa abincin kallo tare da jinjina kai, ko a Guest Inn din nan ba irin wannan abincin ake kawo mata ba, balle a kuma a koma Kiyari tsakaninta da irin wannan ai sai ana hidima a masarautar ko kuma Sadiya ta samo musu ragowar abincin wani b'angare na matan Sarkin,  ammayau gashi a b'agas wai shine abincin ranarta.

Sai ta maida su ta rufe sannan ta cigaba da kallon dogwayen rigunan dake gabanta da kuma kwalayen turaren nan, har yanzu ta kasa yarda wai nata ne gabaɗaya, wai ita zata saka, gani take kamar kasuwa ta raka Jamila suka tsaya a wani shago don suyi kallo kawai. Ta ɗauki wata pitch colour mai adon baki ta ɗaga ta, tayi mata kyau gaskiya, kamar ace ne mutum ne ya riƙa kallon abinda ba nasa ba, sai ta maida ita itama ta ajiye sannan ta cigaba da ƙare musu kallo.

Tun bayan ganinta da file ɗin nan bata san me ya dace ta riƙe a matsayi tunani ba, ta san dai duk wani ƙudirin data ɗauka a baya game da Madakin ya narke a zuciyarta yabi iska, don tabbas ta yarda cewar Allah bai zagayo da rayuwarta gare shi a banza ba, ance ƙaddara tana da siffofi mabanbanta, to ta yarda wannan itace tata kuma babu ta yadda za'ayi ta iya canja ta, wataƙila shi yasa tun farkon al'amarin nan kowa ya kasa tabuka wani abu a cikinsa.

Aure abu ne mai girma, kuma ko a wace irin siffa yazo abu ne nai daraja da karamci, don haka ta yaya zan iya zuwa in dakatar da Mai martaba Hauwa'u? Me na taka? Wace hujja muke da ita da tafi waɗannan?

Maganar da Baddo ta gaya mata a safiyar Juma'ar nan lokacin da ta tsugunna cikin kuka tana roƙonta da taje ta baiwa Mai martaba haƙuri ta haska a cikin kanta, a lokacin gani take yi kamar ƙarshen rayuwarta ne yazo amma saboda nauyin waɗannan abubuwa guda biyun haka tana ji tana gani aka canja rayuwarta. Wataƙila shima Madakin abinda ya hana shi sakinta kenan kai tsaye, saboda nauyin Mai martaba da kuma nauyin ƙaddarar da ba mai iya canjata.

Sai ita karan kaɗa miya da take ganin zata taka rawar da kowa ya kasa gwadawa hatta Fulanin da take zargi kuwa tunda har yanzu bata ji wani motsi daga gare ta ba, ta cigaba da kallon kayan tana tunanin Allah yasa yadda idonta ke ganinsu haka suke babu wata kutunguilar ko wani kamashon da zai biyo baya.

Ta sake kallon ƴar paper nan daya rubuto sunansa.

𝓜𝓪𝓭𝓪𝓴𝓲...

Yana son sunan da alama, amma ita gani take Ibrahim yafi ɗaɗi, yafi dacewa dashi ma, don inda ace zai kalli mutum da waɗannan oily eyes ɗin nasa sannan fatar lebbensa ta furta sunan shi kaɗai, Ibrahim... Babu abinda zai hana ka rantsewa cewa duk duniya babu wanda ya dace da sunansa sama dashi.

Ita kanta ta sani cewa Madaki irin mazan nan ne da mace zata shafe rabin rayuwarta kafin kafin taga giftawar irinsa a titi, ba wai don kyawunsa ba sai don ƙima da kwarjininsa, irin kwarjinin da ko bai raɓi gidan sarauta ba dole ne ya karɓi respect daga hannun kowanne irin mutum a duniya. Shi yasa bata sa kanta a wahala ba tun farko, ta yankewa zuciyarta cewa zai sake ta ne da zarar an ɗaura masa ita don shi da ita ba sa'annin juna bane, kamar ka shiga wani haɗaɗɗen kanti ne ka siyo ice cream mai daɗi da garɗi cikin flavors kala-kala sannan ka fito waje ka siya wannan ɗan naira biyar ɗin mai biscuit da dattijai ke turawa a keke.

Zanen Dutse Complete✓Where stories live. Discover now