SHA BIYU.

4.6K 690 131
                                    

~~~~

LAGOS.

09:15 AM.

A safiyar ranar talata, Jidda ta bud'e idanunta a hankali cikin hasken ranar daya ratso ta labulayen d'akin, hasken ya sauka akan rabin fuskarta ne shi yasa sanyin A.c dake busawa a d'akin ma bai dame ta sosai ba.

Babu d'ankwali akanta don haka garin juye-juye ribon din ya cire, gashinta da har a yau bai samu gyara ba yana barbaje a kowanne gefe na fuskarta, yawansa yafi tsawonsa shi yasa ya kusan ya binne fukartata baki d'aya, bayan haka jkinta na sanye da wannan leshin ne da Jamila ta bata tun a ranar da faifan rayuwarta ya canja, kuma bayan ita d'in babu wasu kaya a d'akin sai d'ankwalinta da kuma wannan k'aton farin mayafin data yafo, suna ninke akan bedside drawer dake jikin gadon.

Komai na d'akin kalar fari ne da kuma ruwan k'asa, haka nan komai din daya had'a da gado wardrobe da kuma d'an karamin centre carpet had'addun masu kyau ne da a ranar farko tayi ta santin kyawunsu kafin ta fahimci uk'ubar da take shirin fuskanta a cikinsu.

Idanunta a bud'e suke amma har yanzu bata tashi ba, kwalla a hankali kwalla ta shiga zirara daga idonta na sama tana sulalowa kan hancinta kafin ta had'e da ta d'aya idon. Ba wai kwalla ce ta kuka ko rauni ba, kwalla ce na irin d'acin da zuciyarta ke yi ganin cewar rana ta fad'i gari ya sake wayewa bata fitar da rashin mutuncin data tara fal a cikin kanta ba.

Kwana d'aya, biyu, uku har hud'u kenan tana cikin wannan d'akin daya zame mata kurkuku ita kad'ai ranta... Don tun daga wannan daren da jirgi ya sauke su a airpot na garin Lagos bata kara ganin Madaki ba, tare dai suka fito har inda ya karb'i akwatunansa, kuma har suka k'araso wajen ajiyar motoci tana biye dashi k'afafuwanta har a sannan babu takalmi.

Sannan bayan jirin da take ji game da hawanta jirgi na farko, a lokacin cikinta na wani irin ciwo ne da take jin kamar zata yi amai, amma hakan bai sa ta tsaya ba tayi ta binsa don kar ya b'ace mata a cikin d'imbin mutanen dake wucewa ta kowanne direction... Ya dai juyo sau d'aya yaga tana binsa amma bayan haka bai sake ba har suka k'arasa parking space d'in inda yake a jik'e sharkaf alamun anyi ruwa mai yawa a garin... Kuma haka k'afafunta suka dinga bi ta cikin ruwan yayin da take rik'e da k'aton farin mayafinta mai santsi dake shirin zamewa.

Bata san ainihin lokaci a ranar ba, amma zata iya kintata cewa karfe sha biyu na dare tayi duk da babu alamun hakan, don mutane ne a wajen birjik ke ta harkokinsu kamar da rana.

Madaki bai tsaya ba sai a gaban wasu had'addun motoci guda biyu, dukkaninsu bak'ake wuluk sai kyalli suke alamun ruwa ya wanke su ga kuma hasken fitilar dake haskawa a jikinsu.

Har a lokacin waya ce kare a kunnensa yana magana, kuma da sauri wasu maza biyu dake jikin motar farko suka k'araso suka karbi akwati da kuma jakar hannunsa yayin da suke ta faman durkusawa suna gaishe shi cikin tsananin girmamawa, kuma anan dai ta tabbata ba don matsayin sarauta ake masa irin wannan gaisuwar ba sai don ko wani abu daban.

Direban d'aya motar da kuma wata mace inyamura suka iso gabansa suma da tasu gaisuwar, a lokacin ne ya ajiye wayar da yake yi sannan ya shiga amsa musu bakidaya.

Duk wannan abin tana tsaye daga bayansa jikinta na faman b'ari irin na jiri sannan k'afafunta camb'al akan jik'akk'iyar kwaltar wajen. Ta dai ji sanda yake yiwa macen nan magana amma bata fahimci me yace sosai ba saboda murd'awar cikinta da ya k'aru a lokacin.

Kuma daga nan bai ko juyo ya k'ara tabbatarwa cewa tana bayansa ba taga ya nufi d'aya motar data fi girma inda aka sanya masa kayansa, ya bud'e k'ofar baya kawai ya shige sannan matukin dake zaune a wajen direba ya danna wani abu daya zuge gilasan motar bakid'aya zuwa sama.... Sai idanunta suka ware da tsananin mamaki tana kallonsa ta tsakanin d'ige-digen ruwan daya fara sauka alamun yayyafi akan gilashin b'angaren da yake zaune, taga sanda ya sake kara waya a kunnensa sannan ya shiga magana idanunsa na kallon gaban motar kawai, kuma kafin tayi wani tunani ko yunk'uri motar tazo ta wuce ta gefenta yayin da tayoyinta suka fancalo ruwan da ya jik'a k'asan kayanta.

Zanen Dutse Complete✓Where stories live. Discover now